Sharhin littafin Tsarin Tarbiyyar Yara A Musulunci

Sunan Littafi: Tsarin Tarbiyyar Yara A Musulunci Marubuci: Usman Muhammad Alkasim (Abu-Muhammad) Kamfanin dab’i: Gobernment Printer, Katsina Shekarar Wallafa: 2010 Yawan Shafuka: 197 Farashi: Ba A Fada Ba.   Masu hikimar magana suna cewa, tarbiyya daga gida take farawa amma kuma tana karewa a waje. Wannan ke kara tabbatar da cewa al’ada, addini da halayyar […]

Sharhin littafin Tsarin Tarbiyyar Yara A Musulunci

Sunan Littafi:Tsarin Tarbiyyar Yara A Musulunci

Marubuci:Usman Muhammad Alkasim (Abu-Muhammad)

Kamfanin dab’i:Gobernment Printer, Katsina

Shekarar Wallafa:2010

Yawan Shafuka:197

Farashi:Ba A Fada Ba.

 

Masu hikimar magana suna cewa, tarbiyya daga gida take farawa amma kuma tana karewa a waje. Wannan ke kara tabbatar da cewa al’ada, addini da halayyar iyaye tun daga farko su ne tushe da shika-shikan tarbiyyar da kan danfaru ga yaro, a lokacin da yake tasowa a gidansu. Haka ma abin yake a nafsi, cewa koyami ga yaro kamar rubutu ne bisa dutse, alhali koyami ga mutum idan ya girma, kamar rubutu ne bisa dutse. Musulunci ya zo da tsarin tarbiyya ga al’umma gaba daya. Shin wane tanadi ya yi wa iyaye dangane da tarbiyyar yaransu? Abin da Malam Usman Muhammad Alkasim (Abu-Muhammad) ya yi nazari ke nan, sannan ya rubuta wannan babban littafi da muke nazarta a yau, mai taken Tsarin Tarbiyyar Yara A Musulunci, domin amfanin al’umma gaba daya.

Tun da farko, bayan shafukan gabatarwa a shafi na ii zuwa na dib, marubucin ya ci gaba da warware kunshiyar littafin kai tsaye, mai dauke da babi-babi shida, sannan ya kitse tare da rufewa da shafukan Kammalawa, Manazarta, Jerin Littattafan Da Suke Da Muhimmanci Wajen Tarbiyyar Yara, Kebabbun Haruffa da kuma Ma’ana Da Fassarar Wasu Kalmomi, a shafi na 182 zuwa na 197.

A babi na daya, wanda ya faro daga shafi na 1 zuwa na 40, marubucin ya kasafta shi zuwa fasulla hudu, inda ya yi bayani dalla-dalla dangane da ma’anar tarbiyya a Musulunci, matsayin tarbiyya, siffofin mai tarbiyya da matakan da zai bi ya samu nasara wajen koya tarbiyya ga yara. Haka kuma marubucin ya kawo bayanai dangane da irin muhimmanci da gudunmowar da makaranta da masallaci ke bayarwa wajen gina tarbiyyar yara.

Babi na biyu kuwa ya fara ne daga shafi na 41 zuwa na 74, wanda ke kunshe da fasulla biyar. Marubucin ya kawo wasu ka’idoji da akan kafa wa yara wajen tarbiyya, domin tabbatar da yin ibadojin da addini ya tanadar ga al’umma. An yi bayani game da ibadoji na zuciya da na jiki da dabi’u mafifita da sauransu. An yi bayanin yadda ake gina mutuntaka dangane da zaman tare da mutane daban-daban, da yadda tarayyar za ta amfani mutum a rayuwarsa. An kawo hanyoyin tarbiyyar yara, yadda za su samu karuwar hazaka da kara himma, yadda ba za su tashi a matsayin dolaye ko ragage ba. An bayyana ladubban da ake bi wajen ilimantar da yara da lura da irin baiwar da Allah Ya yi masu da kuma hikimomin da mai tarbiyya zai bi domin ya habaka irin wadannan baiwa da yaran ke da su.

Sai kuma babi na uku, wanda ya samu zama a shafi na 75 zuwa na 89, wanda ke kunshe da fasulla shida. A nan ne marubucin ya warware muhimman bayanan da suka kunshi hakkokin yara a Musulunci. Mene hukuncin binne da da rai ko kuma zubar da cikinsa, bayan an samu? Wadanne ladubba ne suka wajaba ga iyaye wajen zabe da rada suna da tabbatar da nasaba da yanka hakika ga ’ya’yansu? Yaya ake tabbatar da gado kuma yaya ake ciyarwa da shayarwa da aski da kaciya da ma rainon yara gaba daya? Marubucin duk ya samar da cikakkun bayanai a wannan babi.

Idan muka tsallaka babi na hudu kuwa, wanda ya faro daga shafi na 90 zuwa na 131, mai dauke da fasulla biyu, marubucin ya gabatar da bayanai dangane da irie-iren tarbiyya da matakansu.

A babi na biyar kuwa, wanda ya dauki salo daga shafi na 132 zuwa na 144, mai kunshe da fasulla uku, marubucin ya yi bayani game da yanayin yadda ake koya tarbiyya ta musamman ga yaran da ke da yanayi na musamman. Wadannan kuwa sun hada da yadda ake tarbiyyar marayu da yadda ake tafiyar da tarbiyyar yara marasa lafiya da kuma musamman nakasassu. Yara masu hazaka, su ma ba a barsu baya ba, domin kuwa akwai salo da matakai na musamman da ake dauka wajen ba su tarbiyyarsu.

Babi na shida kuma na karshe, yana kunshe da fasulla uku kuma ya faro ne daga shafi na 145 zuwa 181. A nan marubucin ya bijiro da hikimomi da tasirin koyar da yara tarihin magabata. Akwai sunaye da bayanan muminai mata da aka yi wa bushara da aljanna, mutanen da suke da alaka da Manzon Allah (saw). Haka kuma an kawo bayanan gidajen da Annabi Muhammadu (saw) ya zauna a garuruwan Makka da Madina.

Babu shakka littafin nan babbar taska ce ga al’ummar Musulmi, musamman a wannan lokaci da sanabe-sanaben zamani ke yi wa al’umma barazana wajen gurbata tarbiyyar yara. Ta hanyar wannan littafi, iyaye da malaman makaranta za su samu hikimomi da ingantattun hanyoyin koya ingantattar tarbiyya ga yara. 

Saboda muhimmancin littafin nan, zan bi sahun Dokta Musa Muhammad Tukur, wanda ya rubuta mukaddima a shafi na db zuwa na dbi, wanda ya ce: “Saboda haka ina kira da babbar murya ga al’ummar Musulmi, kowa ya yi kokari ya mallaki wannan littafi, ya karanta abubuwan da suke ciki kuma ya yi kokarin aiwatar da su gwargwadon iyawarsa, musamman iyayen yara, malaman tarbiyya da dalibai masu neman ilimi, maza da mata.”