Shari’a tsakanin Adam A Zango da dan jarida ba ta kaya ba

A makon da ya gabata mun kawo muku labarin ofishin ‘yan sanda na Metro da ke Kaduna ya nemi fitaccen jarumin fina-finan Hausa Adam A Zango da editan Mujallar Fim, Aliyu A Gora II su dawo don a ci gaba da bincike kan karar da editan ya kai jarumin, inda ya ce ya lakada masa […]

Shari’a tsakanin Adam A Zango da dan jarida ba ta kaya ba

Adam A Zango da Editan Mujallar Fim, Aliyu A Gora IIA makon da ya gabata mun kawo muku labarin ofishin ‘yan sanda na Metro da ke Kaduna ya nemi fitaccen jarumin fina-finan Hausa Adam A Zango da editan Mujallar Fim, Aliyu A Gora II su dawo don a ci gaba da bincike kan karar da editan ya kai jarumin, inda ya ce ya lakada masa duka har da ya yi masa karo, wanda kuma jarumi ya karyata zargin, ya ce sun cakumi juna ne.
Dukkan bangarori biyun sun halarci ofishin da misalin karfe  takwas na safe, inda kuma aka ci gaba da bincike har zuwa karfe biyu saura na rana, inda kuma aka bukaci su koma don a ci gaba da binciken a jiya Alhamis.
Sai dai wata majiya da al’amarin ya wakana a gabanta ta yi wa wakilinmu bayanin cewa jarumin ya shigo da wadansu cikin batun, kuma shugabannin kamfanin da ke buga mujallar Fim suna jin kunyarsu.”
“A yadda abubuwa suke tafiya zai yi wahala ba kotu ce za ta kawo karshen wannan al’amarin ba.” Inji wata majiya.
Wakilinmu ya nemi jin ta bakin jarumin amma ya ki cewa komai, kamar yadda shi kuma editan ya ce ya bar komai a hannun shugabanninsa.