Shakar dattin safarsa ya sa ya kamu da ciwon huhu
An kwantar da wani matashi kan kamuwa da cuta a huhunsa a asibiti birnin Zhangzhou a kasar China, bayan ya kamu da cutar ta hanyar shakar dattin safar kafarsa a kullum idan ya dawo daga aiki. Mara lafiyar haifafen birnin Zhangzhou a lardin Fujian da ke Kudancin China, yana da dabi’ar duk lokacin da ya […]
An kwantar da wani matashi kan kamuwa da cuta a huhunsa a asibiti birnin Zhangzhou a kasar China, bayan ya kamu da cutar ta hanyar shakar dattin safar kafarsa a kullum idan ya dawo daga aiki.
Mara lafiyar haifafen birnin Zhangzhou a lardin Fujian da ke Kudancin China, yana da dabi’ar duk lokacin da ya dawo gida daga wajen aikinsa zai canja kayan jikinsa, sai ya zauna ya yi ta shakar dattin zufar safar kafarsa da ya saka a ranar.
Sanadiyyar shakar dattin safar ya sa ya kamu da wata cuta mai kama da hunhuna a jikin huhunsa inda take ta yaduwa duk lokacin da ya yi numfashi.
Ma’aikatan asibitin sun a jiye mutumin a sashin kula da marasa lafiya cikin gaggawa, kuma sakamakon daukar hoton cutar da ke damunsa ne aka tabbatar yana dauke da cutar huhu kuma yanzu ana ci gaba da yi masa magani a asibitin.
Binciken likitocin ya tabbatar da cewa, mutumin ya kamu da cutar ce ta hanyar shakar safarsa a koyaushe.
Rahotanni sun bayyana cewa, shekaru da dama jama’a na sunsuna safar kafarsu, amma irin wannan ba kowa ya sani ba illa kadan.
Sai dai akwai rahoton da yake bayyana cewa, a farkon bara an samu wata budurwa ’yar shekara 21 a kasar Amurka, ta bayyana cewa mahaifinta yana da sha’awar safar kafarta lokacin da safar ta yi zufa kuma a shirye yake ya biya kudade a kan ya mallaki safar.