Sharhi a kan fim fim din Spartacus Blood and Sand
A yanzu haka, wani fim na kasashen waje, mai suna Spartacus Blood and Sand, yana cin kasuwarsa a Najeriya. Kamar yadda binciken Aminiya ya nuna, fim din yana matukar kasuwa a sassa daban-daban na duniya, ciki kuwa hard a nan kasarmu ta Najeriya.Fim din na tarihi ne, wanda yake kunshe da yadda al’ummar Yahudawa suka […]

A yanzu haka, wani fim na kasashen waje, mai suna Spartacus Blood and Sand, yana cin kasuwarsa a Najeriya. Kamar yadda binciken Aminiya ya nuna, fim din yana matukar kasuwa a sassa daban-daban na duniya, ciki kuwa hard a nan kasarmu ta Najeriya.
Fim din na tarihi ne, wanda yake kunshe da yadda al’ummar Yahudawa suka yi rayuwarsu a can zamani mai dadewa. dauke yake da halayen dagawa da jiji-da-kai irin na al’ummar Yahudawa. Haka kuma fim din ya nuna yadda dangantaka ke kasancewa tsakanin masu rike da sarauta da attajirai a daya bangarem da kuma yadda bayi ke kasancewa cikin kaskancin bauta a karkashin Yahudawa.
Fim din yana kunshe da badala kala-kala, musamman ma dai caca da nuna tsiraici da tantiranci iri-iri, wanda haka ya kara bayyana halayen Yahudawa, kamar yadda tarihi ya dade da bayyana wa al’umma.
Wani abin hadari ga fim din shi ne, mutane na yawan sayensa ne da nufin ganin wadannan sassa na badala da ke cikinsa, alhali wasu, wadanda kalilan ne ke kallonsa saboda nazari da kara tabbatar da tarihin Yahudawa.
Kamar yadda labarin fim din ya fara, shi dai tauraron fim din, mai suna Spatacus (Kirk Douglas), ya kasance wani bawa mai karfin gaske, wanda ya yi wa ubangidansa Bayahude mai suna Lentulus Batiatus (Peter Ustinob) bore. Shi Batiatus, yana da wata makaranta ce, inda yake turke jarumai, wadanda aikinsu kawai shi ne fada a tsakaninsu, ba don komai ba sai domin nishadantar da mutanen birnin Capua da attajirai rarakuma, musamman ma dai Shugaban Yakin Rum, mai suna Marcus Licinius Crassus (Laurance Olibier). Duk lokacin da ya bukaci nishadi, akan hada jaruman fada ne a tsakaninsu, kuma akan yi kisa da takubba ba tare da tausayi ba. Akan zubar da jini muraran, inda kuma ’yan kallo kan yi caca a tsakaninsu, ta hanyar zaben jarumin da ya kwanta musu a rai.
Shi Spartacus, ya kasance cikin wannan makaranta ta jarumai bisa tilas ne, domin kuwa an kama shi ne, aka bautar da shi da tsiya. Ya yi ta atisaye har ya zama jarumin jarumai a gidan. Ya yi ta kokarin ganin ya samu ’yancinsa, inda yake fafata fada da duk wanda aka hada shi da shi kuma yana samun nasara, tare da alkawarin cewa idan ya kai wani adadin lokaci, zai samu ’yancinsa. A bangare guda kuma, Batiatus, maigidansa, ya yi masa alkawarin dawo masa da matarsa, wacce yake matukar kauna, wacce kuma aka sace ta, aka kai ta bauta can wata kasa ta daban. Alkawarin dai shi ne, Spatarcus zai ci gaba da kokari, domin ya fanshi kansa kuma a dawo masa da matarsa.
Sannu a hankali, sai shi Batistus ya hada kai da wani bawansa, domin ya je ya dawo da matar Spartacus, amma a kan hanya ya shirya giri, ya yi mata lahani, inda yana zuwa gida da ita, Spartacus ya same ta jina-jina, kafin ma ta yi wani bayani, ta mutu. Daga nan duniya ta yi masa baki.
Spartacus bai tashi gane makircin da aka shirya masa ba, sai da ya hadu da wata sabuwar budurwa, mai suna barinia (Jean Simmons), ita ce ta shaida masa labarin yadda aka kashe masa mata. Wannan ne kuma ya haddasa ya shiya gagarumar zanga-zanga, inda ya jagoranci sauran jarumai 78 na makarantar, suka yi wa Batiatus bore, inda suka kashe shi tare da munafukar matarsa, sannan suka dauki hanyar tafiya zuwa babban birnin Rum, da nufin ’yanto ’yan uwansu da kuma daukar fansar kisan da aka yi wa matarsa.
Jerin ’yan wasan da suka fito cikin fim din sun hada da Kirk Douglas – Spartacus da Laurence Olibier – Marcus Licinius Crassus da Jean Simmons – barinia da Charles Laughton – Sempronius Gracchus da Peter Ustinob – Lentulus Batiatus da Tony Curtis – Antoninus da John Gabin – Julius Caesar da Nina Foch – Helena Glabrus da Herbert Lom – Tigranes da John Ireland – Cridus da John Dall – Glabrus da Joanna Barnes – Claudia Marius da sauransu.
Wanda ya ba da ummurni a fim din, shi ne Stanley Kubrick, a yayin da Furodusa ya kasance Edward Lewis; sai kuma Kirk Douglas, wanda ya dauki nauyin shiryawa.
Wani abin kula da wannan fim shi ne, yana da matukar hadari, musamman sakamakon binciken da ya nuna cewa mutane da dama, maza da mata suna kallon fim din a gidajensu. Hasali ma, kwanakin baya a Kano, a lokacin da ake gasar kwallon duniya; na taba shiga wani gidan kallo, da nufin kallon kwallon kafa, kawai sai na ga wani sashi na gidan, wata katuwar talabijin na nuna wa wasu ’yan kallo wannan fim na Spartacus. Da aka zo wani wuri, dole aka kashe fim din, aka canja shi da wani, saboda tsintsar badalar da ke cikinsa.
Shawarar da zan ba masu kallo shi ne, idan har ya zama dole su kalle shi, to su yi da kyakkyawar niyya, da nufin ganin tarihin rayuwar tantagaryar Yahudawa, domin kauce wa irin wannan gurbatattar rayuwa. Haka kuma, lallai a tabbatar ba a bar yara sun kalli fim din ba.
Allah Ya kiyaye mu daga bata, amin!