Sharhin littafin tarihin Babban Alkalin Jihar Katsina

Sunan Littafi: Brief Biography of Shiek Al-Hafiz M Abubakar Marubucin littafin:Hamisu Garba Madabba’a: UMYU Press Katsina Shekarar bugu: 2019 Yawan shafukan: 58 Mai sharhi: Danjuma Katsina   Wani littafi da aka rubuta na tarihin Alkalin Alkalai na jihar Katsina, ya nuna yadda ilimi kan maida  bawa ya zama ɗa ya kuma mai da Almajiri zama […]

Sharhin littafin tarihin Babban Alkalin Jihar Katsina

Sunan Littafi: Brief Biography of Shiek Al-Hafiz M Abubakar

Marubucin littafin:Hamisu Garba

Madabba’a: UMYU Press Katsina

Shekarar bugu: 2019

Yawan shafukan: 58

Mai sharhi: Danjuma Katsina

 

Wani littafi da aka rubuta na tarihin Alkalin Alkalai na jihar Katsina, ya nuna yadda ilimi kan maida  bawa ya zama ɗa ya kuma mai da Almajiri zama duk abinda ya sanya a gaba na rayuwa.

Littafin tarihin mai suna takaitaccen tarihin shiek Al-Hafiz M Abubakar  babban alkalin kotunan Shari’ar musulunci na jihar Katsina wanda wani malami a jami’ar Umaru Musa Yar’adua ya rubuta mai suna Hamisu Garba.

Kuma kamfanin dab’i na jami’ar Umaru Musa Yar’adua ya buga littafin, ya fito a shekarar 2019.

Littafin ne mai kunshe da tarihi mai darasin gaske na rayuwa wanda ya zo daidai lokacin da ake bukatar irin wadannan tarihin abin misali da kwaikwayo.

Littafin na da babi guda biyar, bayan shimfida, gabatarwa da kuma godiya. Babin farko ya kawo tarihin rayuwar babban alkalin. Babi na biyu kuwa  yadda ya shiga aikin alkalanci da inda ya yi aiki har zuwa zamansa babban alkalin jihar Katsina. A babi na hudu an kawo wasu hukunce-hukuncen da ya  taba yankewa wanda marubucin ya kawo guda hudu kacal masu sarkakiya da alkalin ya yanke kuma aka samu Maslaha. Babi na biyar ya yi bayani a kan iyalansa, da kyaututtukan da aka taba bashi na karramawa.

A rayuwar Al-Hafiz abin koyi, an haifeshi a unguwar layin kuka garin Bakori a 1955 ya fara karatun allo a wajen mahaifinshi inda a littafin aka kawo tsarin karatun allo tun daga babbaku har zuwa tattashiya. Kakansa babban malami ne, ya dauke shi zuwa Hadeja wani gari mai suna kauga daga can suka hau jirgin kasa zuwa kwaduke a nan ne aka hada shi da gardawa suka fara kwami wanda har takai cikin shekara daya ya hardace izifi goma na Alkur ani mai tsarki. A nan  Al-Hafiz ya yi rayuwar sa ta almajiranci ta karatun Kura’ani mai tsarki, daga nan ya wuce Zaria, inda ya zauna wajen Malam Garba a 1970 suka wuce Kano shi da malamin shi inda nan ma ya ci gaba da neman ilmi mutuwar kakansa a 1972 ya sanya ya bar Kano ya nufi Azare inda ya zauna a wani waje mai suna kwanar yana  a nan ne ya iske makaranta Alkur’ani daga ko’ina a cikin kasar nan  inda suke haduwa suna kara gogewa a kan nakaltar Alkur’ani mai tsarki, a nan ne ya kammala haddarsa har ma ya fara rubutawa.

Daga 1973 zuwa 1975  ya yi yawo zaurukan karatun allo daban-daban a Malam Madori, Jama’are, Nguru, Yobe, da Maiduguri, daga baya ya wuce Gombe a Jeka da fari da Kumbiya-kumbiya/inda ya hadu da manyan Alarammomi suka kara gogewa a kan ilmin Alkur’ani.

1975 ya wuce garin Jo’s inda ya fara karatun littattafai na ilimin Fikhu tunda yanzu ya nakalci sanin karatun alkur’ani sosai. Bayan zuwa  zaurukan malamai yana daukar karatu Al-Hafiz ya shiga makarantar Jama’atul Nasarul Islam  inda malamai daga kasashe daban-daban suka rika  horas dasu bangarorin ilmi daban-daban, daga cikin Malaman nasa har da Sheikh Ismail Idris, Shiek Aliyu Tilde, Shiek Hafiz Abdelhamid da sauransu.

A ajinsu na karatun har da Shiek Sani Yahaya Jingir da Saidu Alhassan, Suleman Gwani da Sauransu. A makarantar Jama’atul Nasarul Islam ta Jos, Khadi Alhafiz ya karantu dai dai gwargwado daga can sai ya dawo Katsina ya shiga makarantar horos da malaman musulunci ta ATC Katsina. Inda ya shiga a 1978 ya kuma fita a 1981a cikin ‘yan ajinsu a ATC akwai  Alhaji Bawa mai Shinkafa, Umar Lawal, Halilu mai Kyaure da sauransu.

Yana kammalawa ya shiga makarantar Fasaha da Kimiya ta jihar Katsina sashen shari’a da aikin lauya inda ya samu diploma a harkar shara’a da alkalanci.

Wanda da ita ne ya amsa kiran da Shiek Abubakar Gumi ya yi na cewa yana da kyau masana shara’a su rika shiga aikin alkalanci/don kar bangaren ya lalace ko ya fada hannun baragurbi inda ya shiga aikin alkalanci.

Al-Hafiz yana alkali ya koma jami’ar Umaru Musa  Yar’adua inda yayi digri ya kuma rika halartar kwasai-kwasai wanda wannan ya kara habaka iliminsa.

Aikin farko da ya fara bayan samun aiki a ma’aikatar shari’a ta jihar Kaduna shi ne  Maga-takarda (rijistara) a Dutsinma karkashin alkali Maikaita Saulawa. Daga nan ya yi ta aiki daban-daban har zamansa Khadi a 2006 da kuma zamansa babban alkalin jihar katsina a 2018.

Zamansa babban alkalin jihar Katsina ya yi amfani da ilminsa na karatun allo da budewar idonsa ta yawon neman ilmi da ya yi  da  karatunsa na zamani da kwasa-kwasan da ya halarta ya kawo ci gaba da yawa  kotun Shari a na Katsina.

Ya kawo horon karawa juna ilmi da ya yi ma duk alkalan jihar, wanda malamai daga duk bangarorin musulmi suka gabatar da takardun ilmi.

Ya kawo cewa duk wanda za a ba alkalanci sai ya cika sharudda sai kuma an yi masa jarabawa  ta rubutu an kuma yi masa gwaji na tambayoyi.

Kuma duk mai son zama alkali a kalla sai ya mallaki diploma ko digirin farko kafin ya nema.

Ya kuma  kawo buga kalandar musulunci wanda hukumar shari’a ta jiha zata rika bugawa duk shekara a kalandar akwai lokuttan sallah da sauran muhimman bayanai da suka shafi addinin musulunci. Da muhimmantar da shekarar musulunci. Wanda ya kira taron manema labarai a ranar farko ta shiga shekarar musulunci.

Ya kara daukar ma’aikata don inganta ayyukan manyan alkalai a kotunan daukaka kara na musulunci a jihar.

A lokacin  an gyara da sake fasalin gine-gine a kotunan daukaka kara na musulunci a jihar. An  kuma zabi sabbin manyan Khadi a lokacin sa.

Al-Hafiz  ya  kawo tsarin da  ma’aikata a kotunan zasu karo ilmi bisa wani tsari da za a tura ka karo ilmi kuma a  dau nauyin duk karatun naka. San nan kuma an tura ma’aikatan jami’o’i wasu har a kasar Nijar makwabciyar Najeriya.

A Babi na hudu na littafin  marubucin ya kawo wasu shari’u guda hudu sarkakiya wanda Al-Hafiz ya yi hukunci a kan su, kuma ya warware matsalar.

Shara’ar farko ita ce ta Maimuna Alhaji Abdu da Umaru Alhaji Shuaibu a kan aure da ya shafi hul’i an ta bugawa har kotun daukaka kara ta musulunci kuma Al-Hafiz ya yanke ta.

Sharia ta biyu a kan yarjejeniya ce ta aiki tsakanin  Muhammad Sama’ila da Nasir Plumber da sauran. Shari’a ce aka yi tayi har kotun daukaka kara ta musulunci, Al-Hafiz shi ne ya yanke ta.

Shari’a ta uku ta maganar gona ce tsakanin Musa Dan Sabo da Lawal Dabo Shari’a ce aka yi ta tafkawa har kotun daukaka kara itama Al-Hafiz ya yanke ta.

Shari’a ta hudu tsakanin saminu Umar da Sa’adiya Sani an yi ta Tafkata har kotun daukaka kara inda Al-Hafiz ya yanke ta duk Shari’un an kawo cikakken rubutun hukuncin yadda aka fara ta da hujjojin da aka dogara kansu aka dau hukuncin da aka yanke.

Babi na biyar ya kawo kungiyoyi da jami’o’in da suka karrama Alhafiz da dalilai da suka sanya suka karrama shi. Al-Hafiz yana da mata hudu da ‘ya’ya da jikoki biyu daga cikin ‘ya’yansa ‘yan jarida ne dake aiki da gidan rediyon jihar Katsina. Duk ‘ya’yansa yana basu tarbiyya ta karatun Muhammadiya da kuma na boko.

Littafin ya fito a lokacin bukatar sa watau yanzu da ake son sanin tarihi da zai zaburar da Matasanmu su san ciwon kansu, su kuma nemawa kansu mafita. Littafin an rubuta shi da turanci amma yana da kyau a yi na Hausar shi.

Akwai gyara da kurakurai a littafin wasu sun kama daga tsara bayanan dake ciki wasu an manta ba fade su yadda suke ba.

Ya kamata ace littafin kamar wannan wani Alkali ne  wanda ke aiki ko ya yi ritaya shi ne ya rubuta gabatarwarsa, kuma ya kamata ace an yi magana da abokan karatun sa da wasu daga alkalan da ya yi aiki dasu su fadi ra’ayinsu a kan sa, da wasu da ya taba yanke wa hukuncin  su fadi ya suka ji.

Da fatan a bugu na biyu a gyara wannan barayin kuma in za ayi na Hausar shi a gyara inda aka samu kura-kurai.

Littafin ya kamata ya shiga makarantu da dakunan karatu.

Danjuma  Marubuci ne kuma Danjarida 08035904408

Gwamnatin Yobe ta tallafa wa magidanta 53,000 da N3.91bn a 2024

Uwargidan Sanata Goje ta tallafa wa mata da matasa a Gombe

An kama bokaye 2 kan zargin yi wa shugaban Zambiya asiri

Kirsimeti: FRSC ta aike jami’ai 1,539 zuwa Kano