Shani Shingnapur: kauyen da kofofin gidajensa ba su da kyaure

A kauyen Shani Shingnapur da ke Jihar Maharashtra, ta kasar Indiya, mutanen garin musamman zuri’ar Gade ba sa sanya kyaure a gidajensu, kuma ba wata alama da ke nuna ana tsaurara tsaro. Sukan baje damin kudin Rupees a dakunan kwanansu, duk da cewa kofar shiga gidajensu ba ta da kyaure. Wannan al’ada ta rashin sanya […]

Shani Shingnapur: kauyen da kofofin gidajensa ba su da kyaure
Shani Shingnapur: kauyen da kofofin gidajensa ba su da kyaure

A kauyen Shani Shingnapur da ke Jihar Maharashtra, ta kasar Indiya, mutanen garin musamman zuri’ar Gade ba sa sanya kyaure a gidajensu, kuma ba wata alama da ke nuna ana tsaurara tsaro. Sukan baje damin kudin Rupees a dakunan kwanansu, duk da cewa kofar shiga gidajensu ba ta da kyaure.

Wannan al’ada ta rashin sanya marfin kofa a gidaje, ta samo asali ne shekaru da dama a wannan gari. Kuma mutanen garin mafi yawansu manoma ne, don haka sai su tara damin rage a kan keken shanu, su bi ta gaban gidaje marasa murfin kofa.
“Shekaru da suka gabata, Shani (abin bauta) ya bayyana ga masu ibada, ya sanar da su cewa ba ku bukatar marfin kofa a gidajen ku,” a cewar wata matar aure, Jayashree Gade, a hirar da ta yi da Kamfnain Dillancin Labarai na AFP.
“Zan ba ku kariya. Wannan shi ne dalilin da ya sanya ba mu da kyauren kofa,” inji ta.
Sai dai wasu mazaunan kauyen sun ce suna kange kofar su da daddare saboda dabbobin daji.
Wani abin mamakin shi ne, reshen bankin UCO da ke kauyen, na alfahari da cewa ba a kulle kofarsa. Duk da cewa ana adana kudi a sundukin karfe, kofar shiga ginin ta gilashi ce, wadda ba ta da makulli, ita ma an kanga ta ne don kariya daga mahaukatan karnuka.