Shaguna 500 sun ƙone a gobarar kasuwar katako ta Sakkwato

Sau biyu gobara ta tashi a kasuwar a ranar Laraba, inda ta biyun ta cinye shagunan wucin gadi kimanin 500

Shaguna 500 sun ƙone a gobarar kasuwar katako ta Sakkwato

Kiminanin rumfuna 500 ne aka kiyasta sun kone a gobarar da ta tashi da daddare a Kasuwar Katako  da ke garin Sakkwato.

Shugaban kungiyar ’yan kasuwar, Alhaji Modi Major ne ya sanara da haka yana mai cewa sau biyu gobara ta tashi a kasuwar a ranar Laraba, inda ta biyun ta yi wannan barna.

Ya bayyana cewa ta farko ta tashi ne da misalin karfe 12 na rana, inda aka yi nasarar kashe ta cikin gaggawa “amma daga bisani da misalin karfe 11.30 na dare wuta ta sake tashi, inda ta kona rumfunan wucin gadi kimanin 500 da wasu gine-gine da sauran kadarori na miliyoyin Naira.”

Alhaji Modi Major ya ce ba su kai ga gano musabbabin tashin gobara, yana mai cewa ’yan kungiyar suna bin dokokin kariyar da aka shimfida musu.

Ya bayyana cewa, “Mun umarci mambobinmu cewa kowannensu ya tanadi ruwa cikin duro a runfarsa kuma muna bibiyar su domin tabbatar da bin wannan umarni.

“Mun amince da tarar N5,000 a kan duk wanda ya saba umarnin kuma mun yi kulla kawance da kamfanin rarraba wutar lantarki na KEDCO ta yadda suke yanke layin kasuwar idan aka rufe ta, don haka mun dauki wannan abu a matsayinj kaddara daga Allah.”

Ya kuma yaba da taimakon da gwamnatin jihar ta saba yi wa kasuwar, inda ya ce ta samar musu da fitilun kan hanya masu amfani da hasken rana.