Sharhin Littafin “Kwamfuta” Na Malam Salisu Hassan (Webmaster) (3)
Dangane da tsarin rubutu kuwa, Malam Salisu ya zuba harshen Ingilishi sosai a cikin littafin. A tunanina, dalilin hakan ba ya rasa alaka da abubuwa biyu: Na farko shi ne asalin wannan ilimi daga harshen Ingilishi ne. Don haka, rubuta littafi kan ilimin kwamfuta a harshen Hausa ba zai taba yiwuwa ba sai da tsofa […]
Dangane da tsarin rubutu kuwa, Malam Salisu ya zuba harshen Ingilishi sosai a cikin littafin. A tunanina, dalilin hakan ba ya rasa alaka da abubuwa biyu: Na farko shi ne asalin wannan ilimi daga harshen Ingilishi ne. Don haka, rubuta littafi kan ilimin kwamfuta a harshen Hausa ba zai taba yiwuwa ba sai da tsofa kalmomin Ingilishi, tunda shi ne asali. Na biyu kuma, saboda da yawa cikin wadanda suke da ilimin kwamfuta cikin Hausawa a yau, za ka samu kashi 90 cikin 100 na kalmomin da suka san bangarorin kwamfuta da su duk cikin harshen Ingilishi ne. Don haka, kusan dukkan babi-babin littafin an rubuta su ne cikin harshen Ingilishi ba da Hausa ba.
Ta bangaren ma’anonin kalmomi kuma, marubucin bai rike wani tsari guda wanda ya tabbata a kai ba. Da farko dai, galibin kalmomin da ya fassara bai ba su suna tilo ko murakkabi ba. Galibi ya kan yi bayanin ma’anar kalmar ce, sannan ya kawo misali don mai karatu ya fahimci ma’anar. Misali, a shafi na 75 inda mawallafin ke bayani kan ma’anar “CPU,” ya yi amfani da kalmomi sama da daya ko biyu tsakanin Hausa da Ingilishi, don fahimtar da mai karatu ma’anar wannan kalma cikin sauki. Ga yadda ya sa abin nan:
CPU ko kuma a kira shi da Processor wani lokaci ma shi ake kira da ƙwaƙwalwar kwamfuta… shi ke kasancewa mai fashin baki da fassara ga duk abin da yake faruwa a cikin kwamfuta. Iyakar abin da za a iya maka misali shi ne mutumin da ya je ƙasar da ba sa jin harshensa kuma shi ba ya jin harshensu dole yana buƙatar tafinta wannan tafinta shi ke jin harshensa kuma yana jin harshensu.
A wasu wuraren kuma yakan yi amfani da kalmar Ingilishi kai -tsaye ba tare da kawo ma’anarta ga mai karatu ba, musamman idan a baya ya ambaci kalmar. A wasu lokuta kuma yakan yi haka tun kafin ya ambaci kalmar a wani wuri da ya gabata. Kyakkyawar misali na shafi na 94 a Babi na 4 (Input Debices), inda yake bayani kan ma’anar kalmomin “Input” da kuma “Debice,” yana cewa:
Input na nufin shigar da data ko program ko umarni ta hanyar da ɗan Adam zai iya umartar kwamfuta da shi. Debice kuma na nufin kayan lantarki…
A baya ya kawo ma’anar “data” a Babi na 1, amma da ya zo Babi na 4 sai ya sake ambatar kalmar cikin harshen Ingilishi, maimakon harshen Hausa kamar yadda wadansu za su zata. A daya bangaren kuma, ya ambaci kalmar “program” a Turance a nan, wanda bai riga ya ambaci kalmar a ko’ina ba kafin wannan wuri. Wannan salo ne da marubucin ya dauka saboda wasu dalilai.
Shawarwari
Bayan nazari da bita kan littafin “Kwamfuta” har sau uku da na yi, daga cikin abubuwan da za su taimaka wajen kara inganta littafin shi ne, rage yawan kalmomin Ingilishi ta hanyar fassara su cikin gajerun jimloli. Wannan zai kara fahimtar da mai karatu cikin sauki. Ta bangaren jimlolin littafin kuma, zai dace a rage tsayinsu. Saboda gajerun jimloli sun fi saurin isar da ma’ana, musamman ga littafin da ke kokarin isar da wani sabon ilimi irin wannan, wanda rubuce-rubuce ba su yadu a fannin ba, cikin harshen Hausa. Haka nan, zai dace idan aka ba da ma’anar kalma a farko cikin wani babi a harshen Hausa, to, idan aka zo ambaton kalmar a wani wuri a ambace ta cikin ma’anar da aka ba ta a harshen Hausa; in ya so sai a sanya asalin kalmar Ingilishin a cikin baka biyu, misali: “Beran kwamfuta” (Mouse). Ko “Allon Shigar da Bayanai” (Keyboard). Hakan zai kara tunatar da mai karatu asalin kalmar da aka ciro kalmar Hausar. Bayan haka, zai dace a yi bitar ma’anar wasu kalmomi. Misali a shafi na 231, mawallafin ya fassara kalmar “Internet” da “Web” da ma’anar “Yanar Gizo,” maimakon “Yanar Sadarwa,” wadda ita ce ta fi isar da ma’ana mai inganci. Haka kalmar “Script” a fannin gina manhajar kwamfuta, an fassara ta da: “Surkullen Yaren kwamfuta”. Wannan ba zai bai wa mai karatu kyakkyawar fahimta kan sakon da kalmar ke isarwa ba. “Script” nau’i ne na yaren gina manhaja ko shafukan Intanet. Sannan kalmar “surkulle” tana ishara ce ga wani abin da ba ya da hakika; kamar rufa-ido ne. Wannan ya saba wa ilimin gina manhajar kwamfuta, wanda hakika ne shi, ba surkulle ba. Ba dukkan mai karatu zai fahimci asalin ma’anar ba. Ina ganin bitar ma’anar kalmar zai dace don isar da ma’ana mai inganci.
Kammalawa
A karshe, wannan littafi ne da duk mai son fahimtar yadda kwamfuta ke aiki da gudanuwa zai fa’idantu sosai da shi. Duk da cewa akwai kalmomin Ingilishi da dama, kamar yadda na sanar a baya, hikimar hakan a fili take. Rubuce-rubuce a harshen Hausa kan fannin kimiyya da fasahar sadarwa, musamman na kwamfuta, ba su yadu sosai ba a kasar Hausa. Daga cikin manyan kalubalen da ke gaban harshen Hausa wajen ci gaba a wannan fanni, akwai rashin daidaituwar ma’anonin kalmomin Ingilishi na wannan fanni. Ma’ana, samun daidaito A tsakanin masana kan ma’anar kalma, misali: “Click”- “Matsa” ko “Danna?” Haka idan ka dauki kalmar: “Storage” – “Ma’adana” take nufi ko “Ma’ajiya?” Ga kalmar; “Memory”-“Kwakwalwa” take nufi ko “Ma’adana?” Da sauran ire-irensu.
Wannan kalubale ne da ya kamata masana harshen Hausa a jami’o’inmu su tunkara, tare da hada kai wajen ganin an tabbatar da abin da zai zama abin dogaro. Lokacin da marubucin wannan littafi ya aiko mini don tofa albarkacin bakina, abu na farko da ya fado zuciyata ke nan. Shi ya sa a karshe da na gama bitar littafin, daga cikin uzurin da na ba shi na rashin tabo ko magana kan ma’anonin da ya bai wa galibin kalmomin Ingilishi da ya kawo a littafin, shi ne rashin daidaitaccen tsari abin dogaro. A yanayi irin wannan kuwa, hanya mafi sauki ita ce samar da daidaitaccen tsari da zai bai wa wadannan kalmomi ma’anonin da aka amince a kansu. Kafin samuwar hakan kuwa, dole ne mu hakura da abin da ya samu. A hankali, wata rana sai labari.