Shaguna 60 sun kone a Kasuwar ’Yankatako da ke Kano
Wata gobara da ta tashi a Kasuwar ’Yankatako da ke unguwar Rijiyar Lemo a birnin Kano ta lakume dukiya mai tarin yawa. Wani ganau mai suna Ibrahim Ado ya ce wutar ta tashi ne da misalin karfe 2:30 na dare. Jami’in hulda da jama’a na kasuwar, Shamsudeen Danwarure, ya ce gobarar ta lakume shaguna da […]
Wata gobara da ta tashi a Kasuwar ’Yankatako da ke unguwar Rijiyar Lemo a birnin Kano ta lakume dukiya mai tarin yawa.
Wani ganau mai suna Ibrahim Ado ya ce wutar ta tashi ne da misalin karfe 2:30 na dare.
Jami’in hulda da jama’a na kasuwar, Shamsudeen Danwarure, ya ce gobarar ta lakume shaguna da dama da tarin katakon da ke jibge a kasuwar.
Jami’in hulda da jama’a na Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano, Saidu Ibrahim, ya tabbatar da tashin gobarar yana cewa shaguna 40 tare da rumfunan je-ka-na-yi-ka (temporary) 20 sun kone kurmus.
Sai dai ya ce ba a kai ga gano musabbabin tashin wutar ba.