Shawara ga Gwamnan Jihar Zamfara

Sanin kowa ne gwamnatin Jihar Zamfara karkashin jagorancin Gwamna Abdul’aziz Yari Abubakar (Shettiman Zamfara) ta taka muhimmiyar rawa wajen inganta makarantun firamare da na sakandare  hadi da inganta titunan birane da kauyuka. Tabbas duk wani dan Jihar Zamfara da kewaye ya tabbatar da haka kuma muna jinjina da wannan gagarumin aikin na Gwamna. To amma […]

Shawara ga Gwamnan Jihar Zamfara

Sanin kowa ne gwamnatin Jihar Zamfara karkashin jagorancin Gwamna Abdul’aziz Yari Abubakar (Shettiman Zamfara) ta taka muhimmiyar rawa wajen inganta makarantun firamare da na sakandare  hadi da inganta titunan birane da kauyuka. Tabbas duk wani dan Jihar Zamfara da kewaye ya tabbatar da haka kuma muna jinjina da wannan gagarumin aikin na Gwamna. To amma kuma ina makomar matasanmu?

Tabbas har yanzu gwamnatin Jihar Zamfara ta bar baya da kura ganin yadda matasanmu suka zama abin tausayi saboda rashin aikin yi da ya yi musu katutu a sassa daban-daban na jihar musamman a cikin Gusau babban birnin jihar.

Haka ne ya sanya kusan kullum muke samun yawaitar barayi,  inda wannan babban ibtila’i ne ga duk al’ummar da ta tsinci kanta a cikin irin wannan hali.

Kwanan nan ne aka samu nasarar kashe kasurgumin barawon nan dan bindiga da ya addabi al’umma, mai suna Janar Buharin Daji wanda har yanzu  ana tafka muhawara a kan kashe shi da aka yi musamman a kafafen sada zumunta na zamani wato (Social Media) inda mafi yawan mutane suke fadin cewa kashe Buharin Dajin ba shi ne samun saukin kashe-kashen rayuka ba, idan har gwamnati da jami’an tsaro ba su tashi tsaye ba wurin mayar da hankalinsu wajen kara inganta tsaro a Jihar Zamfara.

Ko a kwanan nan mun samu labarin wadansu ’yan bindiga da suka kai hari a wani kauye mai suna Dogon Daji  inda suka banka wa garin wuta sai dai ba mu samu labarin ko an rasa rayuka ba.

Haka kuma a karamar Hukumar Maru a cikin wani kauye da ake kira Bingi mun samu labarin shigar wadansu ’yan bindiga inda a nan suka samu sa’ar yi wa mutanen garin kwanton-bauna suka kashe rayuka da dama hadi da jikkata wadansu.

Sannan a ranar Litinin din makon jiya ma mun samu labarin sace Shamsuddeen Tatti Usman, wani dalibi a  Jami’ar Tarayya da ke Gusau, (Federal Unibersity Gusau, FUG) wanda har yanzu babu wani labari dangane da wannan dalibi.

Duk wadannan suna zuwa ne jim kadan da kashe Janar Buharin Dajin a Jihar Zamfara. 

A bisa wannan muke kira da babbar murya ga Mai girma Gwamnan jiharmu ta Zamfara ya dubi wannan lamarin da idon basira domin daukar matakan da suka dace wajen magance wannan matsalar.

Ko shakka babu mun ji dadin ziyarar da Shugaba Muhammadu Buhari ya kawo a cikin wannan jiha tamu, kuma mun ji dadin irin kalamansa na son tallafa wa matasa ta kowane bangare domin dogaro da kai, hadi da samar musu da ayyuka don inganta rayuwarsu.

Da wannan muke amfani da wannan dama domin bai wa Mai girma Gwamna Yari shawara ta musamman domin ya bullo da wasu hanyoyi wadanda za su taimaka wajen samun wasu sahihan bayanai a duk lokacin da wani abu yake faruwa, a cikin gari ko a kauyuka.

Muna addu’ar samun zaman lafiya a cikin Jihar Zamfara da Arewacin Najeriya da ma kasar nan baki daya. 

 

Wannan sako ya fito ne daga Sulaiman Mohammed Gusau da Nura Muhammad Mai Apple Gusau dan kishin marasa galihu kuma dan kungiyar Muryar Talaka ta kasa Reshen Jihar Zamfara 07067297714/08133376020