Shagari ya bukaci ’yan Najeriya su yi zabe cikin kwanciyar hankali

Bayan da aka yi ta yada jita-jitar cewa tsohon Shugaban kasa Alhaji Shehu Shagari ya rasu a ranar Lahadin da ta gabata, tsohon Shugaban kasar ya kira taron manema labarai a ranar Litinin inda ya musanta labarin rasuwar tasa tare da shawartar al’ummar kasar nan su zauna lafiya su dauki kansu daya su guji nuna […]

Shagari ya bukaci ’yan Najeriya su yi zabe cikin kwanciyar hankali
Shagari ya bukaci ’yan Najeriya su yi zabe cikin kwanciyar hankali

Bayan da aka yi ta yada jita-jitar cewa tsohon Shugaban kasa Alhaji Shehu Shagari ya rasu a ranar Lahadin da ta gabata, tsohon Shugaban kasar ya kira taron manema labarai a ranar Litinin inda ya musanta labarin rasuwar tasa tare da shawartar al’ummar kasar nan su zauna lafiya su dauki kansu daya su guji nuna bambancin yanki, “Kowa nawa ne da wanda ya zo nan da wanda ma bai zo ba a dai zauna lafiya” inji Shagari.

Turakin Sakkwato ya ci gaba da cewa duk ’yan kasa su samar da zaman lafiyar da zai ba wannan kasar damar gudanar da babban zabe mai zuwa cikin kwanciyar hankali. “Dukkanmu ’yan kasa guda muke, mu sani Allah ba zai taimake mu ba matukar ba mu zauna lafiya da junanmu ba, duk dan kasa nagari yana karbar hukuncin da ya same shi da kyakkyawar manufa koda ya saba wa abin da yake so, don haka kowa ya zauna lafiya kada a yi rikicin zabe a yi hakuri koda wanda ake so bai samu nasara ba,” inji Turakin na Sakkwato.