Shawarar Therasa May: A kai kasuwa!
Fira-Ministar Ingila, Theresa May ta haddasa rudani tare da cece-ku-ce mai yawan gaske a lokacin da ta bukaci Najeriya da sauran kasashe renon Ingila su halasta auren jinsi a kasashensu a yayin taron kasashen na Commonwealth da aka kammala kwanakin baya Landon. Theresa May ta ce babu dalilin da zai sanya ayi watsi ko tauye […]
Fira-Ministar Ingila, Theresa May ta haddasa rudani tare da cece-ku-ce mai yawan gaske a lokacin da ta bukaci Najeriya da sauran kasashe renon Ingila su halasta auren jinsi a kasashensu a yayin taron kasashen na Commonwealth da aka kammala kwanakin baya Landon. Theresa May ta ce babu dalilin da zai sanya ayi watsi ko tauye hakkin wani a tsakanin al’umma bisa abin da ya ke so.
Kuma a cewarta, kasar Ingila na shirye da ta taimaki dukkan kasar da ta yarda ta sauya dokar haramcin aurin jinsi a kasarta. Tana mai cewa duniya ta kara samun cigaba cikin tafiyar shekaru 50 a lokacin da ake tilasta al’umma, amma matasa ‘yan bana-bakwai a yau na son tsara rayuwarsu ne a bisa zabinsu.
Fira Ministar ta kuma yi nuni da cewa a taron CHOGM da ya gabata, an cimma nasarar kafa wata kungiya da za ta karfafa bukatu da kare hakkin ‘yan luwadi da madigo har ma da maza-mata. “Amma abin mamaki har yanzu basu tabuka komai ba. Babu wanda ya cancanci hunkunci ko tofin Ala-tsine don kawai ya zabi ya aiwatar da abin da ransa ke so. Don haka Birtaniya a shirye ta ke da ta mara wa dukkan kasar renon Ingila da ta yarda ta sauya tsohuwar dokar harmaci wanda ya haddasa kyama da bambance-bambance a tsakanin al’umma baya.”
Duk da cewa Daular Birtaniya ta rushe wasu shekaru can baya, amma bukatu da soye-soyen al’umma na cigaba da wanzuwa, kamar kuma yadda a gefe guda zarge-zargen al’adun al’umma ke samun tsangwama. A wasu shekaru kalilan da suka gabata, wasu kasashen Yammacin Duniya sun bukaci Najeriya da sauran kasashe su halasta luwadi da madigo tare da auratayyar jinsi. Majalisar Dokokinmu ta gabatar da wani kuduri a 2013 wanda ke haramta dukkan harkokin mu’amalar saduwa a tsakanin jinsi guda.
Sannan ma da kiraye-kiraye suka yawaita daga kasashen yammaci, sai tsohon Shugaban kasa, Goodluck Jonathan ya rattaba wa kudurin hannu ta zama doka a 2014. Inda dokar ta fayyace cewa dukkan wanda aka samu da aikata luwadi ko kulla auren jinsi zai fuskanci daurin shekaru 14 a gidan yari. Sannan ta kara da cewa, “Dukkan wanda ya yi rajistar ko ta gudanar ko ya halarci wani kulob na ‘yan luwadi ko ma dukkan wata matattara da mu’amalar jinsi a Najeriya, to ya saba doka, kuma zai fuskanci daurin shekaru 10 a gidan maza.”
Jim kadan bayan tataba wa dokar hannu, Sakataren Harkokin Wajen Amurka, John Kerry ya bayyana cewa Fadar Washington ta damu matuka da wannan mataki. Ya ce, “Baya ma ga haramcin auren jinsin, har ila yau dokar ta kasance abar kyama wacce ta tauye ‘yancin ‘Yan Najeriya da kuma wakilcin majalisa.” Amma Najeriya ta yi watsi da kalaman na Kerry wadanda ke cike da shiririta, sannan ta gaggauta fara aikin dokar anan take. Dukkan kasa ta na yin doka ne bisa dacewa da al’adu da ra’ayin al’ummarta, don cika muradin ‘yan kasarta, wadda kuma wannan doka a zahiri ta nuna hakan. Amma ace Madam May ta bukaci mu sauya wannan bisa muradin al’ummar Ingila, ba karamin rainin hankali ba ne.
Hikaka mun yi Allah-wadai da wannan kira na ta, kumma wannan karara ya nuna cewa wannan mata Theresa May ba ta girmama dokokin kasarmu da al’adunmu ba.
Yana da kyau shugabannin kasashen duniya su rika marataba al’adun mutanen sauran kasashe, ko da kuwa sun samu kansu a karkashin inuwar wata kungiya guda. Dukkan kasa ta na da tsarinta da kuma aladunta. Luwadi da madigo sun zama haramun ne a Najeriya tun fil-azal ba yanzu ba, sannan ba maganar wani sauyi ake yi ba. Hakika mun gaji wasu dokoki masu yawa daga Birtaniya a lokacin mulkin mallaka, amma mun cigaba da yin amfani da wadanda suka kwanta mana a rai, sannan kuma mu yim watsi da dukkan wadanda wadanda suka saba wa addinai da al’adunmu kasancewar mallakar ta kare a halin yanzu.