‘Shahararren’ mai safarar bindigogi ya shiga hannun DSS

Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS), ta bayyana cewa ta kama wani mutum da take zargin shaharren mai safarar bindigogi ne da yake cikin jerin sunayen mutanen da take nema ruwa a jallo. Hukumar tana zargin Jonah Abbey, wanda aka fi sani da Jonah Idi da sayar da bindigogi ga kungiyoyin masu tayar da kayar […]

‘Shahararren’ mai safarar bindigogi ya shiga hannun DSS

Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS), ta bayyana cewa ta kama wani mutum da take zargin shaharren mai safarar bindigogi ne da yake cikin jerin sunayen mutanen da take nema ruwa a jallo.

Hukumar tana zargin Jonah Abbey, wanda aka fi sani da Jonah Idi da sayar da bindigogi ga kungiyoyin masu tayar da kayar baya a jihohi da dama na kasar nan. 

Wata sanarwa da Hukumar DSS ta aike wa manema labarai a ranar Lahadi, ta ce ayarin jami’anta sun yi aiki tukuru a cikin kwana 10 da suka gabata inda suka kama wadanda ake zargi da aikata manyan laifuffuka da dama.

Sanarwar ta kuma ce an yi nasarar kama masu satar mutane don karbar kudin fansa da masu safarar bindigogi da masu satar shanu wadanda suke gudanar da tu’annatinsu a jihohin Filato da Taraba da Benuwai.

Hukumar DSS ta ce jami’anta sun shafe shekara 10 suna neman Abbey ruwa a jallo.

“A ranar 13 ga Maris ne da misalin karfe 12.20 na rana aka yi nasarar kama Mista Abbey a garin Wukari na Jihar Taraba tare da direbansa Agyo Sabiour wanda aka fi kira da dan-Wase. Wasu bayanan sirri na baya-bayan nan sun nuna cewa Mista Abbey ya aiki direbansa Sabiour da makamai da harsasai daga Konduga a Jihar Borno zuwa Jihar Taraba,” inji sanarwar

Hukumar ta ce Mista Abbey yana da abokan kasuwanci a jihohin Filato da Ebonyi da Kuros Riba da Enugu da kuma Bayelsa. “Kuma alamu sun nuna cewa yana samun makaman ne daga Jamhuriyyar Kamaru da wasu sassan Arewa Maso Gabas,” inji DSS.

Hukumar ta ce ta kama wani mai satar mutane don karbar kudin fansa mai Lawal Ibrahim wanda aka fi sani da Alhaji Awalu a Ungwar Rogo da ke kan titin Bauchi a birnin Jos, sakamakon kama abokan barnarsa Ado Saleh da Bayero Adamu. 

Wakilinmu ya ce ganau sun shaida masa cewa jami’an DSS sun kama Alhaji Auwalu ne a garin Jos, a kofar tashar mota ta Titin Bauchi da ke garin Jos. 

Wani da ya gane wa idonsa yadda jami’an tsaron suka kama mutumin, ya shaida wa Aminiya cewa jami’an tsaron na DSS sun tare mutumin ne, a daidai wajen da ake sayar da lemo da kankana a kofar tashar da misalin karfe 7:30 na safiyar ranar. 

Ya ce ganin mutumin yana kokarin ya gudu ne ya sanya jami’an tsaron suka harbe shi a kafa suka tattara shi suka jefa a mota.

Wata majiyar ta shaida wa Aminiya cewa, an ga mutumin yana ta kaiwa da komawa a kofar tashar, yana buga waya.

 “Shi ne wanda ake zargi da kashe wani ma’aikacin gwamnatin Jihar Filato mai suna Daanan Balgnan, a ranar 30 ga Disamban bara, kuma yana da hannu a wasu sace-sacen mutane a jihohin Nasarawa da Kaduna da Bauchi,” in ji DSS.

“Kuma an same su da Naira miliyan daya da rabi wani bangare na Naira miliyan biyu da suka karba fansa daga Ayuba Gamale, wani ma’aikacin Hukumar Horar da Ma’aikata ta kasa (ITF), wanda aka sake iyalansa biyu da aka sace a ranar 14 ga Maris din nan,” inji sanarwar.

Kazalika kuma a ranar 7 ga Maris jami’an DSS sun kama wani mai suna Sesugh Aondoseer, wanda babban kwamandan “gungun ’yan ta’adda ne” da Terwase Akwaza wanda aka fi sani da Ghana, ke jagoranta a kusa da Babbar Kasuwar Makurdi a Jihar Benuwai.

Ana zarginsa da kitsa sace mutane da dama da fashi a hanyoyin Katsina Ala zuwa Ukum da Gboko zuwa Makurdi da kuma Takum a Jihar Taraba.

Ba ya ga rikicin addini da na kabilanci da satar mutane don karbar kudin fansa, akwai kuma rikici tsakanin manoma da makiyaya, wanda shi ma ke kara yaduwa a kasar nan. Kuma hakan na jawo asarar dimbin rayuka da dukiyoyi, duk da kokarin da gwamnati ke yi don kawo karshen matsalolin.

Kawo yanzu mutanen da ake zargin ba su ce komai ba game da sanarwar Hukumar DSS din ba, kuma ba a bayyana lokacin da za a gurfanar da su a gaban kotu ba.

A makon jiya wani rahoto na masana’antar kera makamai ta duniya da Cibiyar Binciken Zaman Lafiya ta Stockholm ta fitar, ya ce an samu karin shigo da makamai cikin kasar nan da kashi 42 cikin 100 a cikin shekara hudu da suka gabata.

Kuma a bara Hukumar Kwastam ta sha kama daruruwan bindigogi da aka shigo da su ba bisa ka’ida ba ta tashar jiragen ruwa ta Legas, inda ake zargin daga Turkiyya aka shigo da su.