Shawara kan canja Tsarin Mulki
Zuwa ga shugabannin Majalisar Dokoki ta kasa (ta wakilai da ta dattawa) da shugaban kwamitin gyaran tsarin mulki da kwamitin taron kasa da dukkan ’yan majalisun jihohi da manyan jami’an gwamnati da malaman jami’o’i da sarakuna da manyan malaman addini ko fastoci da kwararru da attajirai da kafofin watsa labarai na gida da waje.A madadin […]
Zuwa ga shugabannin Majalisar Dokoki ta kasa (ta wakilai da ta dattawa) da shugaban kwamitin gyaran tsarin mulki da kwamitin taron kasa da dukkan ’yan majalisun jihohi da manyan jami’an gwamnati da malaman jami’o’i da sarakuna da manyan malaman addini ko fastoci da kwararru da attajirai da kafofin watsa labarai na gida da waje.
A madadin al’ummar wannan kasa, musamman ’yan uwana talakawa da raunana wadanda kullum kowane zalunci a kansu yake karewa ga namu shawarwarin da muke ganin sun fi muhimmanci game da wannan yunkuri mai alfanu, bisa kyakkyawan zaton matukar ana nufin yin gyara ne, to za a yi la’akari da su.
Za mu bayar da shawarwarin nan ne a takaice, in dama ta yi na a neme mu, sai mu zo mu yi fashin baki a fadade.
Abubuwan da muke ganin sun fi kamata a ba muhimmanci a lamarin gyara tsarin mulkin, su ne kamar haka:
1. Shugabanci:
Ya kamata a tabbatar karara a cikin tsarin mulkin kasar nan cewa duk wanda yake son yin takara ko a nada shi a wani mukami, tun daga mazabar kansila zuwa karamar hukuma zuwa jiha zuwa tarayya, to dole ne sai ya samu sahalewa daga dattijan mutane na hakika mutum 12, a cikinsu har da mai unguwarsu da dagacinsu.
Su wadannan mutum 12 su kasance mutane ne da suke da kyakkyawar shaida a wurin al’umma, kuma ba a taba samunsu da hannu a wata barna ko wani abin zargi ba. Kuma su tabbatar duk wanda za su sanya wa hannu, sun san asalinsa da iyayensa da sana’arsa. Su tabbatar ba maha’inci ba ne ko barawo ko fajiri ko fasiki, ko wanda ake tuhuma da wata ta’asa a gwamnatance ko a al’ummance. Haka sai sun yarda da cewa duk abin da wanda suka fitar ya yi, to su ma suna cikin wadanda al’umma da hukuma za su tuhuma, har sai sun bayar da gamsassun dalilan da za a aminta da su.
Sannan duk wani shugaba da aka zabe shi, matukar yana da ikon ya kai wani kara alhali yana kan mulki, to shi ma sai doka ta bayar da dama shi ma a iya gurfanar da shi idan ya yi laifin da ya cancanci hakan. In kuwa har yana da rigar kariya, to shi ma sai ya bari sai ya sauka daga mulki, sannan ya iya kai karar duk wanda yake ganin ya taba shi.
2. Tsarin Jamhuriyya:
Shiyyoyin nan shida da muke da su a kasar nan, da ba sa cikin tsarin mulki, amma aka fifita su fiye da abubuwan da ke cikinsa, to ya kamata a yi musu muhalli su zamanto a cikin tsarin mulkin. Wato ya kasance kwatankwacin yadda muke a Jamhuriyya ta daya, wacce take da Firayi Minista da firimiyoyi. Ya kasance kasar nan ta zama mai Firayi Minista daya da firimiyoyi shida. Sannan kowace shiyya a cikin shidan a ba shi cin gashin kansa, ta yadda zai tsara kundin tsarin mulkinsa na kansa da zai dace da mutanensa ta fuskar addini da al’ada.
Kwatankwacin yadda ko a Amurka, wata jiha take bambanta da wata a kundin tsarin mulkinta da kuma nau’in horo ko hukunci ga kowane laifi. In ba haka ba kuma, to mu koma tsarin Ingila baki daya. Wato ga Firayi Minista, amma babu jihohi, sai kananan hukumomi.
3. Tattalin arziki:
A kowace kasa a fadin duniyar nan, komai girmanta, komai yawan mutanenta, komai karancin arzikinta, Allah Mai kowa da komai Ya tanadar wa kowa duk abin da yake bukata domin ya yi kyakkyawar rayuwa. Sai dai idan an samu rashin iya mulki ko zaluncin masu mulki.
Kamar yadda yake a cikin kundin tsarin mulkin Najeriya, tun daga Jamhuriyya ta daya har zuwa yanzu, duk abin da yake arzikin kasa, shin a ruwa yake ko a tudu, a dutse yake ko a rami, ko a sararin samaniyar kasar nan yake, to mallakar duk ’yan kasar nan ne. Koda kuwa ya kasance wannan arzikin kasar ya kusanci wasu mazauna wani wuri, to sai dai a tashe su a sake musu wani wurin zama. Wannan arzikin zai kasance a wannan muhallin kuma yana matsayin mallakar duk ’yan kasa ba tare da fifita wani yanki ba.
Kamar yadda aka tashi wasu al’umma daga gidajensu da gonakinsu da wuraren sana’o’insu, aka mayar da wurin a matsayin birnin tarayya, wato Abuja. Su kuma aka musanya musu da wasu wuraren zama da gonaki da wuraren sana’o’in. Kuma koda zai kasance wasu albarkatun kasa sun bayyana a gidan wani mutum ko wane ne shi, wato ya kasance an gano lu’u-lu’u ko gwal ko azurfa ko tagulla ko man fetur ko iskar gas, ko ma menene, to mallakin tarayyar Najeriya ne. Sai dai shi wannan mutumin a ba shi wani wurin ya koma, ko kuma a biya shi diyya.
4. Harshen kasa
Saboda a samu dankon zumunci da hadin kai a tsakanin al’umma na kasancewa kasa daya al’umma daya da kuma karfafa tsimi da tanadin tattalin arzikinmu, lokaci ya yi da kasar nan za ta yi watsi da harshen wata kasa da aka bautar da mu da shi, kuma ake tatse mana arzikin kasa dominsa, ake nuna mana har yanzu ba mu san komai a cikinsa ba.Mu zabi daya daga cikin harsunan Najeriya mafi bunkasa a duniya, a tsarma shi a cikin manhajar karatu ta kasar nan, tun daga firamare zuwa jami’a, ta yadda nan gaba kadan za a iya mayar da shi harshen kasar nan baki daya. Ya zamanto da shi za a rika amfani a duk ayyukan gwamnati da sauran mu’amalolin da suka shafi kasa.
5. Inganta tsaro
Tun da sarakunan gargajiya ba su da wani tanadi na ayyukan da za su yi a cikin kundin tsarin mulkin kasar nan, akwai wajabcin a kirkiro wani tsari mai kama da na Hisba a ko’ina cikin kasar nan, a ba su horo na musamman, yadda za a dora musu nauyin kula da duk abin da yake faruwa a kowace unguwa gida-gida da lungu-lungu da kuma sako-sako, tun daga unguwanni zuwa mazabu zuwa kananan hukumomi zuwa jihohi. Aikinsu ya zama bankado batagari baki da ’yan gari, maza da mata, ta fannin bincikowa da hana shaye-shayen ababen maye ko fajirci da fasikanci da algus da tauye mudu da damfara da yaudara da sauransu. Haka kuma su ne za su rika kula da rajistar haihuwa da mutuwa ta yadda in ana neman bayanan wadannan za a iya samu a wurinsu. Hakan zai saukaka kashe kudi da wahalar kidayar yawan jama’a. Kuma duk wanda suka kama, ya zama suna da ikon gurfanar da shi a gaban kotu, tare da goyon bayan masu unguwanni da hadin kan ’yan sandan wurin da abin ya faru. Ya kasance suna da ikon bibiyar kowace shari’a har zuwa Kotun koli don tabbatar da adalci.
6. Biyan diyyar rai
Kowace gwamnati ana kafa ta ne don ta kare rayuka da lafiya da dukiya da mutunci da addinin kowa da kowa.
Tilas ne a rika biyan diyyar duk rayukan da suka salwanta ba ta hanyar shari’a ba. Wadanda jami’an gwamnati ke kashewa kai-tsaye da wadanda sauran mutane ke kashewa wasu hanyoyi. Ya zamo nauyin biyan diyya yana wuyan gwamnati, wadda ita kuma daga baya za ta bi kadin yadda aka yi kisan, tare da matsayin diyyar da ta biya daga wanda ya yi kisan, domin daukar mataki ko horon da ya dace.
7. Tallafi ga marasa galihu
Bisa la’akari da dimbin arzikin da kasar nan take da shi, bai kamata a ce akwai dan kasar nan da ke kasa iya cin abinci sau uku a rana ko ya rasa tufafi, ko ba shi da muhalli koda na haya ne ba. Wajibi ne gwamnati ta samar da wani tsari na tallafi ga duk wanda bai da aikin ko sana’a, ko wani dalili ya sanya ya rasa su. Haka kuma a rika tallafa wa sauran raunana da nakassu da marasa lafiya akalla duk mako. Duk rukunin wadannan mutane kowa ya je karamar hukuma mafi kusa da shi, don karbar alawus din abin da zai kula da rayuwarsa da ta iyalinsa na kwana bakwai. Kuma dukkan wata uku ya je ya karbi tufafi guda biyu, sannan a yi musu tanadin mafakar ruwa da sanyi da ban-dakuna da wuraren ibada, har sai gwamnati ta samar musu da aiki ko sana’a, sannan a fitar da shi daga rukunin ’yan tallafi. Kuma wadannan mutane gwamnati ce za ta dauki nauyin ilimin ’ya’yansu, tun daga firamare zuwa jami’a. Haka kula da lafiyarsu da ta ’ya’yansu da iyalansu.
Babu wani dan kasar nan da yake da ilimi da hankali, da zai ce wadannan abubuwa ba za su yiwu ba, sai dai kawai a ki yi.
Abdulkarim dayyabu
Shugaban Rundunar Adalci ta Najeriya
08060116666, 08173106666, 08023106666