Shawarwari ga ma’aurata (2)
Assalamu alaikum wa rahmatullahi wa barakatuh. Barkanmu da sake haduwa cikin wannan fili. Ga ci gaban kyawawan shawarwarin da masu karatu suka aiko ga ma’aurata domin gyarawa da inganta rayuwar aurensu, da fatan Allah Ya sa wannan bayani ya isa ga masu bukatarsa, ya kuma amfanar da su, amin.1. Ina ja hankalin ma’aurata mata a […]
Assalamu alaikum wa rahmatullahi wa barakatuh. Barkanmu da sake haduwa cikin wannan fili. Ga ci gaban kyawawan shawarwarin da masu karatu suka aiko ga ma’aurata domin gyarawa da inganta rayuwar aurensu, da fatan Allah Ya sa wannan bayani ya isa ga masu bukatarsa, ya kuma amfanar da su, amin.
1. Ina ja hankalin ma’aurata mata a kan su dubi Girman Allah su rike aure don fadin Annabi SAW ya ce: “Ku ji tsoron Allah kamar kuna ganinSa, in ba ku ganinsa to Shi Yana ganinku.
—Bala Musali Azare Bauchi
2. Ina ba ma’aurata shawara da su zama masu yawan tsafta da gyara jiki a kodayaushe musamman mata, da haka ne za su zama masu sha’awa, so da kaunar junansu. Sannan ina ba matan aure shawara a kan idan za su aikata wani abu kowane iri ne, to su shawarci mazansu, don mace idan ta yi aure ba ta da wanda ya fi mijinta.
3. Akwai wata babbar matsala daya a kan iyaye wadanda suke yi wa ‘ya’yansu lakabi da ’yar mace’. Sai ya kasance duk abin da yarinya ta zo ta fada a gidansu sai a yanke hukunci ba tare da wani bincike ba. Irin wannan na kassara rayuwar aure a wannan zamani.
—Nagode, Alh. Ibrahim M. Katsina.
4. Malama na karanta duk bayaninki a kan matsalar rashin adalci tsakanin mata biyu; yadda kika san kin shigo gidana domin abin da nake ta fama da shi ke nan: Idan ya yi wa ’ya’yanta wani abu ba ya yi wa nawa dan, sai ta ce min haka kawai a zo gidana a fi ni isa, kuma duk wata takarda ta kadararsa tana hannunta, kai ni dai wani abin ma ba zan iya fadar su ba. Ina kira ga masu irin wannan hali da su ji tsoron Allah su bari.
—Nagode, Twins.
5. Gaskiya bai dace yadda masu tallar kayan karin sha’awa ke bin hanya da hotunan batsa ba su jin kunyar Jama’a ba, ga yara ana tafiya da su suna gani. Kamata ya yi a ce sun ware shagon kayansu saboda akwai masu bukata sosai. Sannan kuma ina kira ga matan aure da su rika ba mazajensu hakkinsu musamman ta shimfidar aure. Rashin kulawar mace a gun mijinta shi ma yakan iya sa ya fada cikin wata masifa, wanda matar ba za ta so ba. Sannan mata ku zamo masu ladabi da girmama iyayen mazajenku. Sannan ku rika yawan nuna kulawarku gare mijinku, musamman wajen yin tsafta da kwalliya. Kar mace ta zama mai kushe mijinta a ko’ina ne, sannan ku kasance masu tsoron Allah.
—Jamila M Hassan
6. Ina so in mika sakona ga matan da ba su san biya wa mazajensu bukatar sha’awa da su sani cewa, mu maza mun fi su sha’awa, kuma su ji tsoran Allah, da cewar Allah zai tambaye su a kan hakkinmu da ba su ba mu ba, kuma su sani cewar mu maza Allah Ya ba mu damar yin auren mata har hudu, don haka ina mika shawarata ga mata da su daure wajen biya wa mazajensu bukatunsu, domin ta hanyar hakan ne za su iya sauke nauyin da Allah Ya aza musu.
—Mustafa Magaji
7. Ya kamata tun da har kuna ta magana a kan ma’aurata, to ku koma ga ‘yan mata da samari kan yadda da an yi aure wata 1,2,3 an fita yadda zawarawa suke lalata tarbiya, da yadda ake ta fasikanci, zawarawa sun fi ‘yan mata matsala kuma abin takaici za ku ga duk yawancinsu yara ne ko haihuwar fari ba su yi ba, wannan matsala tana ga mazaje, don suna yin auren dandane ne.
— Sulaiman Tafida Na’inna dambatta.
8 Na karanta nasiharki game da zinar hannu, sai dai gyara a kan Hadisan da kika dogara da su cewa mai zinar hannu zai tashi da ciki a hannunsa, domin dukansu ba su inganta ba, sai dai Allah (S.W.A) ya bayyana siffofin muminai ya bayyana su ne masu kiyaye Sallah, masu kiyaye farjojinsu sai ga iyalansu ko abin da damarsu ta mallaka, wanda kuma ya riki wata hanya bayan wannan su ne ’yan ta’adda, wato masu ketare iyaka. Sannan ya kamata a ba da shawara ga iyaye maza da mata da su yi wa Allah su lura da mummunar shigar da ‘ya’yansu mata suke yi, wanda shi hakan ne tushen dukkan wata barna a cikin al’umma. Allah Ya sa mu dace, amin.
—Muhammad Kabir Usman Katsina
9 Ni ina da aure, sai dai na kasance daga cikin masu wannan muguwar dabi’a ta zinar hannu. Na san hakan da mamaki, sai dai ba laifina ba ne, domin kwata-kwata matata ba ta da lokacina, mukan yi sati daya zuwa kwana goma ba tare da komai ya shiga tsakaninmu ba. Ga shi kuma na kasance mai tsananin sha’awa, hakan ne ma ya tilasta min aure da wuri. Sai dai an gudu ba a tsira ba.
10 Na karanta bayani a kan hukuncin zinar hannu, inda kuka ce hukuncinta daya da zinar asali wanda hakan a fahimta ta kuskure ne, domin zinar hannu malamam fikihu suna kiran ta da ‘al-istimna’ kuma sun yi sabani a kan hukuncinta kamar haka: haramun, makaruhi, ja’izun ma’addharurati.
11 Ni ma na kasance ina wannan dabi’a ta zinar hannu, kuma na san illarta, amma na rasa yadda zan yi na daina. A da ni mutum ne mai hadda sosai domin ina yin na daya a ajinmu, amma yanzu ina da yawan mantuwa. Kuma an gaya min cewa tana sa dakikanci na kuma ga alama a gare ni.
—Anas Kano.