Shah Rukh Khan ya zama tauraron da aka fi kauna a Indiya

Shah Rukh Khan, wanda ake kira da lakanin ‘Sarki a Gidan Khan na Bollywood’ ya sake samun wata sarautar, inda a makon jiya aka tabbatar masa da sarautar mutumin day a fi jan hankalin mutane kuma aka fi kauna a kasar Indiya.A kwanakin baya ne wani kamfani da ya kware wajen nazari da bincike mai […]

Shah Rukh Khan ya zama tauraron da aka fi kauna a Indiya

Shah Rukh Khan, Sarkin farin jinin mutaen Indiya!Shah Rukh Khan, wanda ake kira da lakanin ‘Sarki a Gidan Khan na Bollywood’ ya sake samun wata sarautar, inda a makon jiya aka tabbatar masa da sarautar mutumin day a fi jan hankalin mutane kuma aka fi kauna a kasar Indiya.
A kwanakin baya ne wani kamfani da ya kware wajen nazari da bincike mai suna ‘TRA’ (Trust Research Adbisory) ya gudanar da bincike a manyan birane 16 na kasar Indiya, domin gano mutumin da ya fi daukar hankalin al’umma kuma aka fi kauna a kasar.
Sakamakon binciken ya tabbatar da cewa Shah Rukh Khan ne ya zo na daya, inda ya doke Amitah Bachchan da Aamir Khan da Salman Khan.
Cikin wadanda suka fi zaben jarumin, su ne mata, inda haka ta nuna cewa shi ne shalelen matan Indiya. Wannan ya kara tabbatar da gaskiyar lakanin da ake kiransa da shi, ‘Sarki.’