Sharhin littafin ‘Zamani ina za ka da mu’

Kullum ina yawan fada cewa shi rubutu duk yadda aka yi shi, ana yin sa ne domin a ilimantar ko a fadakar ko kuma a yi hannunka mai sanda ga al’umma a kan wani bakon abu da ya gallabi ko ya damu al’umma domin a samu sauki ko domin a gyara don ci gaban al’umma. […]

Sharhin littafin ‘Zamani ina za ka da mu’

Bangon littafin Zamani Ina Za Ka Da Mu

Kullum ina yawan fada cewa shi rubutu duk yadda aka yi shi, ana yin sa ne domin a ilimantar ko a fadakar ko kuma a yi hannunka mai sanda ga al’umma a kan wani bakon abu da ya gallabi ko ya damu al’umma domin a samu sauki ko domin a gyara don ci gaban al’umma.

Tabbas mun tsinci kawunanmu a wani irin yanayi inda ake koke-koke kan lalacewar tarbiyya a tsakanin maza da mata; musamman ma matasa. Har ta kai wasu bakin al’adu sun cudanya da al’adun Malam Bahaushe, an kori kunya da kawaici da sanin daraja da mutunci musamman a tsakanin mata wadanda suke dauke da tubalin gina al’umma.

Wayewar zamani ta sanya mace ta fito daga shingen kariya da darajar da addinin Musulunci ya yi mata, ta fito tana gogayya da maza a dukkan bangarorin rayuwa. Hakan ya sa mace ta shiga cikin kunci da gararin rayuwa.

A cikin wannan sabon littafi da Dokta Aliyu Ibrahim Kankara ya rubuta, ya baje duk wani nau’in abu marar alfanu da za a iya sa mace ta shiga cikinsa idan har ba a ba ta ingantacciyar tarbiyya ba da addinin Musulunci ya ce a yi domin a samu ingantacciyar al’umma.

Dokta Aliyu Kankara shi ne marubucin littafin tarihin shahararren mawakin nan Alhaji Mamman Shata Katsina mai suna: ‘Shata Mahadi Mai Dogon Zamani,’ kuma da shi aka rubuta littafin ‘Shata Ikon Allah,’ wanda suka rubuta da wadansu mutane uku a baya.

Labarin littafin Zamani Ina Za Ka Da Mu yana bada labarin wata mata ce mai suna Surayya wadda ta auri Nas Abbas wanda gogaggen dan boko ne, malamin asibiti a can birnin Katina, lokacin da ya aure ta iyakar iliminta na sakandare ne, bayan aurenta na farko inda ta auri Aliyu wanda suka yi rayuwa a kauye, inda ba ta da ’yanci, suka yi rayuwar hannu-baka-hannu-kwarya, tunda shi Aliyu  ba mai wadata ba ne. Amma ita Surayya ta yi karatun addini sosai. Nas Abbas ya matsa mata sai ta yi karatu a jami’a tare da sama mata aiki bayan ta gama. Tura ta kasar waje karatu wato shigarta Jami’ar Andaz a kasar Denmark ya canja rayuwarta gaba daya inda a can ne ta rikide ta zama wayayya ta shiga sabuwar rayuwar zamani ta iskanci, fajirci da shaidanci. Wannan ya jawo mata kora daga makarantar.

Zuwanta Turai karatu ne ya sa ta bude sabon shafi a rayuwarta kasancewar babu mai kwabarta, a can ne ta hadu da wani mutum mai suna Ayyam daga neman masauki wanda suka rika ma’amala kamar ma’aurata (alhali da aurenta). Daga nan bayan sun rabu, ta koma wajen wani malaminta (Dokta Zin Walsha) wanda har aure suka yi ta kuma haihu da shi, sun samu ’ya mace. Wani abin ban haushi shi ne ’ya’yan da suka haifa da Nas Abbas a she ba nasa ba ne (wani abokinsa ne ya ci amanarsa) kuma da yardar Surayya suka haife su.

Tabbas zuwan wannan littafin a wannan lokaci abin yabawa ne saboda zai sa maza su yi taka-tsantsan wajen zabar abokan rayuwa masu tarbiyya da sanin ya kamata da rike amana. Marubucin littafin ya yi namijin kokari kuma abin burgewa shi ne ingantaccen aiki da aka yi wa littafin abin koyi ne ga sauran marubuta, sai dai an rika jefa kalmomin Ingilishi a cikin littafin ko me ya kawo haka?

Za a iya samun Aminu Ahmed Mohd Tsagem ta: 08065032730

Kirsimeti: FRSC ta aike jami’ai 1,539 zuwa Kano

Gwamnatin Kano na shirin tara harajin 80bn a 2025

Kirsimeti: Zulum ya ɗauki nauyin jigilar fasinjoji 710 zuwa garuruwansu

Ɗan shekara 60 ya rasu a hatsarin kwalekwale a Sakkwato