Shah Rukh Khan ya yi bikin kalankuwa a Malesiya duk da raunin da ke kafarsa

Daga Umar Rayyan (da rahoton waje)      Fitaccen  jarumin fina-finan Indiya Shah Rukh Khan ya halarci bikin kalankuwa a kasar Malesiya duk da raunin da ke kafarsa. Da farko an yada jita-jitar cewa jarumin ba zai halarci bikin kalankuwar da za a yi a Malesiya sakamakon raunin da ke kafarsa ba, sai dai jama’a da […]

Shah Rukh Khan ya yi bikin kalankuwa a Malesiya duk da raunin da ke kafarsa

Daga Umar Rayyan (da rahoton waje)     

Fitaccen  jarumin fina-finan Indiya Shah Rukh Khan ya halarci bikin kalankuwa a kasar Malesiya duk da raunin da ke kafarsa.
Da farko an yada jita-jitar cewa jarumin ba zai halarci bikin kalankuwar da za a yi a Malesiya sakamakon raunin da ke kafarsa ba, sai dai jama’a da dama sun yi farin ciki da suka ji jarumin ya tabbatar da zuwansa don halartar bikin.
Jarumin ya isa kasar Malesiya cike da annuri duk da raunin da ke kafarsa, inda dubban masoyansa da manema labarai suka yi dafifi wajen taryensa.
Bikin kalankuwar wanda aka yi wa taken ‘Temptation Reloaded Libe In Malaysia’ ya gudana a filin wasa na Merdeka ya kuma samu halartar wasu fittatun ‘yan wasan Indiya  kamar su Madhuri Didit, Rani Mukherje and kuma Jackueline Fernandez.
Jarumin ya bayyana a shafin sada zumuncinsa na Twitter cewa ya samu raunin ne sakamakon wani kyaure da ya fado masa a kafarsa a lokacin da suke daukar fim din ‘Happy New Year’.
A karshe ya yaba wa ‘yan kasar Malesiya bisa soyayyar da suka nuna masa.