Shahararrun fina-finan Tom Clancy biyar

A makon jiya ne shahararren marubucin littattafan kirkirarrun labarun yaki, Tom Clancy ya mutu, a Amurka. Ya mutu ne yana da shekaru 66 a duniya. Da dama daga cikin littattafansa, an mayar da su fina-finan yaki na zamani. Cikin fina-finan nasa, ga fitattu kuma shahararru guda biyar, kamar haka:  ‘Hunt for Red October’ Fim ne […]

Shahararrun fina-finan Tom Clancy biyar

A makon jiya ne shahararren marubucin littattafan kirkirarrun labarun yaki, Tom Clancy ya mutu, a Amurka. Ya mutu ne yana da shekaru 66 a duniya. Da dama daga cikin littattafansa, an mayar da su fina-finan yaki na zamani. Cikin fina-finan nasa, ga fitattu kuma shahararru guda biyar, kamar haka:
 ‘Hunt for Red October’ Fim ne da ke kunshe da wasan kwaikwayo da yaki da siyasa da abin al’ajabi. Shahararren dan fim din nan, Sean Connery ne ya jagoranci sauran ’yan wasa, kamar Scott Glenn da Alec Baldwin da James Earl Jones da sauransu. John McTiernan ne ya ba da umurni a fim din.
‘Clear and Present Danger’
 Shi kuma fim ne da ya kunshi fadace-fadace, manyan laifuka, akwai siyasa, sannan kuma ga batun cin hanci da rashawa. Jarumi Harrison Ford ne ya jagoranci sauran ’yan wasa kamar Willem Dafoe da James Earl Jones da sauransu. Sai kuma Phillip Noyce ya ba da umarni.
 ‘Sum of All Fears’
 A wannan fim din, akwai fadace-face da abin al’ajabi da suddabaru da kuma yake-yake. dan fim Morgan Freeman ne ya jagoranci sauran ’yan wasa.
‘Patriot Games:’
kunshiyar fim din ya hada da fadace-fadace da al’ajabi da siyasa da ta’addanci. dan fim Harrison Ford ne jagoranci ’yan wasa, a yayin da mai ba da umarni ya kasance  PhillipNoyce.
‘Submarine: Steel Boats, Iron Men’
Ba kamar sauran fina-finan baya ba, shi wannan an hada shi ne bisa al’amuran da suka faru na zahiri. Jigonsa ya hada da al’amuran ilimi da yaki da sauransu. dan wasa  Robert Lansing ne ya jagoranci ’yan wasa.