Shahararren dan fim Kader Khan ya tafi aikin Hajji

Shahararren dan fim na Indiya, Kader Khan na daya daga cikin al’ummar Musulmi sama da miliyan daya da ke aikin Hajjin bana a kasar Saudiya.Bayanai sun nuna cewa ’ya’yan dan wasan mai shekaru 78 da haihuwa, Shahnawaz da Sarfaraz da surukarsa ne suka rako shi zuwa gudanar da aikin Hajjin; a cewar jaridar Arab News.Jami’in […]

Shahararren dan fim Kader Khan ya tafi aikin Hajji
Shahararren dan fim Kader Khan ya tafi aikin Hajji

Shahararren dan fim na Indiya, Kader Khan na daya daga cikin al’ummar Musulmi sama da miliyan daya da ke aikin Hajjin bana a kasar Saudiya.
Bayanai sun nuna cewa ’ya’yan dan wasan mai shekaru 78 da haihuwa, Shahnawaz da Sarfaraz da surukarsa ne suka rako shi zuwa gudanar da aikin Hajjin; a cewar jaridar Arab News.
Jami’in Ofishin Jakadancin Indiya da ke Saudiyya, B. S. Mubarak ya ce Kader na daya daga cikin alhazan da suka ba su karramawa ta musamman saboda shahararsa a duniya.
“Jami’anmu ne suka tarbe shi a Makka a Lahadin makon jiya bayan isowarsa kuma yana cike da farin cikin zuwa kasar Saudiyya domin aikin Hajji,” inji jami`in.
Haka kuma Omer Khan ya kara da cewa hatta yaran nasa suna cike da farin cikin zuwa garin Makka domin sauke faralinsu. Sun kuma kosa da su ga sun gudanar da aikin Hajjinsu yadda ya kamata.
“Mutanen da suke kusa da inda aka sauke shi ne suka fara gane shi, wanda hakan ya sa wasu suka rika sumbatarsa domin taya shi murnar zuwa wannan kasa mai daraja. Kader Khan ya iso wannan kasa ce ta hannun wani kanfanin aikin Hajji mai zaman kansa.” Inji shi.
Bayanai sun nuna cewa a wata hira da aka yi da dan wasan a kwanakin baya, ya ce ya yi nadamar bata shekaru da ya yi yana wasan fina-finai, wanda hakan ya sa a yanzu ya canza tsarin rayuwarsa, ya koma yi wa addinin Musulunci hidima.
Ya yi karatunsa ne a Kwalejin Ismail Yusuf da ke birnin Mumbai kafin ya fara koyarwa a Kwalejin Fasaha ta Saboo Siddik, kana daga baya ya koma harkar fim kuma ya yi fice wajen fitowa a matsayin mugu ko kuma dan wasan barkwanci a fina-finansa.