Shawara ga masu son kafa kasar Biyafara
Zuwa ga Editan Aminiya. Zan yi amfani da wannan dama matukar zan samu, domin in ba abokan zamana shawara ’yan kabilar Ibo da ma Kudu maso Gabashin kasar nan da ke son kafa kasar su ta Biyafara, wato Biafra ’yan shawarwari ne nake ganin idan sun bi su, za su cimma buri gare su. Su […]
Zuwa ga Editan Aminiya. Zan yi amfani da wannan dama matukar zan samu, domin in ba abokan zamana shawara ’yan kabilar Ibo da ma Kudu maso Gabashin kasar nan da ke son kafa kasar su ta Biyafara, wato Biafra ’yan shawarwari ne nake ganin idan sun bi su, za su cimma buri gare su. Su rufe shagunan su da ke kowane sashe na kasar nan, su kirawo ’yan uwansu mazauna gida da waje su dawo gida, su hana saye-da sayarwa duo rani dan Najeriya bayan su, su janye ’yan kabilar su daga mukaman gwamnati da na ma’aikatunta biyar. su yi takardar iznin shiga kasar su. A fahimta ta su rufe saye da sayarwa a manyan kasuwannin Kano da Alaba intl. Legas Anacha da kuma Kaduna da sauran manyan biranen Najeriya, su toshe kofar babbar gadar nan ta Onitsha kada na Arewa ya shigo, na kudu kuma ya fita. Kada su fita Arewa sayo kayan abinci ko dabbobi., komai su tanade shi. Ina ga watakila za su iya cimma bukata, amma nasan wanda duk ya karanta wannan ’yar makala tawa, zai dora kuma zai fi ni hangen wani abin da ni ban hango ba. Da fatan shawarata da ta karbu a wajen kabilar Igbo. Domin masu iya magana kan ce duk abin da zaman lafiya bai bayar ba, tashin hankali kuwa ba zai iya ba da shi ba. Da fatan Sudan ta Kudu za ta iya zama darasi gare su. Nagode. Daga Ahmad Abdusslam. [email protected] 09035953671