Shari’ar Maryam Sanda ta samu cikas sakamakon rashin shaida

’Yan sanda sun kasa gabatar da shaida a shari’ar da ake yi wa Maryam Sanda biyo bayan shawara da shaida na farko ya yanke na ficewa daga dakin shari’ar kafin a kira shi.   Dan sanda mai gabatar da kara, CSP James Idachaba ya fada wa kotun cewa shaidu biyu suna cikin kotun kuma a […]

Shari’ar Maryam Sanda ta samu cikas sakamakon rashin shaida

’Yan sanda sun kasa gabatar da shaida a shari’ar da ake yi wa Maryam Sanda biyo bayan shawara da shaida na farko ya yanke na ficewa daga dakin shari’ar kafin a kira shi.
 
Dan sanda mai gabatar da kara, CSP James Idachaba ya fada wa kotun cewa shaidu biyu suna cikin kotun kuma a shirye yake ya  gabatar da su.
 
To sai dai lauyan Maryam, Joseph Daudu ya fada wa kotun cewa yana da bukata da ya gabatarwa kotun na neman kotun ta wanke wacce ake zargi kuma ta kori karar.
 
Ya nemi kotun ta ummarci ’yan sanda su baiwa wacce ake zargi damar nazarin dukkan takardun karar.