‘Shata ya yi wa Ahmadun Gaya hidima kafin ya yi masa waka’
Alhaji Isa Sallau Jibrin mutumin Kibiya da ke Rano ta Jihar Kano ne. Shi ne Sarkin Fawan Sojoji a Bonny Camp, Ikko da kuma a fagen yaki a kasar Saliyo. Shi ne mahaifin mawakin zamani, Ali Isa Jita kuma yanzu yana sana’a a rukunin gidajen ’yan majalisa na Apo, Abuja. A tattaunawarsa da Aminiya, ya […]
Alhaji Isa Sallau Jibrin mutumin Kibiya da ke Rano ta Jihar Kano ne. Shi ne Sarkin Fawan Sojoji a Bonny Camp, Ikko da kuma a fagen yaki a kasar Saliyo. Shi ne mahaifin mawakin zamani, Ali Isa Jita kuma yanzu yana sana’a a rukunin gidajen ’yan majalisa na Apo, Abuja. A tattaunawarsa da Aminiya, ya bayyana wa wakilinmu yadda aka yi har Shata ya yi wa Ahmadun Gaya waka. Ga yadda tattaunawar ta kasance:
Mene takaitaccen tarihinka?
Saboda an haife ni ranar Sallah, shi ya sa aka kirana da lakanin Sallau. A yanzu shekaruna 69. Ni dan Sarkin Fawan Rano ne, wanda kuma shi ne abokin maragayi Sarkin Rano Ila-Autan-Bawo. Ina iya cewa ni dan gata ne, domin ni ne dan auta a cikin yara 16. Bayan na kai shekara 17, sai aka tura ni karatun allo Kano wurin Malam dahiru Alaramma, inda muka zauna a Jimgau cikin birni. Wadanda muka yi karatu, akwai Muhammadu Maidankudi da Alaramma Mai ’Yankunduba.
Ya aka yi ka bude rumfarka kana dan Shekaru 19?
Ina karatu sai na rika zuwa aikin tsire, sannan na bar karatu inda na koma aikin fawa gadan-gadan, ana biya na lada gun dan uwana Bala a Fagge. Sannan ina da shekaru 19 na hada jari na fam biyu, na fara sayo saniya kudi hannu a garin dambatta, bayan na kafa rumfata a Gyadi-Gyadi kusa da Joji-Kwata, gefen titin kwata, inda nake yanka sa guda in sayar da danye da kuma yin tsire. Sannan kuma na shiga siyasar NEPU, ina bin Malam Aminu Kano.
Mene dalilin da ya sa aka rushe maka rumfa, da gaske kai mahaifin mawakin Hausa Ali Isa Jita ne?
Ina da shekaru 20 na yi aure a birni, daga bisani na sayi mota. Ganin haka ya sa wani mahauci ya sa malamin tsabta ya rushe mini rumfa, amma daga baya cikin ikon Allah na zamo ubangidansu dukkansu. A yanzu ina da yara 31 masu rai. Ciki har da mawakin zamani na Hausa, Ali Isa Jita.
Bugu da kari wani aminina mai suna Garba Rabi’u, wanda suka yi zaman mutunci tun yana makaranta har ya shiga aikin soja ya zama kyaftin kuma mai tsaron lafiyar Janar Muhammadu Magoro. Shi ya kai ni Barikin Bonny Camp a Ikko, inda na rika yi wa sojoji fawa amma ya ba ni dokar cewa kar in nemi mata ko ’yar soja da kuma barin kalle-kallen gidajensu a bariki.
A shekaru ashirin da na yi a bariki, ba a taba kai ni kwata-gadi (watau kai karata ko a kulle ni ba), domin na tsare doka har na koya wa wani dan kabilar Igbo mai suna Emma yin tsire kuma har yanzu yana nan a Barikin Bonny. Na yi zamani da hafsoshi kaman Joshua Madaki, Habu I.I. Hassan, Ongobani, Zidon, Abduylamalik Jibrin, Dambazau, Tukur Buratai da sauransu.
Akwai wani abin mamaki da ya faru da kai a bariki?
Yadda aka dauki igiyar daure shanu a shagona, sannan aka dauki Limamin Bariki mai suna Iman Elaro don ya yi addu’a kafin aka daure kuma ak harbe Janar Mamman Batsa, sannan Iman Elaro ya zo da zoben da Batsa ya ba shi, ya ce ya kai wa matarsa kuma ya kai mata. Sai kuma lokacin juyin mulkin Okah, inda aka harbi shanuna sannan a cikin kwana uku aka hana mu fita yawo a bataliya har sai da su Janar Zidon suka kamo Gideon Okah.
Ya aka yi aka je da kai fagen yaki kasar Saliyo?
Soja suka ce sai in bi su zuwa kasar Saliyo domin in rika yin fawa. Bayan na sami wuri daga baya sai na fada cikin jidali, domin ’yan tawaye na zuwa su ce in ba su kudi. Da abin ya fara yawa sai na fada wa soja, sai aka sa ’yan sanda suna aiki kusa da rumfata, ta haka na tsira da taimakon Janar-Janar Dambazau da Abdulmalik Jibrin da Ungobani da kuma Tukur Buratai.
Ya aka yi kuka saba da Alhaji Mammam Shata?
Na san marigayi Mamman Shata kuma shi ma ya san ni tun a Kano, sannan kuma a kudancin kasar nan. Mun fara haduwa ne da marigayi Mamman Shata a Neja ta Wafa da ke Kano, lokacin Shata na son ganin Alhaji Mamuda Wafa dantata, amma ya kasa ganinsa har sai da Alhaji Musa Guza Namamuda, wanda abokinsa ne na kut-da-kut ya yi masa iso, ya hada su har suka saba. Mun saba da Musa Guza don shi ma mahauci ne. Sannan a otel din Wazahed ta Sabongari Shata ya fara wakar da ya ke cewa: ‘Ina aljani abokin shaidan Musa Guza Namamuda. Filin garin Tashar Kuka, filinku ne ina shaida. Alhaji Musa Guza Namamuda.’
Wane abin mamaki ka sani da Mamman Shata?
Akwai abubuwan mamaki da suka faru da Mamman Shata, domin wani malamin asibiti ya bata masa rai, sai ya ce ko a nan a akwai malamin asibiti? Sai aka ce babu, sai dai akwai mai wanke gyambo. Sai ya ce a kira shi, da ya ga talaka ne, sai ya saya masa lemo, ya yi masa hidima. Sai ya barke da wakar: ‘Na gode wa Ahmadun Gaya. Doktan yake mai ba da magani.’ Ya yi wakar zambon ce don ya rama abin da malamin asibitin can ya yi masa.
Ko ya taba yi maka waka, ko kuma ka nemi da ya yi maka?
Ni bai taba yi mini waka ba kuma ban matsa sai ya yi mini waka ba. Idan Shata ya ga wanda ya sani amma bai tantance sunanasa ba, sai ya zuba masa ido ya ce: “Kai kana nan kuwa.” Ni dai duk inda ya gan ni yana ce min Alhaji Mainama, kuma yana sayen dabba, rago ko akuya amma ya fi son rago a yanka, a bankare, a hada yaji mai zafi kowa ya sa hannu ya yanka ya ci; ana hira ana dariya, ba ya rowa sam.
Ko wane irin shu’umanci na Shata ka taba gani?
A garin Shagamu na ga shu’umancin Mamman Shata, inda ’yan kungiya suka yi suka yi ya yi waka amma ya ki yi. Shi ya sa ban matsa ya yi mini waka ba. Yanzu ga shi dana na cikina, mai suna Ali Isa Jita yana waka irin ta zamani.