Sharhi da nazarin wakokin Ali Jita

Tun kusan wata hudu ko ma fiye da haka nake zuba ido tare da bude kunnuwana, domin in ji wata jami’a daga cikin jami’o’in Arewa sun kira Ali Jita domin su ba shi lambar girmamawa, kamar yadda Jami’ar Ahmadu Bello ta karrama Dauda Kahutu Rarara amma na ji shiru.Abu ne sananne ga kowace al’umma, cewa […]

Sharhi da nazarin wakokin Ali Jita
Sharhi da nazarin wakokin Ali Jita

Tun kusan wata hudu ko ma fiye da haka nake zuba ido tare da bude kunnuwana, domin in ji wata jami’a daga cikin jami’o’in Arewa sun kira Ali Jita domin su ba shi lambar girmamawa, kamar yadda Jami’ar Ahmadu Bello ta karrama Dauda Kahutu Rarara amma na ji shiru.
Abu ne sananne ga kowace al’umma, cewa mawaki yana da matukar muhimmanci da tasiri. Saboda haka ya kamata ga kowace al’ummar da ta sami mawaki a cikinta, ta yi kokarin jawo ra’ayinsa da karfafa masa gwiwa a kan wakokin da yake yi. Idan ba haka ba, to kuwa zai zamo a kodayaushe zai rika ganin wakarc e kawai yake yi amma ba a kula da sakon da yake isarwa.
Sashen Hausa na Jami’ar Ahmadu Bello ya karrama Rarara mawakin ’yan siyasa, ba don komai ba sa saboda irin gudunmuwar da ya bayar a zaben da ya gabata na shekarar 2015. Ina ganin wannan karramawar da aka yi masa za ta kara ba shi karfin gwiwar ci gaba da yin ingantattun wakoki tare da kauce wa yin gurbatattun wakoki.
Idan kuwa haka ne, to me zai hana a kira Ali Jita shi ma a karrama shi, domin ba shi karfin gwiwa a kan wakokinsa?
Babu ko shakka, idan ana neman mawakin da ya ba addininsa da al’adarsa gudunmuwa domin a karrama shi, to kuwa za a nemo Ali Jita a karrama shi tare da kara karfafa masa gwiwa a kan wakokin da yake yi, ba don komai ba sai don irin sakonnin da yake isarwa a cikin wakokinsa.
Babu wata waka ta Ali Jita da za ka saurara ba ka ji ya ba addininsa da al’adarsa wata gudummuwa ba ko ya take. Misali, a cikin wakarsa ta Rayuwa, ya kawo wasu baituka inda yake cewa:
“Lahira da akwai kallo, shugabanninmu nika tausaya wa.
Masu mulkinmu na yanzu arzikin kasar suka sacewa.
Allah Ka yi sakayya talakawa ba ma yafewa.
Sun bar mu cikin kunci da yunwa, su ke hutawa.
Matasan kasarmu wallahi mu ne aka cutarwa.
Domin in kun gane da bazarmu ne suka takawa.
Allah gatan bawa, bawa gatan aiki ne.
Mai taimakon jama’a, wannan mai tsoron Allah ne.
Alheri mai dadi, mai kyauta ba zai talauci ba.
Masu kudin yanzu burinsu tari ba ci ba.
Mutum daya ya danne dukiya bai san ya yi zakka ba.
Dadin kabari ke nan, ba za a shige shi da sisi ba.
Rayuwa mai ban tsoro, Allah sa ba za mu ji kunya ba.
Wanda duk ya yi zalunci karshensa sam ba zai kyau ba.”
Wadannan baituka idan mutum mai hankali ya dube su da idon basira, zai san cewa wannan talikin ya ba addininsa na Musulunci gagarumar gudunmuwa a cikinsu.
Har wayau a cikin wakar tasa ta Rayuwa, ya ba al’adarsa muhimmanci da gudummuwa mai yawa, domin akwai inda yake cewa:
“A dade ana yi, mai gaskiya ba ya kasawa.
Aka ce ramin karya kurarre ne, ba ya dadewa.
Kuma duk asalin dan birni daga kauye yai yi fitowa.
’Yan matanmu na yanzu ku dinga kishin Hausawa.
Asali shi ne tushe gayu kar ku yi boyewa.
Ta inda aka hau na ji an ce wa ta nan ne za a yi saukowa.
Ni ma dai Ali Jita bara ku ji sunan kauyena.
Kibiya kauyen baba ni ma shi ne tushena.
Mutanen Kano ta Dabo ai kun zama dangina.
Babana Haji Sallau, a garinmu Sarkin Fawa ne.
Na iya sukar tsire da fidar rago kowanne.
In waka tai karewa ai Fawa zan koma ne.
Wanda ke boye asalinsa, wallahi babban baho ne.”
Ina ganin wadannan baituka ba su da bukatar fashin baki ga dukkanin mutum mai nazari da tunani, mai kuma jin Hausa.
Bayan wannan wakar, akwai tulin wakokinsa wadanda ya yi kuma duk na fadakarwa ne, kamar su, Zama Na Aure, Yara Manyan Gobe, Bakandamiya, Mamana da sauransu.
Daga cikin wadannan wakoki nasa, akwai wata wakar wacce a kanta kawai ya kamata a karrama shi. Wakar kuwa ita ce, Labarin Duniya ta 2. Ga dai wakar a rubuce:
“Jama’a ga Ali Jita,
Ya zo zan kada ’yar jitata.
Jama’a ga Ali Jita,
Na zo zan kada ‘yar jitata.
Duniya labarin duniya.
Duniya wayyo duniya.
Zama da masoyi dadi rabuwa da masoyi daci.
In zama da masoyi dadi ai rabuwa sam ba ta da dadi.
Ga wata can tana ta zumudi,
Duniya ba a mata kaudi.
Duniya rawar ’yan mata,
Ni tun tuni na manta ta.
Na gama gane manufarta.
Kai ma malam ajiye ta.
Duniya kuma zancen banza.
Duniya wayyo duniya.
Duniya labarin duniya.
Wata ran ina da budurwa.
Fara take tas kyakykyawa.
Amma don ba ni da Naira na ga takaicin duniya.
Allah ba ni kudin nan ni ma.
Nai sadaka nai kyauta, na huce takaicin zamanina.
Duniya wayyo duniya.
’Yan yara ku je makaranta,
Musamman ma ku mata.
Mai ilimi ta bambanta,
Koda ma a cikin ’yan mata.
Na tausaya wa matasan,
Da ba su da aikin komai,
Sai zaman kashe wando.
Ai maula ba aiki ne ba.
A tausaya wa talakawa.
Don babu ba ta da dadi,
Mai sa gigi da zumudi.
Talauci in kun gane, ba karamin ciwo ne ba.
Arziki daga Allah ne,
Na san shi ne mai yin komai.
Da gari ya wayewa.
Wani zai je aikin gona.
Wani ko shi su zai je.
Wani zaije turin kura
Wani ko shi ba ya komai,
Ba shi da kowa ba shi da komai.
Mai hakuri zai dafa dutse,
Ba ni ne farkon zance ba.
Sabo da maza ma jari ne.
Ba ni ne farkon zance ba.
Ai arziki daga Allah ne.
Ba yin boka ko malam ne ba.
Asiri ba ya dorewa zancen karya ne ’yan mata
Ga wani labari ’yan mata.
Ku saurara ku fahimta,
Labarin wata mata,
Burin ta mallake angonta.
Lalle ita ta so kanta,
Kuma ta zalunci kanta.
Angonta akwai shi da hali,
dan kasuwa mai hali,
Magidanci ne sosai,
Ai ba karamin yaro ne ba.
Ta kai sunan shi ga boka,
Ka san abinka da mata;
Burinta a sa shi ya so ta,
Har ma yake tsoronta;
Da bin duka umurninta,
Ya ji ma ba ya son kowa,
Ba ya so ya ga kowa sai ita,
Ba ta so ya yi nisa.
Boka ya ce, ta samu bukata.
Koma gidanki ki huta.
Sannu-sannu asirin zai aiki,
Amma ba da garaje ba.
Kwana biyu ba labara.
Asiri ba tasiri.
Ta kara komawa gun boka,
A kara wani wancen bai hau ba.
Boka ya kara kan wancen,
Wanda a kai ya dara wancen,
Koma gidanki ki huta,
Za ki ga aiki da gaggawa.
Alhaji lamari sun rikice,
Ba shi da aiki sai zance;
Kasuwanci sun lalace,
Kullum ga shi gida kwance,
Duk inda tayyi yana bin ta.
Sam ba ya nisantar ta,
Tai ta fada ya kyale ta.
Amma ba ya kyale ta,
Shi ke tsefe gashinta.
Ko da gaban kawayenta,
Zai zo ya zauna cinyarta.
Lamarin ya fara damun ta.
Mijinta ya zama bawanta.
Abu ya ki ci ya ki cinyewa,
Gaba kullum yaka karawa.
Ta je ga boka ya kwancewa,
Ya ce mata bai iya kwancewa,
Ba ya kwancewa.
Duniya wayyo duniya.
Duniya labarin duniya.
Duniya mu guje duniya.
Duniya mu kyale rudin duniya.
Duniya mu kyale kyawon duniya.
Duniya mu kyale zancen duniya.
Jama’a ga Ali Jita na zo,
Zan kada ’yar jitata.
Jama’a ga Ali Jita na zo,
Zan kada ’yar jitata.
Jama’a ga Ali Jita na zo,
Zan kada ’yar jitata.”
Babu shakka in dai har saboda gudunmowar da mutum ya ba al’ummarsa da addininsa ake masa taron karramawa, to kuwa muna jiran mu ji wadannan jami’o’in namu, kamar ABU, danfodiyo, BUK da sauransu sun shirya taron karrama Ali Isah Jita. Domin ba karamar gudunmuwa ya ke ba al’adar Hausawa da addinin Musulunci ba.
A karshe, ina rokon shaihunnan malamanmu, manya da mabiyansu da su zauna su yi tunani a kan wannan bawan Allah da ire-irensa, a kan wakokin da su ke yi, domin a ba su kwarin gwiwa.
Jamilu ya rubuto daga Rabah, jihar Sakkwato, 07031960698, [email protected]