Shawarar Tony Blair ga Buhari: Ko ya dace a cire tallafin mai a Najeriya?

Tsohon Firaministan Ingila, Tony Blair ya shawarci Shugaba Muhammadu Buhari da ya cire tallafin mai da ake ta kwakwazon ana yi a Najeriya. Abin tambaya a nan shi ne, shin ko ya dace a dauki shwarar tasa ko kuwa? Wakilanmu sun tatattaro ra’ayoyin mutane game da al’amarin kuma ga abin da suke cewa: Ya dace […]

Shawarar Tony Blair ga Buhari: Ko ya dace a cire tallafin mai a Najeriya?
Shawarar Tony Blair ga Buhari: Ko ya dace a cire tallafin mai a Najeriya?

Tsohon Firaministan Ingila, Tony Blair ya shawarci Shugaba Muhammadu Buhari da ya cire tallafin mai da ake ta kwakwazon ana yi a Najeriya. Abin tambaya a nan shi ne, shin ko ya dace a dauki shwarar tasa ko kuwa? Wakilanmu sun tatattaro ra’ayoyin mutane game da al’amarin kuma ga abin da suke cewa:

Ya dace a dauki shawarar Blair – Aminu Abdullahi

Musa Kutama, a Kalaba

Alhaji Aminu S. Abdullahi: “Gaskiya daya ce, ya dace Shugaba Muhammadu Buhari ya yi amfani da shawarar da Tony Blair ya ba shi, domin yana daga cikin ajandar mai girma Shugaban kasa na mayar da hankali kan hako ma’adanai da farfado da aikin gona domin a rage dogara da albarkatun man fetur. In ka duba manyan kasashen duniya kamar kasar Sin ai ba ta dogara da albarkar man feturu ba, sun dogara ne da masana’antu, fasaha da kere-kere. don haka daukar shawarar abu ne mai kyau.”

Kada ya dauki shawarar Blair – Alhaji Malami

Musa Kutama, a Kalaba

Alhaji Malami kofar Atiku: “Alal hakiki idan har mai girma Shugaban kasa Muhammad Buhari ya ce zai dauki shawarar da Firaministan Birtaniya Tony Blair ya ba shi, zai jawo masa talakawa su fara yin guna-guni, su fara ganin murnarsu ko ciki za ta koma na ganin sawaba ta zo ma su. Ai da can shugabannin baya sun rage farashin albarkatun man fetur din amma hakarsu da ta sanya su suka rage ba ta cin ma ruwa ba. Idan da a ce Shugaban kasa zai neme ni da in ba shi shawara to da sai in ce masa ya yi watsi da waccan shawara shi yafi.”

daukar shawarar daidai ne – Abubakar Sadik

Sani Gazas Chinade, a damaturu

Abubakar Sadik Maidusa: “A ganina, dangane da shawarar da tsohon Firaministan Birtaniya Blair ya bayar ga Shugaban kasa Muhammadu Buhari a kan a cire tallafin mai da ake bayarwa daidai ne, matukar za a yi da kyakkyawar manufa. dalilina na fadin haka kuwa shi ne, a iya fahimtata dama can wannan tallafi ba duka ne fa ke amfanar da talakawan kasa ba, a mafi yawan lokaci ya fi amfanar manyan gwamnatocin da suka shude ne da wadansu daidaikun ’yan kasuwar mai. don haka cire tallafin shi ya fi zama fa’ida tare da gyara matatun manmu da aka kashe su da gangan don sayo mai daga wajen kasar nan, don biyan bukatun wasu.”

A dauki shawarar madmar… – Hussaini Tela

Sani Gazas Chinade, a damaturu

Malam Hussaini Tela: “Ra’ayina dangane da shawarar da tsohon Firaministan Birtaniya ya bayar ga Shugaban Buhari, cewa ya cire tallafin mai. Wannan shawarar abin yarda ce matukar gwamnatin za ta gyara mana matatun man kasar nan. domin in har Gwamnatin Tarayya a karkashin adalin Shugaba Muhammadu Buhari ta gyara matatun man kasar nan guda hudu, to ba mu ga dalilin sake sayo mai daga kasashen ketare ba, ballantana a yi zancen wani abu wai shi tallafi. don haka tallafin dama su wadanda suka yi uwa suka yi makarbiya wajen kashe matatun man kasar nan, su suke amfana da tallafin amma ba talaka ba da a yanzu ma yake sayen lita daya ta man fetur a kan farashin Naira 140.”

A bi shawarar Blair daidai ne – Harira Abdussalam

Rabilu Abubakar, a Gombe

Harirah Abdussalam: “Ni ina mai goyon bayan shawarar da tsohon Firaministan Ingila Tony Blair ya bai wa Shugaban kasa Muhammad Buhari, na janye tallafin man fetur domin amfanuwar ’yan Najeriya. Janye tallafin yana da matukar amfani domin da shi ne ake taimaka wa dinbim matasa marasa aikin yi ta hanyar Sure-P da sauransu don haka janye tallafin man fetur alheri ne gare mu. Idan aka janye, Shugaba Buhari ya sa ido sosai wajen ganin an yi amfani kudaden tallafin yadda ya kamata.”

A yi bincike kan shawarar Blair – Yaya Ahmad

Rabilu Abubakar, a Gombe

Yaya Ahmad Ngaudare: “Tony Blair ba dan Najeriya ba ne, Buhari ne dan Najeriya kuma ya fi Blair sanin halin da Najeriya take ciki, don haka shi ya kamata ya yanke wa kansa shawara na ko ya janye tallafin man fetur ko kar ya janye. Ko an janye tallafi ko ba a janye ba, ba duk ’yan Najeriya ba ne suke amfanuwa da wannan tallafin ba saboda wasu ’yan tsiraru ne kawai suke amfana. Buhari shi ne Shugaban kasa kuma ya san halin da kasar take ciki, shi ya kamata ya yi shawarar abun da ya fi kyau ga jama’ar kasarsa.”