Shari’ar jabun dokar majalisa: Saraki da fadar Shugaban kasa sun sa zare

Shugaban Majalisar Dattawa Sanata Bukola Saraki da fadar Shugaban kasa sun sanya zare sakamakon shari’ar jabun dokar majalisa, inda Sanata Bukola Saraki ya yi zargin cewa wadansu tsirarun mutane sun kwace ikon tafiyar da gwamnati daga hannun Shugaban kasa Muhammadu Buhari.Saraki ya bayyana haka ne a wata sanarwa da ya sanya wa hannu da mai […]

Shari’ar jabun dokar majalisa: Saraki da fadar Shugaban kasa sun sa zare
Shari’ar jabun dokar majalisa: Saraki da fadar Shugaban kasa sun sa zare

Shugaban Majalisar Dattawa Sanata Bukola Saraki da fadar Shugaban kasa sun sanya zare sakamakon shari’ar jabun dokar majalisa, inda Sanata Bukola Saraki ya yi zargin cewa wadansu tsirarun mutane sun kwace ikon tafiyar da gwamnati daga hannun Shugaban kasa Muhammadu Buhari.
Saraki ya bayyana haka ne a wata sanarwa da ya sanya wa hannu da mai magana da yawunsa ya aike wa manema labarai a Abuja a ranar Litinin, inda ya ce, mutanen da suka aikata hakan sun kwace iko ne domin biyan bukatunsu na kansu.
Sanarwar ta ce, wannan ‘bi-ta-da-kulli’ da ake yi wa Majalisar Dokokin na nuna irin matsalar da dimokuradiyya ke fuskanta, wadda jama’ar kasar nan suka sha wahala wajen ganin tabbatuwarta.
Sanata Saraki ya ce, tuhumarsu da ake yi a madadin Gwamnatin Tarayya na nuna cewa wadansu kusoshi a gwamnati sun ki yarda cewa ana gudanar da majalisar ce bisa dokokinta, wadanda kuma da su ne ake amfani wajen warware duk wata matsala da ake fuskanta a majalisar.
Ya ce a shirye yake ya ci gaba da shanye duk wata barazana da ke fuskantarsa da kuma tsayuwa kan gaskiya da sauke nauyin al’umma da ke kansa.
Sanata Saraki da mataimakinsa Ike Ekweremadu da tsohon Akawun Majalisar, Salisu Maikasuwa na fuskantar tuhuma ne kan yin jabun dokoki a Majalisar Dattawan.
Sai dai a martanin da Kakakin Shugaba Buhari, Mista Femi Adesina ya mayar kan zargin na Sanata Bukola wadda ya aike wa manema labarai, ya kalubalanci Sanata Saraki ya bayyana sunayen mutanen da yake zargi da kwace ikon gwamnati daga Shugaba Buhari.
Ya ce, “Idan Saraki zai bayyana sunayen mutanen da kwace iko da gwamnati ko suka kafa wata gwamnati a cikin gwamnatin (Buhari), a nan ne za mu tabbatar da maganar da yake yi ba shifcin-gizo ba ne. Amma yanzu zargi kawai yake yi, wanda bai kamata wani ya kula da shi ba.”
Mista Adesina ya ce kundin tsarin mulkin Najeriya ya bai wa Ministan Shari’a, wanda kuma shi ne Babban Lauyan Gwamnati damar shigar da karar duk mutumin da ake zargi da aikata laifi domin a hukunta shi.
Ya ce “Don haka duk mutumin da ya ce Shugaba Buhari yaron wani ne bai san abin da yake yi ba, domin kuwa ba halayyarsa ba ce.”