Shaida ya fadi ya mutu ana shari’a cikin kotu

Marigayin ya kasance a gaban kotu domin ba da shaida a wata shari’a da ta shafi abokinsa.

Shaida ya fadi ya mutu ana shari’a cikin kotu

Kotu

Wani dattijo da ya wuce shekara 70, ya faɗi ya mutu a cikin kotu yayin da ake zama a babbar kotun jihar Ondo, a ranar Laraba.

Aminiya ta gano cewa marigayin ya kasance a gaban kotun da ke Ondo, hedikwatar ƙaramar hukumar Ondo ta Yamma domin ba da shaida a wata shari’a da ta shafi abokinsa.

Wani ma’aikacin kotun da ya nemi a sakaya sunansa, ya shaida wa wakilinmu cewa ba zato ba tsammani mutumin mai shekaru sama da 70 a duniya ya faɗi a cikin kotun yayin da aka ambaci shari’ar da bayyana shi a gaban kotun.

“Mutumin yana kotu ne tare da abokinsa, kwatsam, sai ya mike a inda yake zaune ya fadi, ya buga kansa a kan tayal kuma ya rasu.

“Bai yi kama da wanda ba shi da lafiya ba, kuma bai yi hulɗa da kowa ba, amma ba zato ba tsammani ya rasu,” in ji shi.

An samu rahoton cewa ’yan sanda daga sashin Enu-Owa da ke Ondo ne suka ɗauko gawar dattijon suka ajiye a ɗakin ajiye gawa.

Jami’ar hulɗa da jama’a ta rundunar ‘’yan sanda a jihar, Funmilayo Odunlami-Omisanya, ta tabbatar wa da Aminiya faruwar lamarin.

Ta ce, ana kan bincike, inda ta jaddada cewa an mayar da shari’ar zuwa sashin kisan kai na hedikwatar ’yan sanda da ke Akure.

Tags