Sharhin Littafin Gwagwarmayata Da Cutar Sikila
Marubuciya: Samira Haruna Sanusi Shekarar Wallafa: 2014 Yawan Shafuka: 101 Sunan wannan littafin shi ne wanda ya fara jan hankalina, domin ni ma na dandana bakin ciki da zafin wannan cuta. dana Muhammad na farko, abin da ya kashe shi ke nan. Lokacin ni da mai dakina ba mu san cutar ba, ba mu […]
Marubuciya: Samira Haruna Sanusi
Shekarar Wallafa: 2014
Yawan Shafuka: 101
Sunan wannan littafin shi ne wanda ya fara jan hankalina, domin ni ma na dandana bakin ciki da zafin wannan cuta. dana Muhammad na farko, abin da ya kashe shi ke nan. Lokacin ni da mai dakina ba mu san cutar ba, ba mu san mene ne sanadin rasa ransa ba; mun dauka masassara ce mai zafi.
Ya dau lokaci ba ya lafiya sosai. Wata rana ina a kofar gida aka kira ni, aka ce Muhammad ba ya numfashi. Na zo na dauke shi na girgiza, na tabbatar ba ya numfashi. Matata ta ce ya rasu, na kafe da ra’ayin cewa doguwar su ma ce. Na bar shi kwance, na ruga wani asibiti mai zaman kansa na kira wani ma’aikacinsu mai suna Hamisu Likita. Shi ne ya tabbatar mani cewa ba doguwar suma ba ce, ya rasu. Ya rasu yana dan wata goma a duniya, lokacin akwai samartaka, domin duka shekarata 23, matata ta dara ni shekaru kuma ta fi ni wayewa.
dana na biyu, Muhammad Sani shi ma da wannan cuta aka haife shi, a kansa muka tabbatar da cewa ’ya’yanmu suna iya daukar Sikila. Bayan an yi gwaji, aka ce ga matsalar. Mun rika daukar matakai kala-kala na kariya, wanda ya rage masa yawan tashin cutar. Alhamdu lillah, yanzu ya girma har da kansa yake daukar matakan kula da kansa amma kafin nan an sha wahala da shi.
Littafin Gwagwarmayata Da Cutar Sikila, littafi ne mai motsa zuciya da ban tausayi da kuma kara wa mai karatu karsashi da karfin gwiwar cewa, a rayuwa ba a mika wuya, a sallama wa matsala; ana gwagwarmaya da ita ne har zuwa samun mafita.
Salon rubutun zai rike mai karatu har zuwa kammalawa idan ya fara. Saukin kalmomin Turanci da aka yi amfani da su da zubin yadda ake misalta duk abin da aka kawo zai sa mai karatu ba ya bukatar karin wani haske idan yana karantawa. Rubutu ne wanda ya fassara kansa da kansa.
Darussan labaran suna da yawa, wasu daga cikinsu shi ne, mahaifiyar marubuciyar ta rasu a wajen aikin Hajji a kasa mai tsarki, Makka. Ta rasu da fatan cewa ’ya’yanta guda biyu, wadanda suke da cutar Sikila za su rayu cikin farin ciki da lafiya ingantacciya. Yaran kuwa su ne Samira da Zainab, danta kuma namiji ya rayu a matsayin mutumin kirki, abin misali ga kowa; mai suna Mustafah.
Mahaifin Samira, marubuciyar littafin ya sha alwashin yin duk abin da za iya daidai karfinsa ya ga cewa wadannan yaran guda biyu masu Sikila sun samu kulawa ta magani, domin su rayu a cikin kwanciyar hankali. Wacce ta rene su, watau matar mahaifinsu ta dauke su kamar ’ya’yanta, ta rika wahala da su kamar yadda mahaifiyarsu za ta yi. Kamar yadda marubuciyar ta rubuta: “Na samu kulawar uwa wadda ba ni da kalmar da zan iya misalta jinjinata da godiyata a kanta.”
Lokacin da za a bayar da bargon jini (bone marrow) wanda za a yi mata dashensa a cikin jikinta, kanenta uwa daya uba daya, Mustafa shi ne wanda ya rika bayarwa; wanda a cikin rubutun ta rika jinjina wa sadaukarwarsa da tausaya masa da tsoron kar shi ma wani abu ya same shi.
Wani abin burgewa ga marubuciyar shi ne, yadda tana cikin jinya amma ta yi ta kokarin ganin yaya za ta shiga makaranta domin ta yi karatu, ga jinya ga ciwo ga kuma shiga makaranta? A rubutun ta bayyana cewa ta yi ta kokarin yin karatu a makarantu.Wani lamarin karfin gwiwa shi ne, duk da wannan wahala da Samira ta shiga na shekaru, ba ta taba karaya ba, ba ta kuma taba yanke kauna tsakaninta da Allah ba. Ba ta kuma yarda ta shiga wata mummunar damuwa, kamar yadda ta rubuta a littafin.
Ta rika kokarin samar wa kanta farin ciki da kwanciyar hankali. A shafi na 95 ta rubuta cewa, “kila ba ni da takardar shaidar kammala karatu kamar haka: Digirin farko, kasuwanci da iya shugabanci, Digiri na biyu a kan sanin kasuwancin kasa-da-kasa; ta yiwu da kwarewa a aiki wuri kaza da kaza. Samira kila ba ni da wadancan amma a rayuwata, na cin ma nasarori da yawan gaske; wadanda na koya kuma babu wanda ke iya saninsu sai ni. Ni kuma kadai zan iya koyar da su. Darrussan da na sani, babu mai iya koyonsu sai ni. Rayuwa ita ce makarantata, dauke zafin ciwo, juriya da sallamawa su ne darussan da na yi nasara a jarabawata.”
Littafin ya kunshi labarin wata yarinya ce mai suna Samira Haruna Sanusi, wadda aka haifa a Jos, a 1988 amma asalinsu daga Funtuwa suke, ta Jihar Katsina. Sunan mahaifinta Haruna Sanusi, mahaifiyarta kuma Zainab. Mahaifiyarta ta rasu tun tana karama amma ta samu kulawa mai kyau daga wajen matar mahaifinta.
Samira su uku ne a dakinsu, ita da kannenta biyu, wadanda suke uwa daya uba daya. Ita da kanwarta duk suna da cutar ta Sikila, kanensu ba ya da cutar amma shi ne ya rika bayar da bargonsa ana sa wa ’yan uwansa.
Tana da shekara shidda ta lura cewa ba ta da cikakkiyar lafiya, kamar yadda ta rubuta a shafi na 6 na littafin nata. A 1994 mahaifiyata suka tafi aikin Hajji, a can ta ta rasu. Ta girma a wajen kulawa mai kyau da inganci daga wajen matar da mahaifinta ya aura bayan mahaifiyarsu ta rasu. Tana da shekara 15 ciwonta na Sikila ya fara matsawa da haifar mata da matsaloli, inda aka fara daukar matakin magani daga asibitin cikin kasarmu Najeriya, har zuwa wani asibiti a kasar Saudiyya. Daga can suka ce babu abin da za su iya sai dai a yanke kafafuwanta; abin da mahaifinta ya ki amincewa, ya fara neman wani asibitin a kasashen Turai.
Daga asibiti a Saudiyya suka wuce wani asibiti a kasar Austria da ake kira St. Anna Kinderpital. Nan ma wasu gwaje-gwajen da ayyukan suka ci gaba, har aka kai ga an yi mata dashen bargo, domin raba ta da cutar ta Sikila. A kuma nan asibitin aka yi wa kanwarta dashen na bargo, wadda ita ma take da cutar amma tata ba ta yi munin na Samira ba. Daga Austria ta wuce Landan, domin samun shawara daga wasu likitocin can a kan yadda ko kafarta za ta iya mikewa. Daga Landan ne ta yi wa likitoci saki uku, ta sallama wa rayuwarta, ta komo gida Najeriya ta ci gaba da rayuwarta cikin farin ciki kamar kowa, kamar yadda ta rubuta.
Littafi ne da ya bayar da labarin jinya cikin tsananin zafin ciwo da radadin jinya da kuncin neman magani na shekara da shekaru. Littafi ne da ke ba da labarin yadda majinyaciyar ta yi amfani da yanayin da ta ke ciki ta koyi darussan da ba wata makaranta da ake koyar da su, ta kuma zama babbar malama wadda za a iya mafana da iliminta daga ilmi mai zurfin da ta samu a darussan da ta samu na yanayin da ta samu kanta. Littafi ne mai koya maka karfin gwiwa a duk yanayin da kake ciki, kar ka karaya, kar kuma ka mika wuya.
Littafin yana bukatar a bai wa masana adabi su yi masa karin kwaskwarima da gyara shi sosai da kuma buga shi yadda za a iya shiga da shi wasu manyan gasar adabi da ake da gudanarwa a kasar nan da Afrika. Littafin yana da bukatar a samu wata madab’a a Landan ta buga shi, domin shiga hannun makaranta a Turai da Amurka. Don wasu littattafan ba su kai nata kima ba, sun sami karbuwa.
Littafin yana da bukatar bugun Hausa, domin da yawa duniyar Hausawa sun jahilci ciwon kuma ciwon ya dade yana kashe attajirai a Arewa, ba a san cewa shi ne ba kuma ciwon ya dade yana wahalar da duniyar Hausa- Fulani, ba a san shi ba ne.
Littafin abin karantawa ne ga kowa. Irin wannan adabi ake bukata a dakunan karatunmu da makarantu don karatantawa.
Danjuma Katsina, marubuci ne kuma dan jarida. Ana iya samunsa [email protected] (08035904408)