Shawara ga gwamnatin Jigawa da attajirai
Allah mun gode Ma da Ka sa muna cikin wadanda za su azumci wannan wata mai alfarma na Ramadan. Watan Ramadan wata ne da ake son yawaita ayyuka na alkhairi tare da rubanya su. Kada ka raina aikin alkhairi komai kankantar sa maza hanzarta yin sa. Azumin bana ya zo wa al’ummar Nigeria cikin wani […]
Allah mun gode Ma da Ka sa muna cikin wadanda za su azumci wannan wata mai alfarma na Ramadan. Watan Ramadan wata ne da ake son yawaita ayyuka na alkhairi tare da rubanya su. Kada ka raina aikin alkhairi komai kankantar sa maza hanzarta yin sa.
Azumin bana ya zo wa al’ummar Nigeria cikin wani dan yanayi na matsin rayuwa wato rashin kudi da tsadar kayan masarufi wanda hakan ya sanya talakawa da dama cikin kuncin rayuwa. Shugabanni ya kamata ku yi tsarin da zai wadata talaka da abinci a kyauta ko a farashi mai rahusa.
Azumin bara gwamnatin Jigawa ta raba wa talakawa masara. Muna yiwa gwamnatin Jigawa tuni cewa talakawa na da tsananin bukatar tallafi fiye da bara, kamata yayi a bana ace kowane magidanci ya sami buhun masarar guda daya in so samu ne ma a hada masa da na shinkafa domin ya samu yayi azumi cikin nutsuwa da kwanciyar hankali. Mun sani a asusun Jiharmu akwai kudin da za a iya ciyar da talakawan Jihar nan ba tare da asusun ya san ana yi ba. Shugabanni ya kamata ku sani yunwa ta na daga cikin abubuwan dake haifar da ayyukan ta’addanci a cikin al’umma, wadanda suka hada da sata, danfara da sauransu.
Attajirai ku ji tsoran Allah ku rika fidda zakka yadda Allah yace a fidda ta, ta haka ne dukiyarku za ta yi albarka. Ita zakka farilla ce, yinta dole ne ga duk mai dukiya idan dukiyar ta kai matsayin zakkar dole ya fidda kamar yadda Allah ya bada umarni, sannan ku baiwa wadanda ya kamata a ba wa zakkar (mabukata wadanda Allah yace a baiwa)yin haka ne zaman lafiyarku da ita kanta dukiyar. Ita kuma zakka ba a jinkirta ta da zarar lokacin fidda ta yayi kada ka ce sai watan Ramadan za ka fitar, hakki ne na Allah lokacin da dukiyar ta kai matsayin zakkar ya cancanta ka fidda, idan watan Ramadan ya kama kuma ganin damar ka ne ka kyautatawa al’umma amma ba ka ware kudin zakkar ba, ka sa a rika yin kunu a na rabawa talakawa ba ko wani abu makamancin haka. Da ace attajiran Nigeria za su fidda zakka yadda Allah yace a fidda tabbas da mun ji saukin halin kuncin rayuwar da muke fama da shi… Ka tsaya ka yi tunani a ranka ka hararo attajiran garinku ace kowanne daga cikinsu bana ya fidda zakkar dukiyarsa kamar yadda Allah yace a fidda ka na jin ba za a sami saukin halin da ake ciki ba na yunwa? A bisa wannan dalilin har kullum na ke kalubalantar wasu attajiran na Jihar Borno domin da ace za su rika fidda zakka yadda Allah yace a mallakata ga yan gudun hijira ba na jin za su na kukan yunwa duba da yadda Jihar Barno take da gingima-gingiman attajirai. Ba na ce ba sa fidda zakka ba ne a’a masu fitarwar gaskiya ne kalilan. Matsayin zakka a muslunci ba sai an yi dogon bayani ba domin duk wani musulmi ya san matsayin da take da shi domin ta na nuna cikir musluncin mutum ne.
Shawara ga masu daukar nauyin karatu a gidajen radio ba mun ce kada ku dau nauyin karatun ba ne duka a’a ku dan rage maimakon daukar nauyin sai a rika tallafawa talakawa da kudi. A misali ace duk shekara ina daukar nauyin sanya tafsir a gidan radio akan dubu (N500,000) to bana da rabawa makota na mutum biyar dubu dari-dari (N100,000) zan yi ina ga zai fi muhimmanci duba da yadda aka fada matsin rayuwa a kasar nan.
Abin da ya shafi kyautatawa kuma ba sai attajirai ba kowane mutum na iya yin iyakar gwargwadon karfinsa kada ka koma gefe ka na zagin masu kudin garinku, ko unguwarku, alhali kaima ba ka kyautatawa al’umma daidai karfinka. Kamar yadda manzonmu ya fada cewa a nemi aljannah ko da da tsagin dibino ne. To ya kamata ka nemi aljanna da iyakar abin da Allah ya hore ma.
Mun azumci Ramadan na bara tare da wasu amma yanzu ba sa tare da mu sun riga mu gidan gaskiya Ya Allah Ka ji kan musulmai, mu kuma da muke a raye Ya Allah Ka sa mu yi kakkyawan karshe, Ka bamu ikon azumtar azumin badin badada. Ya Allah Ka bunkasa garina Hadejia Ka sanya albarkarka a cikin garin, Ya Allah ka taimaki gwamnatin Baba Buhari Ka masa jagoranci Ka kara masa lafiya da juriya, gwamnoninmu da duk wani mai jagorantar al’umma a kasar nan Ya Allah Ka masa jagoranci, kuncin rayuwa da ake fama da shi ya Allah Ka kawo mana saukinsa, mata masu juna biyu Ya Allah Ka sauke su lafiya, ina yiwa al’ummar musulmi fatan alheri a duk inda suke cikin duniya fatan za su sha ruwa lafiya. Duk wanda na batawa a cikin duk wani rubutu da na taba yi ina neman afuwarsa ya yafe min nima na yafewa duk wani wanda ya bata min ko da ban da masaniyar abin da ya min na cutarwa ko batanci.
Nasiru Kainuwa Hadeja (Mataimakin Ma’ajin Kungiyar Muryar Talaka, reshen Jihar Jigawa) 08100229688