Shahararriyar mawakiyar Indiya, Reshma ta mutu

A Lahadin da ta gabata ce shahararriyar mawakiyar fina-finan Indiya, Reshma ta mutu a birnin Lahore na kasar Pakistan, bayan ta sha fama da laulayin kansar makogwaro.  Mawakiyar, wacce asalinta ’yar kasar Pakistan ce, ta mutu ne tana da shekaru 66 a duniya kuma za a dade ana tunawa da ita, musamman saboda zakin muryarta.An […]

Shahararriyar mawakiyar Indiya, Reshma ta mutu

Marigayiya ReshmaA Lahadin da ta gabata ce shahararriyar mawakiyar fina-finan Indiya, Reshma ta mutu a birnin Lahore na kasar Pakistan, bayan ta sha fama da laulayin kansar makogwaro. 

Mawakiyar, wacce asalinta ’yar kasar Pakistan ce, ta mutu ne tana da shekaru 66 a duniya kuma za a dade ana tunawa da ita, musamman saboda zakin muryarta.
An haife ta ne a 1947, a garin Bikaner na yankin Rajasthan na kasar Pakistan. An haife ta ne a cikin iyalin Banjara, inda ta mutu ta bar ’ya’a biyu, namiji da mace, Umair da kuma Khadija. “Ta dauki dogon lokaci cikin laulayi a duk tsawon watan da ya gabata. Ta yi fama da cutar kansar makogwaro tun shekarun baya.” Inji Dokta Rahim, wanda ya kula da ita a asibitin da ta yi jinya, kafin mutuwarta.
Kamar yadda tarihinta ya nuna, a lokacin da aka raba Indiya da Pakistan, iyayen Reshma sun koma birnin Karachi da zama amma ita saboda shahararta a sana’ar wakar fina-finai sai ta ci gaba da zama a Indiya. “Raba kasa ba ta dame ni ba, domin kuwa shi mawaki na kowa ne,” inji ta.
Tun farko dai, Reshma ba ta karanci ilimin waka ba a makaranta, wani ma’aikacin gidan rediyo ne ya gan ta tana rera waka a wani wuri, a lokacin tana ’yar shekara 12 da haihuwa. Shi ne ya shirya, ya dauki muryarta, inda ta rera wakar ‘Laal Meri’ kuma aka saka a gidan rediyon Pakistan. Tun daga lokacin nan aka gano hazakarta a fannin waka. A shekarun 1960 ne ta ci gaba da shahara, inda wakokinta suka yi ta bayyana a gidajen talabijin da rediyo a kasashen Pakistan da Indiya, inda daga bisani kuma ta ci gaba da rera wakokin fim a kasashen biyu.
Wasu daga cikin sahahararrun wakokinta sun hada da ‘Hai O Rabba Nahion Lagda Dil Mera’ da ‘Ankhiyan Nu Rehen de Ankhyan de Kol Kol’ da ‘Dama Dam Mast Kalandar’ da kuma ‘Lambi Judaai’