Shawara ga dan majalisar wakilai na Ikara/Kubau

Na yi hakilon haduwa da kai amma abin ya faskara bayan wasu maganganu da muka yi da kai a waya tun watan azumin bara. Mun tsaya tsayin-daka a kanka muka yi canji a zaben 2011, saboda rashin gamsuwa da wakilcin tsohon dan majalisa Ahmad Tsoho Kargi. Tsoho Kargi ya kwashe shekaru 12 a majalisar jiha […]

Shawara ga dan majalisar wakilai na Ikara/Kubau
Shawara ga dan majalisar wakilai na Ikara/Kubau

Na yi hakilon haduwa da kai amma abin ya faskara bayan wasu maganganu da muka yi da kai a waya tun watan azumin bara. Mun tsaya tsayin-daka a kanka muka yi canji a zaben 2011, saboda rashin gamsuwa da wakilcin tsohon dan majalisa Ahmad Tsoho Kargi. Tsoho Kargi ya kwashe shekaru 12 a majalisar jiha da ta tarayya, amma bai tsinana mana komai ba sai kansa da iyalinsa.
Yusuf Bala Ikara ka kasance ba dan siyasa ba, ba mu taba jin labarinka a siyasa ba,  kwatsam ka shigo, cikin ikon Allah muna bukatar canji. Muka tsaya muka jajirce muka kawar da Ahmad  Tsoho Kargi da karfin zatin Allah (SWT).
Allah Ya ba ka nasara cikin sauki ba tare da ka sha wahala ba, domin mu mun fika shan wahala. Mun yi murna ganin mun samu sauyi da fatan ya zame mana mafi alkhairi. Bayan an rantsar da ku a majalisa an sanya ka a wasu kwamitoci kamar haka:
1. Al’adu da yawon shakatawa (Culture & Tourism).
2. Sufurin kasa (Land Transport).
3. Naija Delta.
4. Harkokin jihohi da kananan hukumomi (State & Local Gobt Affairs).
5. Kula da rijiyoyin Man Fetur (Petroleum Downstream).
6. Karafa (Steel)
Wadannan su ne kwamitoci da kake ciki. Hakika wadannan muhimman kwamitoci da za a yi tinkaho da su ga duk wanda ya samu nasarar kasancewa a cikinsu. Saboda ganin yadda wasu ‘yan majalisa suke kishin yankunansu wajen samar da ayyukan ci gaba da kuma samar da guraben ayyuka ga wadanda suka kammala karatu da ba da tallafi ga dalibai da mabukata. Wannan ya sanya ni kokarin ba ka shawara kan abubuwan da ya kamata ka rika yi.
Zan ba ka misali da dan majalisar tarayya mai wakiltar karamar Hukumar Soba, Barista Ibrahim Khalid. Ya kasance tun yana majalisar Jihar Kaduna mutum ne mai kokari ga al’ummar da yake wakilta. Yana tallafa wa daliban mazabarsa masu karatu a manyan makarantun kasar nan. Haka ma sauran al’umma wadanda suka dace da a taimaka masu. Duk inda ya ji ana daukar aiki, ya kan je ya jajirce har sai ya tabbatar da samar wa yankinsa ko a jiha ko a tarayya. Kuma haka yake kai komo wajen samarwa da ‘yan yankinsa gurabe a manyan makarantu da kanana a duk fadin kasar nan. Hakika tsohon dan Majalisarmu bai tabuka komai ba kan irin wadannan abubuwa na ci gaba. Mun yi murna ganin kai matashi ne kamar mu.
Ya kamata tunda kai sabon shiga ne, ka samu irin su Ibrahim Khalid masu zuciyar taimakawa mutanensu, don ka san hannu na taimaka wa wadanda kake wakilta. Ya ba ka shawara kan hanyoyi da dabarun da yake bi na ci gaban mazabarsa tunda mu ba zaka dauki tamu shawarar ba. Ganinka ko jinka ya zama wahala. Shi kuwa Ibrahim Khalid zaku rika haduwa a majalisa lokacin da ka samu zarafin lekawa.
Na kira ka a waya na gaya maka ga halin da ake ciki, ka ce na binciko maka bayani da hanyar da za ka bi don ganin an yi nasara. Na yi iya kokarina wajen tattara maka bayanai da yadda za ka yi ganin an samu nasara. Abin da ya ba ni mamaki shi ne, abin da ka gaya min kamar haka: “na kira mutumin na shaida masa ko ni wane ne, sai ya ce, na je na same shi ranar Litinin a ofishinsa a Abuja. Ni kuma matsalata ba na zama a Abuja ranar Litinin.” Wannan kalami na cewa “matsalata ba na zama a Abuja ranar Litinin, shi kuma ya ce Litinin ne zan same shi”. Wallahi Wannan magana da ka gaya min ta yi matukar daure min kai da ba ni mamaki sosai. Shin dama can a Abuja kake zaune, ko mu ne muka tura ka har ka samu zarafin kara aure da ajiye daya a Kaduna daya a Abuja yanzu? Ya kamata ka sani cewar mu ne muka zabe ka don ka kare mana muradanmu da kwato mana da hakkokinmu.
A wani shiri na gidan Rediyon Nagarta mai suna “Zauren Nagarta”. Na ji duk abubuwan da ka fadi, na gaskiya da akasin haka. A wannan shiri ne suka ba ka sarautar “Sardaunar Zauren Nagarta”.
A karo na biyu a zauren nagarta a nan ne na ji wasu abubuwa da ka lissafo wadanda suka daure min kai matuka. An ce ka raba babura 250, sai mai gabatarwar Nura Kuriga ya ce a’a, 450 ne akalla ka raba wa mutane. Sannan kuma kuma ka yi famfunan burtsatse akalla 109. Sai kuma asibiti wai da aka ce ka yi a Ikara wanda ka kashe akalla Naira miliyan 17. Sai kuma aka ce ka raba motoci 45. Ni dai dan mazabarka ne, tun a lokacin na so mayar maka da martani ds tambayarka. Kwatsam sai malaminmu ya zo shirin rediyon nagarta mai suna “An-ce ka-ce” ya yi maka tambayoyi 20 kan wannan shiri da ka yi na biyu da kuma bayanan da ka sake yi a shirin gidan rediyon tarayya na Kaduna mai suna “Dimokuradiyya adon kasa”. A shirin ka yi wasu bayanai wadanda suke bukatar tambaya.
Ina yawan kallon zaman majalisarku ta wakilai, amma ganinka da na yi na tsawon shekaru biyu bai wuce a kirga ba, kuma ban taba ganin ko daga hannu ka yi ba na neman izinin yin magana. Na gani sau daya ana zaman wani rahoton kwamitin da kake ciki. Ka rubuto bayaninka kana karantawa ya yin zaman kwamitin. Wadanda suka wakilce mu a majalisar tarayya mutane uku duk da kai, watau Tijjani Sani Paki (1999-2007), sai kuma Ahmad Tsoho Kargi (2007-2011), sai kuma kai daga 2011 zuwa yanzu. Mutane su rika yi wa kansu adalci, su daina neman abin da suka san ba za su iya ba, kamar yadda majalisar tarayya take, idan mutum ya san ba zai iya mikewa ya yi magana ba, to ya hakura, ya tsaya daidai shi.
Ni ba dan maula ba ne, amma na kan gaya wa mutum gaskiya kan hakkin da ke kansa don ya rabauta. Mu gudu tare mu tsira tare. Muna nan muna jiran da ka zo ka yi mana bayanin kudin ayyukan da ake ba ku duk wata uku don aiki a yankunanku. Ka zo ka yi mana bayani masu gamsarwa. “Ciki da gaskiya”.
Daga Idris Ibrahim Kubau.
e-mail: [email protected]

Majalisa ta buƙaci sojoji su kawo ƙarshen Lakurawa

Ɗan Aljeriya ya shiga hannu kan safarar makamai a Zamfara

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50