Sharhin littafin ‘Ma’aikacin Banki Don Talaka’
Sunan Littafi: Ma’aikacin Banki Don TalakaMarubuci: Attahiru Kawu BalaKamfanin Wallafa: Author’s House U.S.Shekarar Wallafa: 2010Yawan Shafuka: 363Farashinsa: Ba a fada ba Farfesa Muhammad Yunus, kwararren masani ne a fannin tsimi da tanadi. Ya shahara a duniya wajen fafutikar bayar da kananan basussuka a kasar Bangaladash, musamman a yankunan karkara. Duk da cewa ya fuskanci kalubale […]
Sunan Littafi: Ma’aikacin Banki Don Talaka
Marubuci: Attahiru Kawu Bala
Kamfanin Wallafa: Author’s House U.S.
Shekarar Wallafa: 2010
Yawan Shafuka: 363
Farashinsa: Ba a fada ba
Farfesa Muhammad Yunus, kwararren masani ne a fannin tsimi da tanadi. Ya shahara a duniya wajen fafutikar bayar da kananan basussuka a kasar Bangaladash, musamman a yankunan karkara. Duk da cewa ya fuskanci kalubale daga bankunan gargajiya da jami’an gwamnati, nasarar da ya samu ta dauki hankalin masana da gwamnatoci da al’ummomin duniya. Watakila wannan dalilin ne ya sanya Lauya Attahiru Kawu Bala ya fassara mana tarihin rayuwarsa da aka wallafa a cikin Ingilishi, mai taken ‘Banker to the Poor.’
Ko me ya ja hankalin kwararren Lauya, Attahiru Kawu Bala kan al’amuran Farfesa Muhammad Yunus?
“A shekara ta 200 ne na karanta wata doguwar makala a jaridar Weekly Trust game da Farfesa Muhammad Yunus da irin kokarin da yake yi a wani banki da ya ba ni sha’awa da al’ajabi. Makalar ta yi bayani ne cewa wani mutum da ake kira Farfesa Yunus ya kafa Bankin Grameen a Bangladesh – Bankin da dogon rubutun ya ce yana “bayar da bashi ba tare da kudin ruwa ba balle bukatar masu karbar rance su gabatar da kadara kafin a ba su bashi.” Ganin kuma irin yadda ya samo asali ta bayar da bashin Dalar Amurka 27 ga wata mata, har ya zuwa yadda abin ya ci gaba ya zama bankin da ake maganarsa a yau a sassan duniya wannan ya sake jawo hankalina. Ga shi kuma an nuna Bankin Grameen ya samar da rassan masana’antu da kamfanoni iri-iri karkashinsa.” Inji shi a shafi na db.
Wannan littafi ya tattaro kuruciya da karatu da gwagwarmayar neman ilimi da fafutikar ’yancin kasarsa; sai dai kacokan ya fi bayar da karfi kan yadda aka kafa bankin talakawa na Grameen.
Rayuwar Muhammad Yunus, wanda ya shahara a duniya wajen fafutikar yaki da fatara da talauci a tsakanin makaskanta a cikin al’umma, inda ya yi ta kokarin ganin bankuna sun bai wa talakawa bashi, ko da ba su da dukiyar da za a yi garkuwa da ita, har ya kai ga kafa bankin talakwa na Grameen, shi ne hakikanin abin da Lauya Attahiru Kawu Bala ya rairayo mana.
Marubucin ya fito wa masu karatu irin kaifin basirar da Allah Ya bai wa Farfesa Muhammad Yunus da irin jajircewarsa wajen ganin ya kawo sauyi a hada-hadar banki ta zamani, har ta kai ga ya kafa Bankin Grameen ko bankin talakawa, wanda kacokan ayyukansa sun dukufa ka’in-da-na’in wajen bunkasa sana’o’i da kasuwanci, wadanda ba su da kama-sayar; kai wasu ma bara suke yi a titunan kasar Bangaladesh.
An yi gawajin wannan dabara ta bayar da karamin bashi ga matalauta, kuma ya samu gagarumar nasara a yankin Jobara da Togail, amma duk da haka manyan ma’aikatan gwamnati da shugabannin bankuna na ganin nasarar da aka samu a gwajin, aiki ne da Farfesa Yunus da ma’aikatansa suka yi ba dare ba rana. Don haka suka kalublance shi kan ya fadada gwajinsa a sauran yankunan karkara. Shi kuwa ya tunkari wannan kalubale, har ma jami’ar da yake koyarwa ta Chittagong ta ba shi hutun aiki na shekara biyu (shafi na 159).
A 1983, duk da dimbin kalubalen da ya fuskanta a tsakanin bankuna da jami’an gwamnati, sai ya kafa Bankin Grameen, wanda ya ginu a kan akidar cewa bayar da bashi ga talaka wanda bai mallaki kama-sayar ba, wani hakki ne. Tun daga wancan lokacin zuwa yau, Bankin Grameen ya bayar da basussuka da kimarsu ta kai Dala biliyan biyu da rabi kuma wadannan kudi duk an raba su ne a yankunan karkara, musamman ga kashi 95 cikin 100 duk mata ne.
Babban kalubalen da bankin Grameen ya fuskata shi ne daga malaman addini masu ra’ayin rikau, wadanda suka rika tsorata mata masu karbar bashi a bankin, da cewa idan sun mutu ba za a binne su, ko a yi jana’aiza tamkar yaddda ake yi wa Musulmi a kasr Musulunci ba.
Farfesa Muhammad Yunusa ya bayyana yadda ya lakaba wa bankinsa sunan ‘Grameen,’ kalmar da ke daukar ma’anar karkara ko kayan kauye, a cewarsa. (Shafi na 171).
Tarihin rayuwar Muhammad Yunus, kamar yadda aka ruwaito a Babi na ukku, ya tabbatar da cewa wannan gwarzon al’umma bai tashi a cikin talauci ko wani mawuyacin hali na rayuwa ba. Amma abin tambaya, me ya sa yake da tsananin tausayin talakawa, musamman matan kulle da ke gidajensu na aure a kauyuka? Farfesa Muhammad Yunus ya bayyana yadda yake jin dadin koya wa dalibansa manyan dabaru na tsimi da tanadi da kuma yadda ake bunkasa tattalin arziki, amma daga bisani sai ya gano cewa, “soki burutsu ne kawai.” Domin darussan da yake koyarwa sun saba wa hakikanin halin da talakawa suke ciki. Shi ya sa sai ya yanke wa kansa cewa daga malamin jami’a shi ma ya koma ‘dalibi,’ inda kauyen Jobra ya kasance jami’arsa, sannan mutanen kauyen suka zama malamaina.” Inji shi.
A cewarsa: “Ta hanyar himmatuwa wajen samar wa dalibai fahimta ta sama-sama, jami’o’in da aka sani sun haifar da nisa mai tsananin yawa a tsakanin dalibai da hakikanin rayuwa.” (Shafi na 3). Daga nan Farfesa Yunus ya yi ta ziyartar gidajen talakawa, tare da abokinsa Farfesa Latifee, musamman ma saboda ya san mutanen kauyen. A irin wannan ziyarar da ya saba kai wa gidajen talakawa. Ta haka ya gano cewa akwai iyalai 40 da ke bukatar Dalar Amurka 27, don su fita daga cikin kangin talauci da talalar masu bayar da bashi da ruwa, wadanda ke ba su bashi, su kuma sayi abin da suka sana’anta, ta yadda matar da ta shafe safiya da yininta tana sakar kujerar kwangwala, babu abin da zai rage mata na riba, illa abin da kawai za ta ci abinci.
Masu bayar da bashi da ruwa da malaman addini (mullah), sun yi matukar fafutikar ganin sun rusa Grameen amma saboda jajircewar Farfesa Yunusa da daukacin ma’aikatansa masu kishi, shirinsa ya samu nasarar da a yau ana koyi da shi a daukacin fadin duniya.
Ba zai yiwu a zuba wa mai karatu dimbin dabarun da Farfesa Muhammad Yunusa ya yi amfani da su wajen yaye wa talakawan kasarsa fatara da talauci, har shirinsa ya samu karbuwa a duniya ba amma tabbas kowa zai so ya ji, idan an bayar da bashi ga mace ko wanda ba shi da kama-sayar, yaya yake biyan bashin? Ko in an samu asara, wane kamfanin inshora ne ke bayar da kariya ga dukiyar da ake juyawa a bankin Grameen?
To, ana bai wa mata wadanda ba su iya rubutu da karatu ba, inda za su kafa kungiya ta mutum biyar, daga nan sai a karanta musu dokokin Grameen, don amfanin kansu. Kuma idan aka bayar da bashi ga wasu ’yan kungiyar Grameen ko da wani ya gudu, ’yan kungiyar ne za su kamo shi ko kuma su biya. Domin Farfesa Yunus ya ce ba sa amfani da dan sanda ko hukumar shari’a wajen kwato kudinsu da aka ranta aka ki biya.
Wannan tsari na bankin talakawa, ya samu karbuwa da amincewar cibiyoyin hada-hadar kudi na duniya, wadanda suka hada da Bankin Duniya da Asusun Lamuni don bunkasa aikin gona a duniya. Wannan ba karamar nasara ce ga al’umma, musamman idan Malam Bahaushe ya fahimci tsarin Grameen, ya aiwatar da shi to za a rage mabarata a tituna da masu zaman kashe wando da wadanda sana’o’in da suke yi ba sa biya musu bukatun rayuwa.
Hakika kwararren Lauya Attahiru Kawu Bala ya yi matukar kokari wajen rairayo wa Malam Bahaushe dabarun da Farfesa Yunus ya yi amfani da su don taimaka wa talakawan Bangladesh, da ma na duniya baki daya amma duk da haka ya yi amfani da wasu kalmomi da suka kawo wa sakon da yake kokarin isarwa tarnaki. Wadannan kalmomi sun hada da ‘Lifin’ da ya ce an bai wa Muhammad Yunus daga jami’a na shekara biyu (shafi na 159). Idan na fahimta, yana nufin jami’a ta sallama Farfesa Yunus har na tsawon shekara biyu, don aikin gwajin Grameen. Ya kuma yi amfani da kalmar ‘Jifa,’ inda yake maganar yadda kungiyar mata ta mutum biyar za ta fara biyan bashinta, maimakon kalmar “Zubi.” Sai kuma wasu kalmomi da ya yi wa jama’u, alhalin ba a saba amfani da su a rubutun makala ko littafi ba; kalmomin sun hada da ‘yarjeniyoyi’ da ‘ambaliyoyi’ da ‘jarabawowi.’
A ganina, kamata yayi sunan wannan littafi ya zama ‘Mai Bankin Talakawa’ ko ‘Bankin Talakawa’ kawai. Domin Farfesa Yunusa ba ma’aikacin banki ba ne kuma da kansa ya bayyana cewa ‘Grameeen,’ ba banki ba ne ‘a zahiri.’ (shafi na 323).
Bisa la’akari da kyawun wannan aiki da Attahiru Kawu Bala ya yi, game da rayuwar Farfesa Muhamamd Yunus da kafuwar bankin Grameen, inda kyautata zaton da zai yi gyara game ire-iren kalmomin da na ambata, tabbas sai ya fi isar da sako ga Hausawa ko masu amfani harshen Hausa, har irin wadannan dabaru su yi tasiri wajen rage karsashin talauci da ya addabi al’umma, musamman a daidai wannan lokaci da yawan kudin da ake juyawa a harkokin kasuwanci a Najeriya (GDP), ya fi na kowace kasa a fadin Afirka, amma abin takaicin, wasu ’yan tsirari ne ke rike da tarin dukiya, alhali gama-garin al’umma na fama da matsanancin talauci. Wannan ya yi daidai da abin da Farfesa Yunus ya gano cewa, darussan da ya dade yana koyarwa, sun sha bamban da abin da ke faruwa a hakikanin rayuwa.
Ina mai karkare bayanaina game littafin ‘Ma’aikacin Banki Don Talaka’ da cewa lallai al’umma su yi kokarin mallakar wannan littafi, don fahimtar baiwar da Allah Ya yi wa Farfesa Muhammad Yunus. Kuma lallai ya kamata a ce Lauya Attahiru Kawu Bala ya yi kira ga Shugabannin al’umma da alkalai da ma’aikatan bankuna, kan lallai su karanta wannan littafi da nufin kawo sauyi mai ma’ana a cikin al’umma.