‘Shan sigari kan hallaka ’yan Najeriya 29,472 a kowacce shekara’

Cibiyar Bincike Kan Tattalin Arzikin Afirka ce ta tabbatar da hakan a wani rahoto da ta wallafa

‘Shan sigari kan hallaka ’yan Najeriya 29,472 a kowacce shekara’

Wani mashayin sigari

Ministan Lafiya, Dakta Osagie Ehanire ya ce akalla ’yan Najeriya 29,472 ne ke mutuwa a kowacce shekara sakamakon shan taba Sigari.

Ministan, wanda ke jawabi a Abuja yayin bikin ranar yaki da shan Sigari ta duniya ya ce Cibiyar Bincike Kan Tattalin Arzikin Afirka ce ta tabbatar da hakan a wani rahoto da ta wallafa na shekarar 2021.

Ya ce taken bikin na bana mai suna, “Yadda za a kaucewa shan Sigari” ya zo a daidai lokacin da aka fi bukatarsa, musamman la’akari da yadda duniya ta dukufa wajen yaki da annobar COVID-19.

“Hakan baya rasa nasaba da yadda kwararan hujjoji suka nuna yadda masu ta’ammali da taba sigari suka fi barazanar kamuwa da cututtuka masu yaduwa, ciki har da COVID-19. Saboda haka, taimakawa jama’a su daina sha zai taimaka wajen yaki da ita,” inji shi.

Kazalika, Ministan ya kuma lura cewa shan Sigarin kan haifar da kamuwa da cututtuka kamar Hawan Jini, Shanyewar Barin Jiki, Ciwon Suga, Sankara da kuma sauran cututtukan ciki.

Ita ma da take nata tsokacin, Daraka mai kula da nahiyar Afirka ta Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO), Dakta Matshidiso Moeti ta ce hukumar ta zabi Najeriya tare da ragowar kasashe 22 domin shirin tallafawa mutane su daina shan Sigarin tun daga tushe.

Ta kuma yi kira ga Ministan da ya kafa cibiyoyin tuntuba a kowanne sakon kasar wadanda za a aike musu da kwararru domin ganawa da jama’a kai tsaye tare da magance musu matsalolinsu kan daina shan Sigarin.