Sharrin harshe

Kamar yadda zabuwa ba ta iya goge zanen jikinta, haka nan ma xan siyasar Najeriya bai iya canja halinsa. Bisa ga dukkan alamu xan siyasar Najeriya bai koyi darasin komai  daga  munanan al’amuran da halayensa  da kuma sharrin harshensa suka jawo wa kasarsa ba tun daga zamanin mulkin Turawa, har ya zuwa bayan  samun ‘yancinta […]

Sharrin harshe

Kamar yadda zabuwa ba ta iya goge zanen jikinta, haka nan ma xan siyasar Najeriya bai iya canja halinsa. Bisa ga dukkan alamu xan siyasar Najeriya bai koyi darasin komai  daga  munanan al’amuran da halayensa  da kuma sharrin harshensa suka jawo wa kasarsa ba tun daga zamanin mulkin Turawa, har ya zuwa bayan  samun ‘yancinta da kuma wannan mawuyacin lokacin da ake ciki, Hasali ma kokari ake yi don komawa gidan jiya, ta hanyar yin furuce-furucen kiyayya ga wasu jinsin kasar nan . 

Babbar illar da mugayen halayen ‘yan siyasar Najeriya suka haifar ita ce bakar gaba tsakanin kabilu da mabiya addinai mabambanta. A lokutan baya an yi gogayya mara armashi da ta buga wa ‘yan siyasar jihohin kasar nan guda uku kaimi wajen bin waxancan manufofin da aka jingina jam’iyyun siyasar da kowace jiha ta haifar a kai, waaxanda kuma jama’arsu  suka runguma, suka xaure musu gindi.

A sakamakon haka ne aka yi mummunar siyasar da  ta rarraba kawunan al’ummomin kasar nan, ta kuma yi sanadiyyar shigowar sojoji cikin harkokin mulki har aka yi yakin basasa. Amma sai dai da farko matsalolin ba su tsananta kamar na wannan marrar ba, a maimakon haka ma kara dankon zumuncin al’ummomin kasar suka yi.  To, tun daga wancan lokaci ne kuma sai aka shiga wani zamani na rikice-rikicen addini  waxanda suka farraka kawunan kanana da manyan  kabilun kasar nan. Wannan al’amari ya yi sanadiyyar muzguna wa wasu kabilun da Yahudu ke yaki da addinin da suka yi imani da shi, har ma ta kai an nemi a yakice lardinsu daga cikin kwaryar tarayyar Najeriya.

A yanzu siyasar addini ce ke tasiri a Najeriya domin a dukkan lokutan da a kan yi zaben shugaban kasa a kan fahimci yadda Najeriya ke  darewa gida biyu: Musulmi na goyon bayan xanuwansu Musulmi, Kiristoci kuma na tare da xanuwansu Kirista. Wannan ne ya nuna cewa dukkan abin da ake yi sai an yi la’akari da batun addini kafin aiwatar da shi. Ta kai ma a wasu garuruwa da manyan biranen jihohin kasar nan muhallin Musulmi dabam, na Kirista kuma dabam, babu wani  mai halartar wuraren da mazauna can ba mabiya addininsa ne ba.

Duk da cewa gwamnatoci, musamman ma na jihohin Arewa,  na ta kokarin faxakar da jama’arsu game da illolin rarrabuwar kawunan jama’a, amma ba ta canja zani ba, domin kuwa limamai da jagororin  jama’an da ya kamata su rungumi junansu don su mance bambance-bambancen da ke tsakaninsu  ne ke ta kara ruruta wutar da kiyayyar addinin junansu ke haddasawa.

Babban abin tsoro game da wannan xabi’a ta ‘yan siyasar kasar nan, masu yin amfani da kalamomi don bata  addinin wasunsu  don biyan bukatunsu, shi ne yadda  idan  wata baraka  ta faru a jam’iyyar da take mulki za ta iya tayar da zaune tsaye a kasar, musamman ma a lokutan yakin neman zabe ko yayin da ake yin zaben, dambarwar da ke faruwa tsakanin wasu shugabannin jam’iyyun siyasa da  wasu gwamnonin jam’iyyunsu  waxanda  ke kukan ana muzguna masu ta nuna cewa dimokuraxiyyar kasar nan na bisa wani mawuyacin siratsi, kuma akwai alamun cewa hakan zai sa kasar tuntsurawa cikin matsnancin yanayi. Muddin gwamnatoci za su ci gaba da yin amfani da jami’an tsaro don dakile jam’iyyun siyasa ko taxiye shugabanninsu , kaman yadda ake yi a halin yanzu a ko ina a faxin tarayyar kasar nan, to ba shakka za a koma gidan jiya da na shekaran jiya, kuma ko da soja ba za su iya sake kutsowa ba don hana zalunci, harkokin tattalin arziki da na zamantakewa ba za su kankama yadda ya kamata ba, kuma babu abin da zai hana matsalolin da miyagun furuce-furucen ‘yan siyasa da ke nuna kiyayya ko kuma gaba tsakaninsu  za su kara  fitowa fili ba, sa’annan kuma za su ci gaba da yin kamari  har sai hakan ya  kai ga rugujewar kasar. Allah Ya kiyaye.

A yanzu dai talakawa na fatan cewa za a samu sa’ida a wannan karon ganin irin wahalhalun da aka sha fama da su game da matsalolin da rashin kame harshe da nuna tsabagen gaba ko matukar kiyayya ga abokan zama ke janyowa,  a kuma  dukufa addu’a  a halin yanzu don kada nan gaba ‘yan siyasa da  jam’iyyunsu su  koma bisa tafarkin da aka saba.  Hakan ba zai yiwuwa ba sai  idan  an ba jama’a damar  nuna ra’ayoyinsu a zahiri  a siyasance  ba tare da tsangwama ko kyararsu ba.. 

Lokaci ya yi da shugabannin jam’iyyun siyasa da mabiyansu da kuma zababbun shugabanni  za su fara tunanin yadda za a gudanar da harkokin siyasa cikin kwanciyar hankali don shimfixa mulki mai armashi ba tare da hayaniya ko hayagagar da za su tayar da yamutsi ba.  Ana dai sane da cewa idan jama’a  na  cikin halin matsin rayuwa komai na iya faruwa, ganin cewa idan fatara ta yi kanta takan zama iko, talaka ya aikata son ransa ba tare da damuwa da sakamakon aikinsa ba.

To amma me ke kawo yanayin da ke haifar da kuncin da zai kai ga furta wasu kalamun da ke tayar da hankali ko nuna tsabar kiyayya da bakar gaba tsakankanin al’umma? Rashawar da ta zauna ne da gindinta a kasar nan ke sa talakawa  nuna kiyayya  ga  shugabannin da suka zamanto  iyayen gidan da ke tallafarta kamar ‘yar lele. Haram ta kasance  a bar kwalliya ga mahukuntan da ke kankarar talaka, kuma da ita suke sutura. Ita ce abincinsu dare da rana. Hakan ya sa talakawan da ake yi wa kallon ayaba  sun dawo daga rakiyar shugaban da suke yi wa kallon biri.

A kullum sai an ji sabon labari game da wani tsohon shugaba ko wanda ke rike da madafun iko da aka gurfanar gaban hukuma bisa zargin ha’inci ko almundahana da dukiyar jama’a  Ya kamata a ce dunkiyar  talakawan da suke wafcewa ana amfani da ita ce don kyautata rayuwarsu. Waxannan al’amura ne ke sa wasu talakawan furta ra’ayoyinsu na kiyayya game da  shugabanni, wani lokaci ma sai abin ya shafi kabilar shugaban da aka samu da  aikata laifin maguxI, kuma hakan ya zamanto abin zambo da zagi har da kyamar sauran ‘yan kabilarsa.

Muddin  shugabanni za su daina aikata ha’inci irin wanda aka ambata, a komo  ana sarrafa dukiyar kasar yadda ya kamata, ana kuma yin amfani da ita ta hanya mai kyau, to hankulan talakawa zai kwanta, su daina batutuwan da suka jibanci kiyayya, da kuma yin gaba da wasu, kuma talaka zai yi alfahari da shugaba ko daga wane bangare na kasar nan ne ya fito, idan har har ya kasance mai kamanta gaskiya da shimfixa adalci a dukkan al’amuransa.

Najeriya za ta kasance aljannar duniya ga ‘ya’yanta da kuma bakin da ke  kawo ziyara, idan har kowane xan kasa zai kiyaye irin kalamun da ke fitowa daga bakinsa game da waninsa, domin shi harshe guba ne, kuma kamata ya yi miyagun shugabanni su kyautata halayensu domin  kowa ya tsira daga sharrinsu. Fitina dai barci take yi, Allah kuma Ya la’anci mai tayar da ita.

Ba mu yanke hukunci kan ƙudirin harajin Tinubu ba — Abbas

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos

Kasuwar Laranto da ke Jos ta yi gobara