Shari’ar Murja: Kotu ta umarci Hisbah ta Akawun Majalisar Kano su bayyana a gabanta

Dokar da ake takkadama a kai ita ce Hisbah ke amfani da ita wajen kama masu laifi.

Shari’ar Murja: Kotu ta umarci Hisbah ta Akawun Majalisar Kano su bayyana a gabanta

A ci gaba da shari’ar da fitacciyar ’yar TikTok, Murja Ibrahim Kunya, ta yi karar hukumar Hisbah ta Jihar Kano, babbar kotun jihar ta bukaci Hukumar ta zo ta yi mata bayani kan wasu dokokinta masu kama da juna.

Babbar Kotun Kano da ke zamanta a Bompai ta umarci Hukumar Hisbah ta ta turo mashawarcinta a bangaren shari’a domin yin bayanin yadda Hukumar take amfani da dokokin biyu masu kama da juna wadanda kuma suka fara aiki a rana daya.

Lauyoyin Murja Ibrahim Kunya na kalubantar dokar Hisbah da cewa ta saba wa Kudin Tsarin Mulkin Najeriya.

Dokar da ake takkadama a kai ita ce Hisbah ke amfani da ita wajen kama masu laifi.

Kotun ta kuma umarci akawun Majalisar Dokokin Jihar Kano ya bayyana a gabanta domin yin cikakken bayanin dalilin da majalisar ta samar da dokokin masu kama da juna a rana daya.

Kotun ta nemi ya yi bayani dalla -dalla a kan shin ana amfani da Sashe na 10 na dokar Hisba ta KSHB law 2003 da wata dokar Mai taken KSHB law (4) 2003.

Haka kuma kotun ta umarci Hukumar Dab’i ta Jihar Kano da ta zo ta yi bayani game da takardar bangaren shari’a wacce aka yi amfani da ita wajen aiwatar da dokar Hukumar Hisbah.

Haka kuma Hukumar za ta bayar da bahasin yadda aka yi wannan doka ta zama cikakkiyar doka.

Idan za a iya tunawa fitacciyar ’yar TikTok, Murja Ibrahim Kunya, ta yi karar Kwamishinan Shari’a na Jihar Kano da Alkalin Babbar Kotun Musulunci da ke Kwana Hudu Malam Nura Yusuf Ahmad da Kwamishinan ’Yan sanda na Jihar Kano da Hukumar Hisbah ta Jihar Kano da Asibitin Kwakwalwa na Gwamnatin Tarayya da ke Dawanau.

Duba da rashin gamsuwar kotu gane da Sashe na 10 na dokar Hukumar Hisbah Alkalin Kotun Mai sharia Nasiru Saminu ya bayar da wadancan umarni inda kuma ya dage sauraren shariar zuwa ranar 17 ga Yuli, 2024.

Davido zai bai wa marayu tallafin N300m a Najeriya

Ba mu yanke hukunci kan ƙudirin harajin Tinubu ba — Abbas

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos