Shan miyagun kwayoyi na taimakawa wajen rura wutar rikice-rikice a kasar nan – Akibishop Kaigama
Bishop din Cocin Katolika na Jos Akibishop Ignatius Kaigama ya ce shaye-shayen miyagun kwayoyi da sauran kayan maye da matasa ke yi, na taimakawa wajen rura wutar rikice-rikice a kasar nan. Akibishop Ignatius Kaigama ya bayyana haka ne a lokacin da yake jawabi a wajen wani taro da cibiyar tattaunawa kan hanyoyin samar da zaman […]
Bishop din Cocin Katolika na Jos Akibishop Ignatius Kaigama ya ce shaye-shayen miyagun kwayoyi da sauran kayan maye da matasa ke yi, na taimakawa wajen rura wutar rikice-rikice a kasar nan. Akibishop Ignatius Kaigama ya bayyana haka ne a lokacin da yake jawabi a wajen wani taro da cibiyar tattaunawa kan hanyoyin samar da zaman lafiya ta DREP dake Kwang a kusa da garin Jos, ta shirya wa shugabannin addini da na al’umma kan hanyoyin magance shaye-shayen miyagun kwayoyi da matasa ke yi.
Ya ce shaye-shayen miyagun kwayoyi sun taimaka a rikice-rikicen da aka yi a kasar nan, musamman a Jihar Filato. “Ya zama wajibi gare mu a matsayinmu na shugabannin addini da na al’umma mu tabbatar cewa matasa sun samu tarbiyya domin kasancewa shugabanni nagari a nan gaba, ta hanyar tsayawa wajen ganin an hana sayar da miyagun kwayoyi da sauran kayan maye a kasar nan,” inji shi.
A jawabin Kwamandar Hukumar Yaki da Tu’ammali da Miyagun kwayoyi ta kasa (NDLEA) a Jihar Filato, Dokta Ngozi Madubuike ta ce hukumarta tana iyakar kokarinta wajen yaki da sha da hana fataucin miyagun kwayoyi a jihar.
Tunda farko a jawabin Daraktan Cibiyar ta DREP, Mista Blaise Agwom ya yaba wa Majalisar Dokokin Jihar Filato, kan kokarin da take yi na kafa wata doka ta hana sha da sayar da miyagun kayan maye a jihar. Ya ce wannan kokari da majalisar ke yi, zai yi matukar taimakawa wajen ceto matasa da sauran jama’ar da suke mu’amula da miyagun kwayoyi da kayan maye a jihar.