Shaguna 200 sun kone a kasuwar Kara ta Sakkwato
A ranar laraba da ta gabata ne shaguna 200 da ke cikin kasuwar kara suka kone sakamakon tashin gobara da ta soma da Asubar ranar, inda aka yi asarar miliyoyin naira.A kasuwar ana sayar da Goro da hatsi da dawa da albasa da kayan gyaran injimin wuta da sauransu.Wutar wadda ta kwashe fiye da awa […]
????????????????????????????????????

A ranar laraba da ta gabata ne shaguna 200 da ke cikin kasuwar kara suka kone sakamakon tashin gobara da ta soma da Asubar ranar, inda aka yi asarar miliyoyin naira.
A kasuwar ana sayar da Goro da hatsi da dawa da albasa da kayan gyaran injimin wuta da sauransu.
Wutar wadda ta kwashe fiye da awa shida tana ci, ba a samu salwantar rayuwa ko samun nakasar wani b,a sai dai dimbin dukiyar da aka yi asara. Sanadiyar tashinta wutar lantarki ce da aka maido a wani shago da ke hannun riga da kofar Kade.
Malam Yusuf Labbo daya daga cikin wadanda lamarin ya rutsa da su ya ce sun yi asarar miliyoyin naira a wannan gobarar da ta same su, kuma wasunsu sun yi nasarar tsirar da wani abu cikin kayansu wasun kuwa gaba daya ba abin da suka tsira da shi.
Sakataren kungiyar masu sayar da goro a kasuwar Mista Agboola ya sheda wa Aminiya cewa ‘yan kungiyarsu fiye da 108 suka tabka asara a gobarar, don haka yake kira ga gwamnati da ta taimaka wa wadanda abin ya shafa.
Daraktan hukumar bayar da agajin gaggawa na jihar Sakkwato Alhaji Hassan Maccido ya tabbatar da faruwar haka, ya ce har gwamnati ta kaddamar da wani kwamiti don ganin yadda za a taimaka musu, kuma su dauki wannan abin ya zo daga Allah ne.