Shawara ga masu masana’antar fina-finan Kannywood

Kamfanin Kanny wood (masana’antar fina-finan Hausa), kamfani ne da ya shafi rayuwar kowa a Najeriya, kodai kai tsaye ko kuma ta hanyar wani nasa. Kamar yadda Hausawa ke cewa ‘’da na kowa ne’’ wannan haka ne, don haka duk abin da zai kawo tabarbarewar tarbiya ko kuma ya kara ingantata, to lallai ya shafi dukan […]

Shawara ga masu masana’antar fina-finan Kannywood
Shawara ga masu masana’antar fina-finan Kannywood

Kamfanin Kanny wood (masana’antar fina-finan Hausa), kamfani ne da ya shafi rayuwar kowa a Najeriya, kodai kai tsaye ko kuma ta hanyar wani nasa. Kamar yadda Hausawa ke cewa ‘’da na kowa ne’’ wannan haka ne, don haka duk abin da zai kawo tabarbarewar tarbiya

ko kuma ya kara ingantata, to lallai ya shafi dukan al’umma ne. Daidai lokacin da kamfanin Kanny wood ya kai kololuwa ga daukaka a idanun al’umma, mutane da yawa suka arzurta ta hanyarsa, a lokacin da kuma matasa da yawa suka samu harkar yi maimakon zaman banza, sai ga shi a rana tsaka, harkar ta ci karo da mummunan cikas da wata guguwar da ke yi barazanar fadowarta kasa warwas, Kuma wannan dalilin ne ya sa nake taya kamfanin murna.
Ba kowace matsala ce ke zama sharri har zuwa karshenta ba, mafi yawanci ma, dukan wata matsala idan an bi dokoki da ka’idodi kuma an kai zuciya nesa, za ka ga karshenta yakan zamo alkhairi ne da za a yi farin ciki da samuwarsa. Misali, idan Kanny wood suka karbi cewar lallai akwai tarin kura-kurai a cikin sana’ar, wadanda kuma ba domin su ba, da ba su ci karo da wadannan matsaloli ba, to shi ke nan magana ta kare, sai kawai in shiga ba su shawara.
Abu na farko; Tunda a fili yake cewa fina-finan Hausa da yawa da suka samu karbuwa a kasar nan ba ainihin na kirkira ba ne, kwafi ne kawai da kwaskwarima daga fim din Indiya zuwa Hausa, ko kuma daga na Turanci zuwa Hausa. Wannan matsalar kuma takan haifar da matsaloli kamar haka; Matsala ta farko ita ce rashin albarka a cikin kasuwanci, Domin Allah ba zai sanya wa dukiyar zalunci albarka ba, kuma satar fasahar wani ka je ka ci gajiyarta ba tare da ya ma san ka yi ba.
Matsala ta biyu ita ce, Barin al’adar Hausawa kacokam zuwa al’adar wadanda aka sato fim din nasu. Misali, duk wanda ya kalli fim din Jalaluddeen zai san cewa abin da ya faru a ciki ya yi hannun riga da al’adar malam Bahaushe da kuma yanayin zamantakewarsa. To abin da ya haifar da haka shi ne; Fim din ba ainihin shiri ne da Hausawa suka kirkira ba, shirin Turawan Nolly wood ne mai taken “Dangerous Mother.” Misalan irin wadannan fina-finai sun wuce a lisafa.
Matsala ta uku, Rashin isar da sako mai alfanu. Saboda kowane yanki matsalarsa takan sha bam-bam da yanayin wasu yankunan daban. Watakila wadanda aka sato fim dinsu, matsalar da ta addabi yankinsu wadda har aka shirya fim din saboda ita, ita ce aurar da yara ’yan kasa ga shekara 20, mu kuma matsalar da ta addabe mu ita ce dadewar da ’ya’ya mata ke yi har zuwa shekaru 15 ba su yi aure ba! To idan ka dauko wancan fim din ka juya mana, me kake so mu fahimta ke nan? Ka ga ba wani alfanu da shirin zai yi mana sai ma kara dabirta mana lissafi da zai yi.
Tunda dai ba harkar tone-tone ba ce a yau, sai dai kokarin bayar da shawara da kuma nema wa kanny wood mafita, zan tsaya a bakin wadannan matsalolin guda uku da ke sama, akan abin da ya shafi satar fasaha. Idan kuma an lura da kyau, za a ga cewar ina nufin satar fasaha ba ta da kyau, kuma akwai bukatar ta zama tarihi a Kanny wood idan dai ana son samun ci gaba. Tunda ga fili yake, Allah bai bai wa masu shirya finfinan Hausa fasahar kirkira shiri mai ma’ana da mutane za su kalla ya dace da al’adarsu har ya fadakar da su ba, to akwai hanya mafi sauki da za a bi domin magance matsalar. Akwai dimbin marubuta littafan Hausa, wadanda littafansu suke dauke da labarai masu kayatarwa matuka, kuma wadanda suke dauke da al’adar malam Bahaushe tsantsa, sai masu kanny wood din kawai su ci gaba da hada kai da su domin a gudu tare a tsira tare.
Shawara ta uku, idan har aka shirya da mai littafin da aka yarda da littafinsa ne za a mayar a matsayin shirin fim, to sai kuma a samu darakta kwararre, wanda ya san makamar aikinsa, ba wanda kawai ya ji ana furta kalmar ‘’Action’’ ba, shi ma ya zo ya are ya yi yafe, wai ga sabon darakta. Domin na fahimci a Kanny wood, hatta da mai kwalliya na iya zamowa darakta idan ya ga dama.
Baya ga littafan da aka riga aka rubuta kuma, akwai marubuta masana, akwai ’yan jarida wadanda suka san al’adar Hausawa, kuma suke da kwazo a wajen aikinsu, su ma idan jarumi yana sha’awar yin sabon fim, babu illa idan ya nemi daya daga cikinsu akan su hada karfi da karfe a taru a taimaki juna? Shi mutumin da ya rubuta fim din, shi kuma jarumin ya fito a matsayin jarumin. Sai ka ga al’amari ya bayar da sha’awa, kuma an samu arziki mai albarka.
Matsalolin fa suna da yawa, amma Allah abin godiya tun da an riga an san su, illa dai magance su kam, sai an kai zuciya nesa. Mu kuma in Allah Ya so za mu ci gaba da bayar da shawara akan yadda za a gyara harkar ta yi armashi, sai dai idan muka lura da ba gaskiyar ake so abi ba, shi ke nan sai ungulu ta koma gidanta na tsamiya.
Nasir Abbas Babi
08033186727