Shaidu na kara nuna Saudiyya ta kashe Dan jarida Kashoggi

Daga cikin mutum 15 da muka ruwaito makon jiya cewa ana zarginsu da hannu a Bacewar Dan jaridar nan Jamal Khashoggi wanda ya B ace kuma ba a samu labarinsa, an tabbatar da cewa akwai Maher Abdulaziz Mutreb wani na hannun damar Yariman Saudiyya mai jiran gado Muhammad bin Salman ne. A makon jiya, Aminiya […]

Shaidu na kara nuna Saudiyya ta kashe Dan jarida Kashoggi

Daga cikin mutum 15 da muka ruwaito makon jiya cewa ana zarginsu da hannu a Bacewar Dan jaridar nan Jamal Khashoggi wanda ya B

ace kuma ba a samu labarinsa, an tabbatar da cewa akwai Maher Abdulaziz Mutreb wani na hannun damar Yariman Saudiyya mai jiran gado Muhammad bin Salman ne.

A makon jiya, Aminiya ta ruwaito cewa ana zargin waDansu mutum 15 da alhakin Bacewar Jamal a karamin ofishin Jakadancin Saudiyya da ke birnin Istanbul a kasar Turkiyya ciki har da wani da ake kyautata zaton Bahaushe ne mai suna Abdul’aziz Alhawsawiy waDanda aka tabbatar da shigowarsu kasar a wasu kananan jirage guda biyu, kuma suka shiga ofishin Jakadancin a daidai lokacin da Jamal Din ya shiga. Ficewarsu ke da wuya, aka nemi Jamal sama ko kasa aka rasa.

Shi dai Maher Abdul’aziz wanda tsohon Jakadan Saudiyya ne a Amurka, yanzu haka yana cikin waDanda hukumomi a kasar Turkiyya suke bincika da hannu kan Bacewar Jamal ko zargin kashe shi.

Maher ya taBa zama Sakataren Ofishin Jakadancin Saudiyya a Landan kamar yadda CNN ya gano daga jerin sunayen ma’aikatan ofisosin jakadancin da ke Landan a shekarar 2007. Sannan ya kai matsayin Kanar a jami’an tsaron sirrin Saudiyya.

Haka kuma CNN ya gano cewa Maher yana daga cikin na hannun damar Mohammad bin Salman, Yarima mai jiran gado, inda ake yawan ganinsu tare. Sai dai kuma CNN ya ce takardar shaidar shiga kasarsa bai cikin waDanda Turkiyya ta ba su guda 7.

Jakadan Saudiyya a Turkiyya ya tsere

A wata muryar da aka Dauka da kafar labarai ta mailonline ta birnin Landan ta jiyo, ta yi zargin cewa muryar da ta jiyo na Jakadan Saudiyya a Turkiyya Mohammed Al-Otaibi ne lokacin da yake faDa wa waDanda ake zargi da Bacewar Jamal cewa kada su ‘jefa shi cikin matsala’ inda yake cewa su fita waje. Sannan su kuma suka ce masa ya kama bakinsa.

Idan har ya tabbata cewa da gaske ne wannan maganar da muryar da ake cewa an jiyo, duk da cewa ba a sake ta a duniya ba, lallai wannan kaDai ya isa ya tabbatar da cewa an kashe Jamal ne a cikin ofishin Jakadancin Saudiyya.

Haka kuma ’yan sandan Turkiyya sun ce sun samu wata babbar hujja da take nuna cewa an kashe Jamal ne, inda hukumomi a Turkiyya suke zaton muryarsa ce.

A daidai lokacin da ake kara kaimi wajen bincike ne, Babban Jakadan Saudiyya a Turkiyya Otaibi ya tsere daga kasar a jirgin haya jim kaDan kafin ’yan sanda su shiga gidansa domin bincike.

Yanzu haka wasu rahotanni da ba a tabbatar ba sun ce kasar Saudiyya ta kori Mohammed Al-Otaibi daga matsayinsa na Babban Jakadan Kasar a Turkiyya sannan za a bincike shi kamar yadda jaridar The Sun ta ruwaito.

Manyan kasashen duniya sun sanya baki

Bacewar Dan jaridar ta sanya kasar Saudiyya a idon duniya, musamman kawarta Amurka. A wata sanarwa da manyan kasashe masu tattalin arziki wato G7 suka fitar, sun ce suna cikin ‘damuwa’ bisa Bacewar Jamal Kashoggi.

“Dole waDanda ake zargi da Bacewarsa su fuskanci hukunci,” kamar yadda sanarwar ta fito.

“Muna kira ga kasashen Saudiyya da Turkiyya su haDa hannu wajen bincike, kuma muna sauraron kasar Saudiyya ta yi binciken kwakwaf cikin sauri kuma a fili kamar yadda ta sanar za ta yi,” inji shi.

A Bangaren Shugaban Amurka Donald Trump ya ce akwai yiwuwar waDansu miyagun masu kisa ne suka kashe shi.

Shugaba Donald Trump ya ce Sarki Salman na Saudiyya ya bayyana masa haka ne a wata tattaunawa da suka yi ta tsawon minti 20 ta tarho

“Ba za mu bar komai a rufe a kan wannan batu ba. Sarkin Saudiyya ya ce ba ya da masaniya a kan kisan, kuma tana yiwuwa bai sani ba. Ba zan ari bakinsa in ci masa albasa ba, amma dai ina gani waDansu miyagun masu kisa ne suka aikata, amma wa ya san gaskiyar? Za mu yi kokari mu kai ga karshen wannan batu nan ba da DaDewa ba,” kamar yadda Muryar Amurka ta ruwaito.

Saudiyya kawarmu ce amma za mu binciki lamarin – Trump

Shugaban  Donald Trump ya ce Saudiyya abokiyar kasuwancinsu ce domin tana sayen makamai a wajensu, “Saudiyya na sayen makamai da wasu kayayyaki a wajenmu. Amma duk da haka za mu binciki abin da ya faru sosai, sannan muna fata za mu samu cikakken bayanin abin da ya faru kafin karshen wannan mako,” inji shi.

Da wakilin CNN ya tambayi Trump a kan sautin muryar da ake magana an samu, sai ya ce har yanzu bai tabbatar akwai sautin muryar ba, amma, “Mun bukaci a kawo mana sautin muryar ko bidiyon idan har akwai shi.”