Shan ruwa a fadar sarkin Kano, Allah maimaita mana
A ranar Laraba 15-07-2015, wadda ta yi daidai da 28-09-1436, ina kan hanya sai na ji waya, a lokacin da na amsa kiran sai na ji muryar matar wani aminina da muke tare tun muna samari a Kaduna. Bayan mun gaisa sai ta ce da ni mai girma dan Majen Kano kuma shugaban ma`aikatan Fadar […]
A ranar Laraba 15-07-2015, wadda ta yi daidai da 28-09-1436, ina kan hanya sai na ji waya, a lokacin da na amsa kiran sai na ji muryar matar wani aminina da muke tare tun muna samari a Kaduna. Bayan mun gaisa sai ta ce da ni mai girma dan Majen Kano kuma shugaban ma`aikatan Fadar Sarkin Kano Alhaji Munnir Sanusi, ya ba da katin gayyyar shan ruwa a kawo ta hannunta ta bani, don halartar shan ruwa da Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Muhammadu Sanusi na II, Sarki na 14, a cikin Daular mulkin Fulani a Kano.
Da ma kuma ina kan hanyar wajen gidansu ne, don haka sai na biya. Ina zuwa sai na tarar da mai gidanta, bayan an gaisa, na tsokane ta a kan abin da na saba na ta hana mijinta ya yi ma ta kishiya, har ina cewa da ita sai ta biya Malamanta, aka dai yi dariya kamar yadda aka saba, sannan ta dauko katin gayyatar ta mika mini. A nan sai na tambaye ta ina na mijinta? Sai ta ce da ni, ai ba ta je fada ba, da ta je da ta karbo masa. Lokacin da na gama karanta katin nan take sai fahimci cewa a wannan ranar ta Laraba za a yi shan ruwan kuma Mai Martaba Sarki da kansa yake gayyatar, har aka kara da cewa a zo karfe bakwai kuma a shigo fadar ta kofar Kudu, wadda ita ce fitacciiyar kofa daga cikin kofofin fadar da ake shiga gidan yau da kullum.
Bayan zuciyata ta natsu a kan zan amsa gayyatar, sai kuma na fara tambayar kaina wannan shan ruwa da zai zama na farko irinsa a gare ni. Shin dama ana yinsa, kuma wadanne irin jinshin mutane ake gayyata, irin shan ruwa da gwamnonin jiha ne da a kan shirya a cikin goman karshe da akan gayyato kungiyoyi daban daban? Wato ma`ana namu na wannan yinin shi ne na takwas kasancewar ranar ita ce 28 ga watan na Ramadan, idan shi ne, mu manema labaria da su wa da wa aka hada mu? Shan ruwa ne na `yan mutane kalilan ta yadda kusan kowa zai samu tattaunawa da Mai Martaba Sarki? Ba don kome ba irin wadancan tambayoyi da makamantansu suka rinka zo ma ni a zuciya ba,sai don a dukka tsawon zama na Kano na aikin jarida, yau shekaru kusan 32, ban taba jin labarin Sarkin Kano ya gayyaci talakawa shan ruwa ba. Sai bayan shan ruwan ne ma na samu labarin cewa a cikin tarihin mulkin Daular Fulani da aka fara da Sarkin Kano Sulaiman a shekarar 1807, yau shekaru 208, babu wani Sarkin Kano da ya taba gayyatar jama`ar gari shan ruwa,da watan azumi sai Sarki Muhammadu Sanusi na II, wanda ya zo kan karagar mulki a ranar 08-06-2014, wato kusan shekara daya da wata daya da kwanaki 8, a lokacin da a kai wannan shan ruwa.
Lokacin da karfe bakwai ta karoto, sai na doso fada, ina zuwa kuwa tun daga filin kofar kudu har zuwa karshen inda mota kan tsaya a cikin fadar, cike suke makil da motoci, ganin haka kuma sai na fara samun amsar cewa wannan shan ruwa, shi ne na farko a wannan watan, kuma ya kunshi kowa da kowa. Don haka na ajiye mota a filin na kofar kudu, na taka zuwa cikin fada. Ina zuwa sai na tarar har an yi raka`a daya, don haka na bi Liman aka karasa da ni, sannan na ciko raka’ar da ta kubuce mani. Ida sallah ke da wuya, sai kuma aka matsa gaba kadan inda aka shiga daya daga cikin Majalisun da ke cikin fadar, da ake wa lakadi da dogon falo, inda muka tarar an shirya kayan shan ruwa na alfarma a kan teburan alfarma.
Mai karatu in bayyana maka irin kayayyakin shan ruwan da aka tanada da wurin da aka zauna din, mai yiwuwa ka ce na yi karin gishiri, amma zan iya barin ka ka kaddara a ranka dukkan abin da ake tanada don a sha ruwa a wuri ko gidan da ya isa, to, akwai shi a wurin. Haka shi ma dogon falon da ka sha rowan da tebura da kujerun da yadda aka kawata falon, sai ka kaddara a zuciyarka cewa wata rana manyan baki irin su shugaban kasa da mutanensa za a saukar da su a wurin don su sha ruwa. Amma dukka da wannan shiri da aka yi, ga kuma Mai martaba Sarki zaune, sai da Hukumar wutar lantarki ta dauke wuta har sau biyu.
Daga yadda na fahinci mutanen da aka gayyata shan rowan, sun fito ne daga sassan al`umma daban-daban. Da farko dai akwai mai girma gwamnan jihar Kano Dokta Abdullahi Umar Ganduje da Kwamishinoninsa, da karamin Jakadan kasar Saudiyya da ke Kano, daga bangaren `yan Kasuwa akwai Khalifa Sheikh Isiyaku Rabi`u (wanda ka iya cewa tudu biyu ya ke ci, kasuwanci da Malantaka), akwai `yan kasuwa irinsu Alhaji Bature Abdulaziz da Alhaji Sabi`u Bako da Alhaji Umaru dansuleka shugaban Cibiyar Kasuwanci, Masa`antu, Ma`adanai da Ayyukan gona na jihar Kano da sauran `yan kasuwa. Ta bangaren Malamai ko Limamai akwai Babban Limamin Kano Farfesa Sani Zahradden da Limamin masallacin juma`a na Al-Furkan Dokta Bashir Aliyu Umar da Limamin masallacin Juma`a na Sheikh Ahmadu Tijjani da ke kofar mata Sheikh Muhammad Nasir Adam da Limamin Masallacin Murtala Malam Kabiru Badamasi dan Taura da Limamin Nomans Land Malam Munnir dan Amu da sauran Maluman addinin islama.
Daga bangaren `yan Boko, musamman Malaman Jami`a akwai Farfesa Shehu Galadanci da Ambasada Farfesa dandatti Abdulkadir da Farfesa Bello Salim, akwai kuma Dokta Kabiru Abubakar tsohon Daraktan Assibitin kashi na Dala. Hakimaikuwa ba a magana. Gaskiyar magana mai karatu mu da aka gayyata shan wancan ruwa, mun haura mutane dari, kuma shan ruwan da ba wanda zai ce bai sha ko ya ci abinda yak e so ba. Allah bada lada.
Mutane hudu suka yi jawabi, wato gwamna Abdullahi Ganduje da Sheikh Isiyaku Rabi`u da karamin Jakadan kasar Saudiyya da shi kansa mai masaukin baki, wato mai martaba Sarki, amma saboda karancin fili na mutane biyu kawai zan iya kawowa. Sheikh Isiyaku ya fadi cewa shekaru baya kafin mutuwar Sarki Ado Bayero, kusan duk shekara, sai sun yi maganar bukatar da ke akwai fada ta shirya shan ruwa irin wannan, amma Allah bai nufa ba, sai a lokacin Sarkin Sanusi II, don haka ya yabawa Sarkin a bisa ga wannan hangen nesa nasa da kuma kokarin hada kan mutanensa.
Shi kuwa mai martaba Sarki a cikin nasa jawabin, dalla-dalla ya yi inda ya fadi cewa makasudin kiran shan ruwan bai wuce don neman hadin kan mutanen jihar ba akalla ko da a zaman bangarorinsu, inda ya kara da cewa inda aka samu kan hadin kan Malamai, darajar Malamantaka za ta dawo, haka samun hadin kan `yan kasuwa, martabar kasuwanci za ta dawo a Kano ta yadda Kano za ta ci gaba da rike kanbinta na kasuwanci, hakaakan su Sarakuna, Sarkin ya tabbatar da cewa muddin shi da Hakimansa da Dagatai da masu Ungunni za su mulki cikin kamanta gaskiya da adalci, to, kuwa martabar sarautar Kano itama za ta dawo. Kafin wannan shan ruwa Mai martaba Sarki ya kai ziyara gidajen Kurkuku biyu da suke cikin birnin Kano, watona Kurmawa da Goron Dutse, inda ya fanshi wasu `yan kurkuku da bashi ya jaza masu zaman sarka da tsabar kudi sama da Naira miliyan 6.
Ba ko shakka maganar da ake ciki tun tuni ba tun yau ba, irin zaman `yan marinar da ake a arewacin kasar nan musamman tsakankanin Hausawa, da a kullum za a tarar ba su da shugaba, inda ya ke biyayya gare shi na karanci. Don haka wannan danba da Mai martaba Sarki ya kafa lalle abar a kama masa ce, musamman yadda ya ce shi a shirye ya ke wajen rungumarharkokin Talakawansa a koda yaushe. Don haka su ma Talakawan (musamman wadanda suka halarci shan ruwan), sai su kama ma kansu, kamawarsu zata sa sauran mabiya su bi. Sauran Sarakuna ma, wadanda suke nesa da jama`arsu suna bukatar su bude kofofin Fadarsu. Allah Ya maimaita mana wannan shan ruwa na Kano.