Shari’ar Batanci: Abduljabbar ya kori lauyansa

Sheikh Abduljabbar Nasir Kabara da aka yanke wa hukuncin kisa ta hanyar rataya bisa laifin yin batanci ga Mazon Allah, ya kori lauyansa

Shari’ar Batanci: Abduljabbar ya kori lauyansa

Sheikh Abduljabbar Nasir Kabara da aka yanke wa hukuncin kisa ta hanyar rataya bisa laifin yin batanci ga Annabi Muhammad Sallallahu Alaihi Wasallam ya kori lauyansa.

Barista Sadiq Yusuf ne yake kare Abduljabbar a shari’ar da ake yi masa a gaban Kotun Daukaka Kara a Jihar Kano, inda malamin ke kalubalantar hukuncin da aka yanke masa.

Aminiya ta rawaito cewa A ranar 15 ga watan Disamba 2022 Babbar Kotun Musulunci da ke zamanta a Kofar Kudu ta yanke wa Abduljabbar Nasir Kabara hukuncin kisa ta hanyar rataya a kan laifin batanci ga Annabi Muhammad Sallallahu Alaihi Wasallam.

Tunda farko Abduljabbar ya shigar da kara ta hannun lauyansa Sadiq Yusuf inda yake kalubalantar kundin shari’ar da Babbar Kotun Musuluncin ta yi inda ya ce akwai kurakurai a ciki.

A zaman kotun na ranar Laraba lauyan gwamnatin Kano kuma wadanda ake kara, Barista Bashir Saleh, ya shaida wa kotun cewa sun sami takarda mai dauke da sa hannun mai kara da kansa, mai kwanan watan 10 ga watan Mayu, 2024 cewa ya kori Sadiq Yusuf a matsayin mai kare shi.

A cewarsa, “kasancewar shari’a ce ta laifi ba za mu iya ci gaba da ita ba a wannan yanayin.”

Sai dai lauyan gwamnatin ya roki kotu da ta yi watsi da rokon da mai kara ya shigar inda yake kalubalantar kundin shari’ar Babbar Kotun Shariar Musulunci.

Sai dai yayin da yake yanke hukunci, alkalin kotun, Mai Shari’a Nasiru Saminu, ya yi fatali da rokon lauyan gwamnati, sannan ya dage shari’ar zuwa lokacin da mai kara zai samu wani sabon lauyan da zai tsaya masa a shari’ar.

Idan za a iya tunawa an samu Abduljabbar da lafin batanci ga Manzon Allah Sallal Lahu Alaihi wa Sallama ne a ranakun 10 ga watan Augusta da 25 ga watan Oktoba da 20 ga watan Disamba, daga karatuttukansa da suka gudana a masallatansa guda biyu da ke unguwar Gwale da kuma na Sabuwar Gandu.

DSS ta gurfanar da Mahdi Shehu kan zargin ta’addanci

Sojoji sun kashe mataimakin Bello Turji

Harin ’Yan Fashi: Buni ya jajanta wa ’yan kasuwar Ngalda

An saki matar Ekweremadu daga gidan yari a Birtaniya, ta dawo Najeriya