Shatrughan Sinha ya yi bikin cika shekara 68 a duniya
A ranar 9 ga Disamba ne dan fim Shatrughan Sinha ya cika shekara 68 a duniya, wanda haka ya sanya shi da iyalinsa suka hada kwarya-kwaryan biki. ’Ya’yansa, Lub da Kush da kanwarsu, Sonakshi sun taka rawa mai yawa domin ganin bikin ya samu nasara.Bikin ya kasance abin tunawa, musamman ganin muhimman ’yan fim ’yan […]
Shatrughan Sinha with wife at Ram Jethmalani’s birthday, Ramada

A ranar 9 ga Disamba ne dan fim Shatrughan Sinha ya cika shekara 68 a duniya, wanda haka ya sanya shi da iyalinsa suka hada kwarya-kwaryan biki. ’Ya’yansa, Lub da Kush da kanwarsu, Sonakshi sun taka rawa mai yawa domin ganin bikin ya samu nasara.
Bikin ya kasance abin tunawa, musamman ganin muhimman ’yan fim ’yan mazan jiya, kamar Amitabh Bachchan da Dharmendra da Shabana Azmi da Hema Malini da Rekha duk sun halarta.
“Ni ta karan kaina, ban yi amanna da shirya bikin cika shekara ba, matata ce ta ga ya dace ta shirya shi, don haka idan na ce ban amince ta yi haka ba, ban yi mata adalci ba. Abin da kawai ba ta yi ba shi ne, ba ta gayyaci zawarawana ba, wanda haka ya nuna cewa na zama mallakinta ita kadai har tsawon rayuwa.” Inji Shatrughan.
A lokacin da ake kacaniyar bikinsa, sai kuma ga shi jam’iyyarsu ta BJP ta samu nasarar zabe. Kasancewarsa daya daga cikin membobin jam’iyyar sai ya shagala da buga waya zuwa ga shugabannin jam’iyyar tasu. An ma jiwo shi yana cewa:
“Nasarar da jam’iyyarmu ta samu kamar wata kyauta ce aka ba ni a daidai wannan rana da na cika shekara 68 a duniya. Na yi matukar farin ciki da yadda zaben ya gudana. Ga shi kuma a daidai lokacin ne fim din da diyata ta shirya mai suna ‘R…Rajkumar’ yake ta samun tagomashi da amsuwa daga al’umma. Idan ka debe wadannan abubuwan farin ciki, ba na tunanin akwai wani tasiri mutum ya ce zai yi bikin zagayowar ranar haihuwarsa, musamman ma ganin yadda tsufa ya kama ni. Kodayake biki ne da aka shirya domin taya abokai da ’yan uwa murna.”
Wani al’amari da ya kara wa Shatrughan farin ciki da nasara a rayuwa, shi ne yadda ya samu gayyata daga Majalisar dinkin Duniya, inda a makon ne ma ya je Amurka ya gabatar da jawabi a gaban taron da majalisar ta tara.
“Wannan shi ne karo na uku da na samu gayyatar Majalisar dinkin Dukiya. Ko a bara ma an gayyace ni amma ban samu damar zuwa ba saboda lalurar rashin lafiya. Babu shakka abin alfahari ne da farin ciki a ce mutum ya wakilci kasarsa a irin wadannan muhimman taruka na dukiya.” Kamar yadda Shatrughan ya bayyana a yayin jawabinsa wajen bikin na ranar haihuwarsa.
A lokacin da yake gabatar da jawabin nasa, ya bayyana cewa: “Ina fata ’yan uwa da abokan arziki su kasance cikin koshon lafiya a kowane lokaci. Ina bukatar a ceto kasata daga almundahana da cin hanci da rashawa. Abin da nake fata ke nan, a yayin bikin nan na ranar haihuwata.”