Shawara ga sabuwar Gwamnatin Zamfara
Assalamu alaikum, muna bada shawara ga wannan sabon gwamna yayi duk mai yiwuwa domin hada kan al’ummar jihar Zamfara kwata, domin tafiya tare don ganin an ciyar da jihar gaba, kasancewar akwai babban aiki ja a gaban sabon gwamnan musamman idon mukayi la’akari da tabarbarewar tsaron da jihar take fuskanta a yanzu haka, babu makawa […]
Assalamu alaikum, muna bada shawara ga wannan sabon gwamna yayi duk mai yiwuwa domin hada kan al’ummar jihar Zamfara kwata, domin tafiya tare don ganin an ciyar da jihar gaba, kasancewar akwai babban aiki ja a gaban sabon gwamnan musamman idon mukayi la’akari da tabarbarewar tsaron da jihar take fuskanta a yanzu haka, babu makawa sai ya daura damarar yin wannan gagarumin aiki don ganin ya magance wannan fanni, domin zaman lafiya shine kashin bayan cigaban kowace irin al’umma a duniya, kuma saida shine sannan dukkan cigaba zai samu gindin zama a tsakanin al’umma.
Sannan sai a dubi fannin matasa da idon rahama, kasancewar akwai dinbin matasanmu dake zaune a sassan Jihar daban-daban marasa aikin yi, wanda hakan ne yake saka mafi yawan matasan shiga cikin wani mawuyacin hali, yana da kyau a dubi makomar matasa a samar musu da kyakkyawar yanayi wanda zai taimaka wajen yakar zaman kashe wando a tsakaninsu.
Sannan yana da kyau a dubi makomar ma’aikatan Gwamnati musamman Malamai masu koyarwa a Makarantu daban-daban a matakai daban-daban, kasancewar dukkan wanda ya taka wani matsayi saida ya biyo ta hanyar Makaranta, yana da matukar alfanu a kyautata walwala da jin dadin su, ta haka ne zasu tsayu haikan domin ganin sun samar da ingantaccen ilimi a cikin al’umma ba tare da sanya ha’inci ba.
Haka sabon Gwamna yana da kyau a dubi matsalar ruwan sha, musamman a cikin Birnin Gusau inda matsalar tafi kamari, kasancewar an shafe shekaru ana fama da matsalar ruwan sha, tabbas zaiyi kyau a dubi wannan matsalar da idon rahama domin magance ta, kasancewar ruwa shine rayuwa, kuma saida shi ne sannan rayuwa take gudana.
Sannan yana da kyau a dubi ‘yan uwanmu marayu da ‘yan gudun Hijira wadanda tashe-tashen hankula ya tilasta musu barin gidajensu suka dai-dai ce a cikin Jihar dama makwaftan Jihar baki daya, a samar musu da wajen zama na musamman wanda za a rika kula da su, har Allah ya kawo zaman lafiyar da zasu koma mazaunansu na asali.
Haka Sabon Gwamna yana da kyau a dubi manyan Kamfanonin da muke da su a cikin jiha domin gyarawa hadi da farfado da wasu sababbi, domin kara inganta Jihar da al’ummar Jihar kwata.
Yana da kyau sabon gwamna a dubi sashen kiyon lafiya, domin akwai babban kalubale a wannan sashen, kasancewar mafi yawa daga cikin asibitocinmu babu isassun Malaman asibiti babu kayan aiki, babu Magani, musamman idon muka dubi asibitocin Kar-kara, sunyi matukar tabarbarewa, yana da kyau a inganta sha’anin kiyon lafiya, domin sai da lafiya ne, sannan za a samu yin ayukan yau da kullum, babban abinda yafi ciwa kowane Dan Zamfara tuwo a kwarya shine matsalar tsaron Jihar Zamfara, yana da kyau a zage damtse domin ganin komai ya zama tarihi, sabon Gwamna muna fatan za a dubi wadannan korafe-korafe a lokacin da komai ya dai-daita a cikin ofis.
Ina amfani da wannan dama domin taya murna ga mai girma Sabon Gwamnan Jihar Zamfara, Alahji Bello Muhammad Matawallen Maradun, a kan nasarar da Allah Ya ba shi na dare wannan kujera cikin sauki. Babu shakka wannan abun ishara ne ga ‘yan siyasa a duk inda suke a fadin duniya.
Muna yiwa Gwamnati, addu’ar samun dukkan kowace irin nasara a cikin mulkinta, muna fatan alheri, kuma zamu iya kokarinmu wajen bayar da shawara a inda muka ga an yi ba daidai ba.
Allah ya bamu lafiya da zama lafiya, da kwanciyar hankali da wadata a Jihar Zamfara da Arewacin Najeriya, da Najeriya, da nahiyar Afrika baki daya.
Daga Nura Muhammad Mai Apple Gusau, dan Kungiyar Muryar Talaka ta Kasa reshen Jihar Zamfara, 08133376020