Shawara da zaburarwa ga Gwamna Yari
Assalamu Alaikum. Ya Mai girma Gwamna ina fatar wannan wasika za ta sameka cikin koshin lafiya. Na yi wasikata ne don in bayar da shawara, in kuma zaburar da gwamnanmu ya ci gaba ayyukan alheri da ya faro ba tare da la’akari da bambadancin masu ingiza mai kantu ruwa ba, ko adawar magabta ba. Na […]
Assalamu Alaikum. Ya Mai girma Gwamna ina fatar wannan wasika za ta sameka cikin koshin lafiya. Na yi wasikata ne don in bayar da shawara, in kuma zaburar da gwamnanmu ya ci gaba ayyukan alheri da ya faro ba tare da la’akari da bambadancin masu ingiza mai kantu ruwa ba, ko adawar magabta ba.
Na zabi in bude sabuwar shekara da rubuta maka wannan wasikar domin tunatarwa da kuma rokon magance wasu Matsaloli guda (ukku) da suka damemu da ma wasu al’ummar Jihar Zamfara a cikin (2017) sune:
1.Ya Mai girma gwamna a cikin shekarar 2014 kasa aka dauki matasa su 1, 400 aiki, a tarihin Zamfara ban taba sanin ma’aikatan da aka dauka da tantancewa ba tun daga sanin asali da yin edams iri daban-daban kamar su ba, daga karshe aka tabbatar da su a matsayin ma’aikatan jiha, amma yau shekara ukku da wata takwas ba a taba biyansu albashi ba.
Duk wata hanya da ya kamata su bi sun bi sun roke ka har ta kai ga sun kai ka kara kotu, amma ba ka ce komai ba, kuma ba ka fadi dalilinka na rashin biyansu ba, muna rokonka ka yi hakuri ka tausaya musu ka biya su hakkokinsu don Allah.
2.Ya Mai girma gwamna Matsalar rashin aikinyi tsakanin Matasan mu tayi yawa, kuma tun 2011 da ka hau mulki ba ka kirkiro hanya ko da kwara guda ba ta samun aikin yi ga matasan mu hasali ma kusan mutum (5000) suka rasa ayukkansu, ta hanyar tantance ma’aikatan bogi da ake yi ko a yaushe.
Dole ne ’yan sara suka suyi muna yawa da masu shaye-shaye saboda rashin aikin yi. Don haka ina kira don Allah cikin kasashen duniyar da kake ziyarta ko wane sati ka samo muna wata kasa ta zo ta yi mana wurin koyon sana’o’i na jiha ko kuma namu da muke da shi na gidan (Dawa) ka bude mana shi, domin tun hawanka mulki ka rufe shi wanda ba mu san dalilin hakan ba, har zuwa yau.
3. Mun ziyarci garuruwan ’Yanku zo, ’Yanware da dauki d cikin kwkramar Hukumar Tsafe. Wallahi Mai girma Gwamna suna cikin wahalar rayuwa, tun daga rashin hanya zuwa ruwan sha. Akwai garin da ko mashin ba ya shiga. Don Allah kafin wa’adin mulkinka ya kare ka taimakesu da hanya daga cikin Tsafe zuwa garin ’Yar-talata.
A karshe muna yi maka jinjina a kan ayyuka ukku da ka yi a cikin 2017, da suka burgemu, su ne
1. Gyaran Makarantun mu na Sakandare a fadin jJihar Zamfara.
2. Yin tagwayen hanya daga Ahmadu Bello zuwa filin wasa zuwa Birnin Ruwa, har aka sake zagayo wa Gidauniyar Muslim foundation da ke rukunin gidajen G.R.A Gusau
3. kara bayar da aikin tagwayen hanya na titin Byepass da ke Gusau (Duk da yake aikin ya yi tsada, amma dai mun yaba ingancin aikin)
Allah ya ba ka ikon taimakawa ya kuma taimaki jihar mu ta Zamfara. Amin.
Mungode.
Kabiru Amadu Mai (Palice) Da Nura Muhammad Mai Apple Gusau 07035023811/08133376020 Muhammad Gusau <[email protected]>