Shaguna fiye da 500 sun kone a kasuwar Aleshinloye da ke Ibadan
Gwamnan Jihar Oyo, Sanata Abiola Ajimobi, ya ce zai tallafa wa ‘yan kasuwar Aleshinloye da ke Ibadan da ‘yan kudin da za su dawo da harkokin kasuwancinsu bayan da gobara ta yi sanadin konewar shaguna fiye da 500 a kasuwar a cikin daren Juma’ar makon jiya. Gwamnan wanda sau biyu ya ziyarci kasuwar a ranar […]
Gwamnan Jihar Oyo, Sanata Abiola Ajimobi, ya ce zai tallafa wa ‘yan kasuwar Aleshinloye da ke Ibadan da ‘yan kudin da za su dawo da harkokin kasuwancinsu bayan da gobara ta yi sanadin konewar shaguna fiye da 500 a kasuwar a cikin daren Juma’ar makon jiya. Gwamnan wanda sau biyu ya ziyarci kasuwar a ranar Asabar, domin jajanta wa ‘yan kasuwar, tare da gane wa idanunsa irin barnar da gobarar ta yi, ya bayar da tabbacin cewa a cikin makon da muke ciki ne gwamnati za ta mika tallafinta ga ‘yan kasuwar da suka yi asarar dukiyoyinsu a dalilin wannan gobara.
Da yake tausaya wa ‘yan kasuwar, Gwamna Ajimobi, ya roke su da su yi hakuri da dan abin da gwamnatinsa za ta iya tallafa musu da shi, domin ya rage musu radadi ne.
Ya ce, Allah Madaukakin Sarki ne kadai zai iya biya musu bukatunsu. Ya bayar da umarni ga ‘yan kasuwar da al’amarin ya rutsa da su, da su kafa kwamitin amintattu a tsakaninsu da zai tunkari wakilan gwamnati domin karbar tallafin, inda ya ja hankalin shugabannin kasuwar kan lallai su tabbatar da cewa, tallafin gwamnati ya isa ga hannun ainihin mutanen da musifar gobarar ta rutsa da dukiyoyinsu.