Shalelen dan malele
Amintattun ’yan makarantar Dodorido, masu koyon watsattsake da buda wagagen littattafai a wannan farfajiya da ke cikin Amintattar jaridar kasar Haurobiya, kowa ya ga ni ko yaji yadda dama-dama-dakurda-kurdar siyasar Haurobiya ta koma wasan Samson Siya-siya da kwanyar al’umma, inda ake ta takaddama kana shaidar kamala koyon watsattsaken Shugaban Burin-huriyya na jam’iyyar maganin radadin kurungu. […]
Amintattun ’yan makarantar Dodorido, masu koyon watsattsake da buda wagagen littattafai a wannan farfajiya da ke cikin Amintattar jaridar kasar Haurobiya, kowa ya ga ni ko yaji yadda dama-dama-dakurda-kurdar siyasar Haurobiya ta koma wasan Samson Siya-siya da kwanyar al’umma, inda ake ta takaddama kana shaidar kamala koyon watsattsaken Shugaban Burin-huriyya na jam’iyyar maganin radadin kurungu. Jiga-jigan jam’iyya mai dan boto da sanda jirge suke tya tufka da warwara don kada Haurobiyawa sun Ankara da irin aika-aikar da suka tafka tsawon shekarun mulkin mulaka’u na Jomna-tantin mulki da gudu a cikin loko.
karshen tika-tika tik! Wannan jimurdar damo-da-kura-da-diyya babu inda za ta kai Haurobiyawa illa duhun-dundumdurundum da yamutsin Haramta Bobo da kwambon bokoko da kwashi kwaraf da dukiyar al’umma. Don wadannan mutane sun kusa yi wa lalitar kasar nan karkaf. Masu kada kuri’u ba sai mun kakaba muku tagiyar Malam Tunau ba, domin kuna nan Maimartaba Masanin Sisi-da-sisi ya koka kan yadda aka tatuke lalitar kasar Haurobiya, inda aka wafci Dalar Hauron Amurkawa karamin lauje.
Kai illar Jam’iyya mai dan boto da sand ajirge bai tsaya kan al’ummar kasa ba, har ma cin dunduniya junansu suke yi. Kowa ya san yadda aka Bangaje Banga-banga Tukururu, ga Dumu-dumu Muzu-muzu yana tangal-tangal.
Sanin kowane Bahaurobiye ne cewa, Asarar-dan-kwabo da Kansakalin-kuku na kada kugen tada yamutsi, matukar aka daina Jona-tantin mulkin mulaka’u da gudun loko. Ga samarin kusu da ’yan matan jaba da gafiya, wadanda suka mayar da gama-garin Haurobiyawa ’ya’yan bora.
Ganin irin tabargazar da mai dan boto ta tafka a tsawon shekarun da ta shafe ta jan ragamar al’umma, tun daga shekarar alif sili da manuniyar kasa da ta kasa da ta kasa zuwa shekara ta dubu karamin lauje da sili da babban lauje suna ta kada mana jauje.
Haurobiyawa, idan muka ganganda muka zabo maganin zogi da radadin kurungu, kusan kowane Bahaurobiye sai ya zama dan lele. Shi ke nan sai a rika yi mana wakar shalelen dan malele. ’Yan makaranta a yi tar era wadannan baituka.
Rokona ga Mai-duka
Don alfarma ta Ma’aikinka
Mai tsira amincinka
Game ahali da sahabban dan aikenka
Mabiya mu tattaru a tafarkinka
Na yi male-male
Ina waken dan malele
A batuna babu surkulle
Sannan ba na zuki-ta-malle
Balle walle-walle
Shalelen dan malele
dare bisa amale
Yau ka zama dan lele
Kwashi kabakin alale
Dankwafe masu tsalle-tsalle
Ina buga maka talle
Ba wani kulle-kulle
Ga kwadon kuli da zogale
’yan mata a yafa gyale
A rage kyale-kayle
Ni ne dai namijin zinaru
Dodon babbaku da farfaru
A baza na-zomo a karu
karfin karafa ya tattaru
Mikiya ta fi tantabaru
Nakasar Haurobiya ta zarta guragu
Tana fama da ciwon kugu
An yi wa kasa rugu-rugu
Mu taho gungu-gungu
Mu kwankwadi maganin ciwon kurungu
Ga taguwa babu maballi
Madinki direban alli
Sanyaki sai Santali
Ya fito yana walwali
Ya yi mana maganin masu gantali
Ina masu kalle-kalle
Na bude muku labule
Na-mujiyarku ya zamto a gwale
Batun ingarma ya zama dole
Waskiya tuni ta cale
Ina ladar direbobin alli
Bokan Turai ya ga taskun balbali
’yan kwadago sun tayar da balli
Wanzami ya iya balli-balli
Ga kwas-kwas da solsali
Mai dan boto da sanda jirge
Masu aikin kurege
Tsimi da ta’adin zabge-zabge
Sun tafka ta’asa wai sun burge
Masu reto ya na jemage
Shalele ya shalle
Ana ta bug amasa talle
Tubani da dangauda da alale
Ka dundumee kururu Baballe
Hakin sama an bar wa amale
Kirawo mini Malam Sale
Ya taho da Salele
Amma ban da mai mele
Fatar jiki nai ta sale
Mai fatsi-fatsi ba ya kyale-kyale
Banbamin-maina na yi maka bille
Ba ni bari ka zille
Ko ka dauki sulalla ka sulale
Makamar miyagu duka ta balle
An fasko su suna ta jele
Ko kun shiga kwale-kwale
Isgilinku ya gille
Kuna jimami a sulale
Haurobiyawa sun daddale
Ku kuw akun makale
Mai sunan sulalla a sake lale
Banbamin-maina babu wuri a Sapele
Ka koma gayauna ka yi kale
Tun tale-tale
An fasko sai kun sagale
Angon Haurobiya Baballe
An lullube amarsu da gyale
Za mu kwashi dan malele
Kar a bar mu da kale
Sai mun yi male-male
Kai Malam Namando
kanen mai harigido
An ce ka rasa gado
Ko ka shirya karo da Dodo
Mulkin Haurobiya babu gado
Haurobiyawa mu yunkura wajen Kare kasarmu daga sharrin su Asarar-dan-kwabo da Kansakalin-kuku da In-gwangwaje-in-wala da Santala kwaiduwa da Baudadden Joji da Malam Namando da sauran masu kwasar gararuma. Mu dai ba zka mu bari a yamutsa ba. Lallai mu yi juyin aya takanda, amma ban da juyin wainar matar mai sana’ar na-duke. Lokaci ya yi da za mu shalle, mu bi shalelen dan malele, myagu kuwa dole ne su cale.