Shake dalibin makarantar yaran sojoji aka yi ya mutu – Binciken Likita
Dalibin makarantar yaran sojojin nan ta Zariya (NMS)) mai suna Hamza Muhammed dan’azumi da aka tsinci gawarsa a bakin ruwa a kwanakin baya, binciken likitoci ya nuna cewa ya rasa ransa ne ta hunyar shake shi da aka yi.Idan za a iya tunawa Aminiya ta ranar 5/4/2013 ta kawo labarin mutuwar wannan dalibi, inda aka […]

Dalibin makarantar yaran sojojin nan ta Zariya (NMS)) mai suna Hamza Muhammed dan’azumi da aka tsinci gawarsa a bakin ruwa a kwanakin baya, binciken likitoci ya nuna cewa ya rasa ransa ne ta hunyar shake shi da aka yi.
Idan za a iya tunawa Aminiya ta ranar 5/4/2013 ta kawo labarin mutuwar wannan dalibi, inda aka tsinci gawarsa a kusa da wani kogi da ke kusa da makarantar.
Binciken da likitoci a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Ahmadu Bello da ke Shika Zariya a Jihar Kaduna suka aiwatar wanda sakamakonsa ya fito dauke da sa hannun wani kwararren likita kuma shugaban sashin binciken cututtuka na jami’ar (Department of Pathology, ABUTH) Dokta M.S Shehu da Aminiya ta samu kwafe ne ya tabbatar da hakan.
Yayin da yeke zantawa da Aminiya a Zariya mahaifin marigayin Malam Muhammadu Ali dan’azumi ya ce sakamakon binciken ya tabbatar da zarginsa na cewa kashe dansa aka yi.
Malam Ali dan’azumi ya ce hukumar kare hakkin dan Adam da ke Kaduna tana nan tana jiran sakamakon binciken “saboda haka zan je in ba ta kwafinta, sa’annan in ba lauyana kwafi. Shi dai wannan sakamakon binciken mun karbe shi ne daga Asibitin Koyarwar na Jami’ar Ahmadu Bello a ranar Juma’a 30/08/2013, kuma a wajen karbar sakamakon mun je tare da jami’in dan sanda mai bincike (IPO) da ke kula da al’amarin tun lokacin da abin ya faru da kuma wakilin makarantar yaran sojojin ta Zariya a karkashin shugabancin Kyaftin A.O Adeleke,” inji shi.
Malam dan’azumi ya ce “Dole zan je kotu saboda kashe min da da aka yi saboda rashin tausayin wadanda ya kamata a ce sun kula da shi, kuma zan ci gaba da bin hakkinna har sai na ga karshensa, kuma na tabbata Allah Zai taimake ni a kan hakkina da hakkin dana.”
Shugaban Asibitin Koyarwar na Jami’ar Ahmadu Bello, Farfesa Lawal Khalid ya ce tsaikon da aka samu na samun sakamakon binciken, ya faru ne saboda wasu bangarorin binciken sai da aka kai su Legas domin a wannan asibitin babu kayan gwajin.
In za a iya tunawa an samu gawar dalibi Hamza ne a bakin wani kogi kusa da babban gidan ruwa na Zariya da ke kusa da makarantar, bayan hukumar makarantar NMS ta shaida wa mahaifin marigayin cewa yaronsa yana tsare, kuma ba zai gan shi ba za a ci gaba da tsare shi har sai hutun Ista.
Malam dan’azumi ya dora laifin mutuwar dansa ne a kan wata jami’ar soja mai mukamin Laftana mai suna Udah da ke makarantar. Ya ce ita ta kulle dansa saboda bai yi mata kyauta ba a lokacin ziyarar duba yara dalibai da ake yi lokaci-lokaci.