Sharhi da tsakure daga littafin Kundin Hirarrakin Bukar Usman (3)

Sunan Littafi:                        Kundin Hirarrakin Bukar Usman Sunan Marubuci:                 Khalid Imam Kamfanin Wallafa:              Whetstone Arts, Kano Shekarar Wallafa:               2018 Yawan Shafuka:                   366   Kamar yadda aka yi tsokaci a can baya, cewa littafin nan kundin tarihi ne, kundin ilimi ne da ke kunshe da bayanan matsalolin al’umma da kuma shawarwarin hanyoyin […]

Sharhi da tsakure daga littafin Kundin Hirarrakin Bukar Usman (3)

Sunan Littafi:                        Kundin Hirarrakin Bukar Usman

Sunan Marubuci:                 Khalid Imam

Kamfanin Wallafa:              Whetstone Arts, Kano

Shekarar Wallafa:               2018

Yawan Shafuka:                   366

 

Kamar yadda aka yi tsokaci a can baya, cewa littafin nan kundin tarihi ne, kundin ilimi ne da ke kunshe da bayanan matsalolin al’umma da kuma shawarwarin hanyoyin warware su, a 1996, dan jarida a 1996 ya tambayi Dokta Bukar Usman wani al’amari da ya shafi tsaro, inda ya nemi da ya yi karin bayani, inda shi kuma a shafi na 160 a littafin nan ya bayyana cewa:

“Gaba dayan kushen kan hukumomin tsaro yake komawa. Amma su masu ruwa da tsaki a harkar tsaro da sauran jami’an tsaron kullum za ka ji suna neman hadin kan jama’a. Saboda idan ka duba za ka ga jami’an tsaron ba su da yawan da ake bukata. Ba zai yiwu su kasance a ko’ina a lokaci guda ba. Don haka, idan aka yi la’akari da karancinsu da karancin kayan aiki da karancin ababen hawa da kayayyakin sadarwa za mu tabbatar da cewa hakika babu yadda ma’aikacin tsaro zai gudanar da aikinsa cikin nasara ba tare da hadin kan al’umma ba.

“Haka kuma wasu daga cikinmu sun kalli yanayin da wadansu kasashe suke ciki na rigingimu, musamman lokutan yakin duniya na daya da na biyu. Ba muna cewa Najeriya za ta fuskanci wata mummunar matsala makamanciyar ta yakin duniya ba. Amma kuma mu ma mun taba tsintar kanmu a yakin basasa. Kuma mun samu darussa masu yawa daga yakin lokacin da yin taka-tsan-tsan ga al’umarmu yake da matukar karfi ta yadda har muka yi tunanin hakan zai dore.

“Kamar yadda abin yake a sauran kasashe, akan samu duk lokacin da wani abu yake faruwa nan da nan mutane suke sanar da hukumomi ko jami’an tsaro domin daukar matakin da ya dace. Na kasa gane me ya sa wasu mutanen suke tsorata idan sun kai wa hukumomin tsaro rahoton wani abu da ke faruwa cewa wani zai ci amanarsu ta hanya fallasa su, su ce wane ne ya sanar da mu. Hakan, a cewarsu, zai iya sa wa a yi musu wani lahani.”

Haka ma a shafi na 170, an tambaye shi cewa a kwarewarsa kan al’amuran tsaro, me ya hango a matsayin kalubale ga tsaro a Nahiyar Afirka da ma duniya baki daya a sabon karni mai zuwa. Amsar da ya ba da ta gaskata hasashensa, inda al’amarin ya wanzu a zahiri. Ga abin da ya ce:

“Shin mutane suna jin cewa wadanda suke rike da madafun iko watakila ba sa gamsar da bukatunsu kamar walwalarsu da sauran tsare-tsaren da suke so? Duk lokacin da aka ce ana kula da walwalar al’umma, ma’ana mutane sun samu nutsuwa, ba a tauye musu wata dama ba kamar yadda Dimokuradiyyar wasu kasashen take, sannan ne za a ce ana yin siyasar jin dadi. Kuma a wannan lokaci ne mutane za su rungume ta hannu bibiyu. Amma ina jin a karni mai zuwa, mutane za su ci gaba da zama barazana ga tsaro musamman idan akwai matsanancin talauci. Saboda su wadanda ba su gamsu ba akwai yiwuwar su yi yunkurin neman canji da zummar su ma su samu tsarin da zai faranta musu ko kuma wanda suke tunanin zai samar musu da abubuwa da aka hana su samu. Kuma wannan matsalar ba magana ce ta kasa ko Afirka ko duniya ba, abu ne da ya shafi ko’ina. Saboda haka, maganar talauci ko hana damammaki, duk girman yadda za ka kwatanta abin, matukar an rage kaifinsa, babu shakka zaman lafiya zai mamaye mafi yawan bangarorin nahiyar Afirka da duniya baki daya.

“Amma idan ka yi tsai ka kalli yadda al’amura suke tafiya watakila ka ce ai yanzu babu barazanar. Wannan haka yake. Amma ina so ka san cewa rigingimun canja salo suka yi. Har yanzu wasu kasashe masu fada a ji suna da burin ci gaba da samun tasiri a sassa daban-daban na duniya. A irin wannan yanayin, za ka ga har yanzu ana samun rigingimu.”

Ko yaya matsayin dagangantaka take tsakanin manyan kasashen duniya da kanana da kuma kasashe masu tasowa?

A 1997, Dokta Bukar ya yi karin bayani a shafi na 178, inda ya amsa wata tambaya mai dangane da wannan batun, inda ya ce:

“Na bayyana cewa kasashen da ake rade-radin sun sanya mana takunkumi saboda mun gaza wajen ciyar da kasarmu gaba, ya kamata su koma baya su duba tarihi. Idan sun yi haka za su fahimci abu daya, cewa da zarar wadannan kasashen sun cin ma muradinsu a kasashen irin namu sai kuma su turo sojoji su yi juyin mulki. Haka suke yi. Don haka, babu yadda za a yi yanzu su zo su ce: “Muna yin haka ne saboda muna son ku yi abu kaza.”

“Kamar yadda na fada a baya ne, manyan kasashen duniya masu fada a ji su ne a koyaushe suke saita manufar da duniya za ta tafi a kai; manyan manufofinsu kuwa a wannan lokaci su ne ’yancin dan Adam da Dimokuradiyya. Wadannan manufofi suke son ganin mun runguma; ba wai domin suna jin za su taimake mu samun ingantacciyar Dimokuradiyya ba, sai domin cin ma bukatun kansu. Hakika wannan shi ne abin da suka saka a gaba.”

Ana samun yawaitar kungiyoyin kare hakkin dan Adam a Najeriya, shi ko yaya al’amarinsu yake a zahiri? A shafi na 200 na littafin nan, Dokta Bukar ya amsa wata tambaya a 1998 dangane da ayyukansu, inda yake cewa:

“Abin lura a nan shi ne, idan kana maganar duk wadannan kungiyoyin na kare hakkin dan Adam ba za ka taba jin wadanda suke magana kan wasu bangarori ba musamman tattalin ariziki da zamantakewar jama’a. Wadanda aka fi mayar da hankali a gare su da tallata su, su ne na bangaren siyasa. Watau wadanda suke cewa za su kare Dimokuradiyya da hakkokin dan Adam. Wadannan su ne wadanda za ka rika jin amonsu a kowacce rana. Amma a gaskiya akwai wadanda suke yin aiki a boye a fanni daban-daban kuma da kyakkyawar manufa. A irin wannan yanayin ne za a yi maganar me ya sa kasashen yamma suke da sha’awa ga wasu daga cikin irin wadannan kungiyoyin?

“Na yi kokarin bayyana cewa tun lokacin Yakin Sunkuru akwai wata fahimta guda daya da ta mamaye duniya, ita ce Jari-Hujja (Capitalism) da abin da ake kira Dimokuradiyya wacce ta samu nasarar danne akidar Kwaminisanci da ta daidaito. Saboda haka, kasashe masu fada a ji a yau sun saita ajandarsu yadda ya kamata a kan hakkin dan Adam da Dimokuradiyya, sannan suke son kowa ya amince da su, domin kusan haka al’adarsu take, kuma suke so ta karfin tsiya sai sun sa kowa ya rungume ta. Idan ba ka yin abin da suke da muradi ba, shi ke nan sai su shafa maka bakin fenti, su ware ka, su kuma tsaurara maka abubuwa. Wannan shi ne tushen tsare-tsaren da wadansu kasashen suka samar a halin yanzu.”

Kowane marubuci yana da buri, shin ko mene burin Dokta Bukar a matsayinsa na marubuci? A shafi na 215 zuwa na 216, ya amsa wannan tambayar a 2009 a Gidan Rediyon Kano, yana cewa:

“Sakona shi ne marubuci ya fi son idan ya yi rubutu mutane su saya su karanta sannan ya amfane su. Idan ya rubuta ba a saya ba, ya zama ba shi da amfani ke nan. Ina son mutane su rika sayan littattafai suna karantawa. Na tabbatar akwai abubuwan amfani masu tarin yawa a ciki. Wannan shi ne fatana.”

Sai kuma a shafi na 221, ya ci gaba da amsa wannan tambaya: “Burina a harkar rubutu shi ne, na daya ina so na wasa kwakwalwata. Kamar yadda na fadi ni dan fansho ne. Na yi aikin gwamnati fiye da shekara talatin. Idan na zauna ba na komai kwakwalwata za ta dakushe. Don haka na shiga rubutu ne domin na wasa kwakwalwata. Na biyu, a ra’ayina, duk inda mutum ya yi aiki har fiye da shekara talatin ya kamata ya rubuta wani abu game da aikin da ya yi, domin ana samun matsala kuma ana samun abubuwan kirki a ciki. Yau shekaruna sittin da bakwai a duniya. Tsawon wadannan shekaru na hadu da abubuwa da yawa a fannin aikina ko rayuwa. Wannan ne ya sanya na rubuta tarihin rayuwata. Ina fata mutanen da suka karanta za su amfana da abubuwan kirkin da suka gani a ciki, sannan su kauce wa halaye marasa kyau da suka ci karo da su a cikin littafin. Ba na fatan sake shiga matsaloli irin wadanda na shiga a baya.”

Tarihin mutum ko garinsu, abu ne mai matukar muhimmanci ga al’umma, domin za su dauki darussa da yawa domin saita rayuwar gaba. Dokta Bukar ya bayyana dalilin da ya sanya ya rubuta wani mashahurin littafin tarihin mahaifarsa ta Biyu, mai suna ‘Tarihin Biu.’ Dan jarida ya tambaye shi dalilin da ya sanya ya rubuta wannan littafi mai kunshe da shafuka sama da 600, inda ya bayar da amsa a shafi na 302, kamar haka:

“Haka kuma, na yi la’akari da cewa wanda ya taba rubuta tarihin Biu, “The Biu Book” wani Baturen mulkin mallaka (D.O. na Biu na karshe) ne mai suna J.G. Dabies, da ya rubuta a shekarar 1956. Haka kuma na lura cewa ba a ma iya samun littafin a halin yanzu idan an tashi nemansa, sai mutum ya yi bincike sosai. Ko mu da muka tashi nemansa sai da muka je laburaren Maiduguri, sannan muka samu. Daga baya kuma wadansu daidaikun mutane suka samu. Wadannan dalilai sai suka sanya na ga akwai bukatar rubuta tarihin kasar Biu.

“Wani abin lura shi ne, Turawa sun bar kasar nan a shekarar 1960. Daga wancan lokacin zuwa yau an samu tarihe-tarihe da canje-canje masu yawa. Abubuwan da suka rubuta bai kunshi na shekarar 1960, lokacin da muka samu ’yancin kai zuwa yau ba. Don haka muka yi kokarin cike wannan gibi. Haka kuma mun yi wa abubuwan da suka rubuta kallon tsanaki, domin wanda ya san tarihin abin da za a rubuta ya fi sanin abubuwan da ya kamata a rubuta.”

Game da muhimmancin tarihi kuwa, ya bayyana cewa: “Ai duk kasar da ba ta da tarihin kanta ba za ta yi alfahari da kanta ba. Tarihi muhimmin abu ne a kowane bangare na rayuwa. A kowane addini ma sai an jaddada tarihi balle a al’ada da ilimin shi kansa. Misali, a lokacin da muke makarantar sakandare, tarihin “Commonwealth” ake yi mana. Wannan ya sanya muka san tarihin Indiya, muka san tarihin Kanada, muka san tarihin Ingilan kanta da kuma tarihin sauran kasashen da ke karkashin mulkinta. To kuma yau ka zo ka ce wai a cire koya wa yara tarihinsu na gida kamar tarihin Kano. Wannan ba daidai ba ne. Ya kamata mutum ya san tarihin jiharsa, ya san tarihin Nijeriya, ya san tarihin nahiyar da yake.”

Littafin nan ya rubutu kuma ya zo a kan kari, sai dai kuma an samu ‘’yan kura-kurai wajen rubuta wasu kalmomi, wanda haka ba zai rasa nasaba da matsalar na’urar rubutu ba. Misali a shafi na 17 an rubuta kalmar “Saukakawa” maimakon “saukaka wa.” A shafi na 19, an rubuta “Dage wa” maimakon “dagewa.” A shafi na 22, an rubuta “Karawa maimakon “kara wa,” an rubuta “Bukatarsa maimakon “bukatarsa,” an rubuta “Dabam-dabam” maimakon “daban-daban.” A shafi na 25, an rubuta “Gareshi maimakon “gare shi,” an rubuta “Sahalewa” maimakon “sahale wa,” an rubuta “Kyautatawa” maimakon “kyautata wa,” an rubuta “ya kan” maimakon “yakan.”

A shafi na 42 da kuma sauran sassa na littafin, an rika nasabta kalmar “hira” da lamirin namiji, maimakon mace. Misali, an ce: “wannan hira ta musamman an yi shi” maimakon “an yi ta.” Haka kuma an kira jam’in “labari” da “labarurruka” maimakon “labarai.”

Haka kuma a shafi na 51, an yi kuskure wajen fassara “White Paper” da “Farar Takarda.” Abin da ya kamata a fassara shi ne: “Matsayar gwamnati kan rahoton kwamitin bincike.”

A shafi na 170 da sauran sassan littafin, an rika rubuta “Afurka” maimakon “Afirka.” An kuma rubuta “saliyo” maimakon “salo.”

A shafi na 200 na littafin kuma, an fassara “Cold War” da “Yakin Sunkuru,” maimakon “Yakin Cacar Baki.”

Wannan littafi, kamar yadda aka jaddada muhimmancinsa tun da farko, ya kamata duk wani mai sha’awar ilimin al’amuran yau da kullum da suka danganci tarihi, zamantakewa, ya mallake shi. Ya kuma kamata a samar da littafin a makarantu manya da kananan da cibiyoyin ilimi da dakunan karatu na ko’ina, domin kuwa tasirinsa mai girma ne.

 

Mun kammala