Sharhi da tsakure daga littafin Kundin Hirarrakin Bukar Usman

Sunan Littafi:                        Kundin Hirarrakin Bukar Usman Sunan Marubuci:                 Khalid Imam Kamfanin Wallafa:              Whetstone Arts, Kano Shekarar Wallafa:               2018 Yawan Shafuka:                   366   Tarihin abin da ya faru a jiya, shi ke wanzar da abin da ke faruwa a yau, kamar yadda yake daidaita ko saita abin da ka iya faruwa gobe. […]

Sharhi da tsakure daga littafin Kundin Hirarrakin Bukar Usman

Sunan Littafi:                        Kundin Hirarrakin Bukar Usman

Sunan Marubuci:                 Khalid Imam

Kamfanin Wallafa:              Whetstone Arts, Kano

Shekarar Wallafa:               2018

Yawan Shafuka:                   366

 

Tarihin abin da ya faru a jiya, shi ke wanzar da abin da ke faruwa a yau, kamar yadda yake daidaita ko saita abin da ka iya faruwa gobe. Bisa mizanin wannan magana da ta gabata na dora kunshiyar wannan littafi da nake wa nazari a yau, mai taken ‘Kundin Hirarrakin Bukar Usman’ littafin da ke kunshe da ingantattun hirarraki masu yawa da kafofin watsa labarai daban-daban suka gudanar da fitaccen marubuci, shahararren ma’aikacin gwamnati, masanin harkokin tsaro, Dokta Bukar Usman OON. Hirarrakin da suka kunshi al’amura da dama na rayuwar al’ummar Najeriya ta wata fuskar da kuma rayuwar al’ummar duniya gaba daya a wata fuskar. Hirarrakin da suka kunshi al’amuran ilimi, tsaro, adabi da sauransu. Hirarraki ne da suka wanzu na tsawon shekara 20 da doriya.

An kasa kunshiyar littafin nan zuwa gida uku, baya ga shafukan gabatarwa (daga shafi na 5 zuwa na 26) da suka kunshi Sadaukarwa, Tarihin Marubuci Khalid Imam, Takaitaccen Tarihin Dokta Bukar Usman, Godiya, Mukaddima, Gabatarwa da kuma Ta’aliki.

Kashi na daya na littafin (daga shafi na 27 zuwa na 155), ya kunshi hirarraki guda 15 da wasu jaridu da mujallu na Hausa da na Ingilishi da suka hada da Daily Trust, Aminiya, New Nigerian, The Gurdian, The Sun, ThisDay, The Punch, Daily Independent, Blueprint, Platform, Muryar Arewa, Leadership Hausa, Fim, Nigerian Pilot da kuma Nigerian Tribune suka yi da shi.

Kashi na biyu na littafin (daga shafi na 157 zuwa na 325) ya kunshi hirarraki ne daban-daban da wasu gidajen rediyo da talabijin, na gida Najeriya da na kasashen waje suka gudanar da Dokta Bukar Usman a lokuta daban-daban. Wadannan kuwa sun hada da Gidan Rediyon BBC Hausa, Gidan Rediyon Faransa (RFI), Gidan Rediyon Najeriya (FRCN), Gidan Rediyon Kano, Gidan Rediyo da Talabijin na Borno (BRTB), Gidan rediyo Altenatibe na Jamhuriyyar Nijar, Gidan Rediyon Freedom Kano da kuma Gidan Rediyon RayPower na Kano.

Kashi na uku na littafin (daga shafi na 327 zuwa na 366) ya kunshi abin da ake kira Rataye, wanda ke kunshe da wasu muhimman al’amura da suka faru a rayuwar Dokta Bukar Usman, wadanda suka hada da harkar rubuce-rubuce, karramawa daban-daban da aka yi masa, sunayen wasu jaridu da mujallun da aka yi hira da shi da hotuna daban-daban.

Taskance wadannan muhimman hirarraki da aka yi da Bukar Usman, babban rumbu ne da ke kunshe da dimbin ilimi abin nazari ga al’umma na yanzu da masu zuwa gaba. “Hira wata muhimmiyar hanya ce ta sadarwa, wacce ake amfani da ita wajen isar da muhimman sakonni ga masu sauraro ko masu kallo ko kuma masu karatu ko yin nazari. Hakika, hanyar sadarwa ta hira ko tattaunawa da masana ko shugabannin al’umma ko wasu mashahuran mutane ko kuma kwararru da sauransu, korama ce ta shayar da al’umma ingantaccen ilimi. Babu shakka hira hanya ce ingantacciya da kan taimaka matuka wajen taskance muhimman bayanai domin adana tarihi da kuma saukaka wa manazarta wahalar yin bincike.” Kamar yadda Farfesa Dandatti Abdulkadir ya bayyana a shafi na 17 na littafin nan, a yayin da yake bayyana muhimmanci da tasirin irin wannan littafi, wanda babu shakka shi ne irinsa na farko a littattafan Hausa.

Littafin nan wani maganadisu ne da ke jawo hankalin al’umma su kasance masu himma da dogaro da kai, domin kuwa yana kunshe da bayanai na tarihi, adabi, fadi-tashin neman halal da kuma hikimomin tafiyar da gwamnati a aikace. “Ban da gamsassun bayanai masu ban ta’ajibi na nasarori, littafin ya zana hoton tasiri da alfanun da dogaro ga Allah da kuma dagewa da yin aiki tukuru suke da shi wajen kawar da duk wasu kalubalen rayuwa. Za mu ga yadda dogaron Dokta Bukar Usman ga Allah da mayar da kai wajen yin aiki tukuru ya zame masa gadar cin nasarori a rayuwarsa ta aikin gwamnati sosai, duk da cewar ya fara aiki daga matsayin karamin akawu a 1965, amma haka ya taimaka masa ya zama Babban-Sakatare a Ofishin Shugaban Kasa kafin ya yi ritaya,” inji Farfesa Dandatti Abdulkadir a shafi na 19 na littafin.

Wane irin mutum ne wannan da har ya tattara nasarori haka a rayuwa? Ga abin da Farfesa Salisu Ahmed Yakasai yake cewa game da Dokta Bukar, a shafi na 21, a yayin gabatarwa: “Haka kuma wannan mutum ne mai kana’a da sanin ya kamata. Irin wannan mutum yana da halayyar taimako wajen yin mu’amala da zuciya daya, kuma yana ba da goyon baya tare da karfafa gwiwa cikin rayuwar mutane. A kowane lokaci kofofinsa a bude suke, wato a shirye yake domin sauraron jama’a da kuma ba su shawara tagari. Saboda haka ya kasance aboki ta yadda mutane za su tunkare shi domin ba da shawara dangane da al’amuran rayuwa na yau da kullum. Wannan mutum shi ne Dokta Bukar Usman, mutumin da hirarrakinsa ne tushen samuwar wannan kundi.”

Da yake nuna muhimmanci da tasiri da alfanun da al’umma za su girba a littafin nan, Malam Salisu Na’inna Dambatta, a shafi na 26, a ta’alikinsa yana cewa: “…wannan taska ko kundin hirarraki na Dokta Bukar Usman abin karantarwa ne kuma akwai bayanai masu amfani ga duk wanda ya karanta abubuwan da ya kunsa da idon basira ko niyyar cin moriyar darussan da ya kunsa.”

Kamar yadda aka ambata a baya, littafin ya tattaro tsagwaron ilimi, sannan ya tattaro matsalolin rayuwa daban-daban da suka shafi al’amuran dan Adam, daya daga cikinsu shi ne matsalolin da suka dabaibaye aikin gwamnati. A wasu daga cikin hirarrakin nan, Dokta Bukar a matsayinsa na tsohon ma’aikacin gwamnati da ya kai mukamin Babban Sakatare a fadar Shugaban Kasa, ya zayyano wasu daga cikin matsalolin, sannan ya bayar da shawarwari ko hanyoyin da za a magance su ko rage su.

Misali, akwai inda ya tabo yadda shigar sojoji harkokin mulki a kasar nan ya haifar da nakasu ga aikin gwamnati, wanda hakan ya haifar da wata matsala mai girma, wacce har zuwa yanzu da aka shigo harkar dimokuradiyya aka kasa magance ta. Ga abin da yake cewa a shafi na 33 na littafin:

“Amma tun lokacin da Janar Murtala da kuma shigo da tsarin jagoranci irin na sojoji, aikin gwamnati ya shiga cikin garari ta bangarori da yawa, ko yaya ka dan yi ba daidai ba, za ka dandana kudarka. Ba ka ma da kimar da za a bi ka’idojin aiki wajen hukunta ka. Saboda haka, za mu iya cewa akwai cakudedeniya na dabi’un sojoji da kuma ka’idojin aiki wajen tafiyar da aikin gwamnati a yau. Saboda a tsarin soja akwai mukaman da ko an ciyar da kai gaba ko ba a ciyar ba, ko ma kwata-kwata ba a amfani da kai, dole kawai ka tafi. Idan suka nada wani a samanka, nan ma dole kawai ka tafi, saboda tsabar biyayya.”

Shin mene ne sirrin da ke kawo wa mutum daukaka kuma ya samu nasara a rayuwa? Karatu, nazari tukuru na tarihin rayuwar fitattun mutane. Wannan ita ce hanyar da Dokta Bukar ya bi ya samu nasarar rayuwa har ya kai kololuwa a fagen aikin gwamnati kuma ya kasance mai amfani ga kansa da al’ummarsa. Mu dubi yadda ya amsa wata tambaya a shafi na 45 na littafin nan, da aka tambaye shi ko yana karatu kuwa?

“Sosai kuwa. Nakan yi karatu sosai. A matsayina na ma’aikacin gwamnati, wajibi ne in yi karatu domin in kara samun kwarewa a kan wacce nake da ita, domin in sake shirya kaina, domin zuwa tarurruka. Bayan wannan, a watanni biyu da suka shige, na gane cewa akan samu muhimman abubuwa wajen karanta littattafan tarihi da na tarihin rayuwar mutum. Na samu na tarihin Iya Kwamdanda Dan Sulaiman da na Mai shari’a Chukwudifu Oputa. Wadannan mutane sun kaddamar da littattafan tarihin rayuwarsu, wadanda za su dauki mutum lokaci mai tsawo kafin ya kammala karatunsu ciki da bai.”

Me ya sa ake samun matsalar tsaro a wasu lokuta a kasa, musamman lokacin canjin gwamnati? A wata hira da aka yi da shi, Dokta Bukar ya amsa makamanciyar wannan tambayar, a shafi na 51 na littafin, inda yake cewa: “Na sha bayyanawa a hirarrakin da na yi a baya cewa, lokacin canje-canjen, lokaci ne na samun rikice-rikice saboda rashin tabbas na abin da ka iya zuwa ya dawo wajen wanzar da canje-canjen. Haka kuma saboda fargabar da ake da ita a irin wadannan bukatu ko nade-nade, lokacin ba ya da bambanci da irin abin da wani yake hasashe. Kana da hanyar inganta abubuwa wadda ke dauke da sababbin hanyoyin aiwatar da wasu abubuwa wadanda babu su a baya. Ka ga ke nan akwai yiwuwar a fuskanci tayar da kura. A matsayinmu na ma’aikatan gwamnati, aikinmu a koyaushe shi ne saita gwamnati kan yadda za ta gabatar da manufofi da tsare-tsaren da ake da su ga al’umma cikin hanyar da za a tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasa.”

Shin me zai kawo daidaito da maslaha a siyasar kasarmu kuma wace shawara ta cancanci ’yan siyasa? A matsayinsa na masani a sha’anin mulki da tsaro, Dokta Bukar Usman ya ba ’yan siyasa shawara a wata tattaunawa da aka yi da shi. Misali, duba abin da ya ce a shafi na 53 na littafin nan:

“Ka san idan ka shiga takara ba ka so ka fadi. Babu wanda yake so ya shiga ya fadi. Hakan ya sa mutane suke yin duk mai yiwuwa don ganin sun kai bantensu. A irin wannan yanayi, za ka yi tsammanin ya zama abin gasa mai tsauri, amma ga ire-irenmu wadanda muke da ilimin shugabanci, musamman a harkokin tsaro, wadanda har yanzu suke cikin gwamnati, koyaushe gaba muke kallo wa irin ayyukan da al’ummar kasa suka aikata bisa tsarin doka. Ba ma son mu ga mutane suna yi wa dokoki karan-tsaye domin cimma burace-buracensu. Fatana shi ne al’umma su rika kiyaye dokokin da aka shimfida a kowane mataki na gwamnati, ta yadda wanda ya samu nasara zai yi shugabanci cikin kwanciyar hankali.”

Za mu ci gaba