Sharhi da nazari kan fim din The Lord of the Ring

Littafin hikaya na The Lord of the Ring, babu ko tantama, yana daya daga cikin littattafan duniya da aka yi nasarar mayar da su fim. Duk da cewa ba shi ne kadai littafin da aka mayar zuwa fim ba, amma daga yanayin yadda aka malkwada labarin, duk da cewa yana dauke da abubuwan al’ajabi, kuma […]

Sharhi da nazari kan fim din The Lord of the Ring
Sharhi da nazari kan fim din The Lord of the Ring

Littafin hikaya na The Lord of the Ring, babu ko tantama, yana daya daga cikin littattafan duniya da aka yi nasarar mayar da su fim. Duk da cewa ba shi ne kadai littafin da aka mayar zuwa fim ba, amma daga yanayin yadda aka malkwada labarin, duk da cewa yana dauke da abubuwan al’ajabi, kuma aka fitar da shi sarai, za a iya cewa fim din ya bambanta da kininsa a zamance.
Wani kwararren mai shirya fina-finai, dan kasar New Zealand, mai suna Peter Jackson ne ya samu nasarar mayar da littafin zuwa fim. Fitaccen marubuci, J.R.R. Tolkien ne ya rubuta littafin, inda shi kuma mai shirya fim din ya kasa shi zuwa gida uku, ya fara fitar da kashin farko a cikin shekarar 2001.
Kamar yadda aka tsara shi littafin, fim din na The Lord of the Ring yana ba da labarin wani tsaffaffen zobe ne, wanda mamallakinsa yake amfani da shi wajen juya duniya ta irin yadda yake so. Labarin yana nuna Elijah Wood (Frodo Baggins), wanda wani dan uwansa Ian Holm (Bilbo) ya ba shi kyautar zoben. Daga bisani ne jarumin ya gano cewa ashe zoben ba karamin jidali ba ne, domin tun da ya mallake shi, bai kara samun sukuni ba. Ba shi kadai ba, duk mahalukin da ya rayu a wannan zamani, bai samu kwanciuyar hankali da zaman lafiya ba, har sai lokacin da aka lalata zoben, bayan an jefa shi cikin wata gagarumar wuta.
A lokacin da Frodo ya rike zoben a hannunsa, wani matsafi, Ian McKellen (Gandalf) ne ya ummurce shi da cewa, lallai ya niki gari, ya tafi zuwa wani tsauni mai nisan gaske, kuma mai hadarin gaske, inda a can ne aka kera zoben shekaru dubbai da suka gabata. Ya ce a wannan tsauni ne kadai za a iya lalata karfi da tasirin zoben, wanda haka ne kadai zai kawo wa duniya kwanciyar hankali da zaman lafiya.
Shi kuwa Frodo bai bata lokaci ba, sai ya kuduri aniyar tafiya wannan tsauni, domin ya ceto duniya daga bala’in da ke tattare da wannan zobe da ke wurinsa. Ba shi kadai ya tafi wannan tafiya mai hadari ba, domin kuwa wasu aminansa, mutum takwas sun kasance tare da shi. Wadannan kuwa sun hada da Hobbit Sam (Sean Astin) da Merry (Dominic Monaghan) da Pippin (Billy Boyd). Sauran sun hada da Gandalf da Aragorn (biggo Mortensen) da Boromir (Sean Bean) da Elf Archer Legolas (Orlando Bloom) da Dwarf Soldier Gimli (John Rhys-Dabies).
’Ya’yan wannan tawaga, sun niki gari suka tunkari kasar Mordo, inda a cikinta ne wannan hatsabibin tsauni yake. Sun yi ta tafiya cikin hadari kala-kala, suka ratsa ta masarautar Elfish na Ribendell, sannan suka shiga surkukin dajin Lothlorien. A nan ne suka samu tallafi daga Gimbiya Elf Arwen (Lib Tyler) da babanta Elrond (Hugo Weabing) da Sarauniya Galadriel (Cate Blanchett).
Tawagar Frodo ta yi ta gamuwa da kalubale da barazana iri-iri, inda akwai wani matsafi, wanda ke adawa da mayar da zoben, wanda kuma yake kokarin ganin ya mallaki shi domin bukatar kansa. Wannan matsafi mai suna Saruman (Christopher Lee), wanda kuma dan uwa ne ga Gandalf, amma ya fitsare kafarsa yana adawa da shi. Haka kuma akwai wasu mahara, masu mugun kuduri, bisa jagorancin Sauron (Sala Baker), wanda su ma sun yi ta kawo wa tawagar cikas.
Baya ga wadannan hatsabibai, tawagar Frodo ta yi ta fafata yaki da fada da wasu halittu masu tashi sama da dabbobi masu dauke da iskokai kala-kala. Haka suka yi ta kokari har suka isa kasar Mordor, kuma suka samu nasarar jefa zoben cikin wannan gagarumar wuta. Daga nan kuwa suka koma gida, suka ci gaba da rayuwarsu cikin farin ciki.
Fim din The Lord of the Rings dai kamar yadda aka fada a baya, an kasa shi ne zuwa gida uku, The Fellowship of the Ring (2001) da The Two Towers (2002) da kuma The Return of the King (2003). Mafi yawa daga sassan fim din, an dauke su ne a dazuzzukan kasar New Zealand.

A-Kurkura: Guba ko Magani?

Tsohon Shugaban Jami’ar Ilori, Farfesa Ambali ya rasu

ICPC ta hana El-Rufai ganin likita —Hadiminsa

Hanyoyin zuwa Katsina sun zama tarkon mutuwa